Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 16

Wane Irin Mutum Ne Ayuba?

Wane Irin Mutum Ne Ayuba?

Akwai wani mutum a ƙasar Uz da ke bauta wa Jehobah. Sunan mutumin Ayuba. Yana da arziki sosai kuma yaransa da bayinsa suna da yawa. Ayuba mutumin kirki ne, ya taimaka wa talakawa da matan da mazansu suka mutu da kuma yaran da ba su da iyaye. Duk da haka, amincin Ayuba ya hana shi fuskantar matsaloli kuwa?

Ayuba bai san cewa Shaiɗan yana kallonsa ba. Sai Jehobah ya ce wa Shaiɗan: ‘Ka lura da bawana Ayuba? Babu wani mutumin kirki da aminci kamarsa a duniya.’ Shaiɗan ya ce: ‘Gaskiya ne cewa Ayuba yana yin abin da kake so. Kana kāre shi kuma ka albarkace shi. Ka ba shi filaye da dabbobi. Idan ka ƙwace waɗannan abubuwan, zai daina bauta maka.’ Sai Jehobah ya ce: ‘Ka jarraba Ayuba. Amma kada ka kashe shi.’ Me ya sa Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya jarraba Ayuba? Ya san cewa Ayuba ba zai daina bauta masa ba.

Sai Shaiɗan ya soma jarraba Ayuba. Da farko, ya sa Sabiyawa su sace shanu da kuma jakunansa. Bayan haka, wuta ta kashe dukan tumakin Ayuba. Sai wasu mutanen da ake kira Chaldiyawa suka sace rakumansa. Aka kashe bayin da suka je neman waɗannan dabbobin. Bayan wannan, wani abu mafi tsanani ya faru. Dukan yaransa da suke biki a cikin wani gida sun mutu sa’ad da gidan ya rushe a kansu. Hakan ya sa Ayuba baƙin ciki sosai, amma bai daina bauta wa Jehobah ba.

Domin Shaiɗan ya ƙara wahalar da Ayuba, ya sa maruru masu zafi sosai  su fito a jikin Ayuba gabaki ɗaya. Ayuba bai san abin da ya sa abubuwan nan suke faruwa ba. Duk da haka, bai daina bauta wa Jehobah ba. Allah ya ga abin da ke faruwa, kuma ya yi farin ciki sosai don abin da Ayuba ya yi.

Sai Shaiɗan ya tura wasu maza uku su je su jarraba Ayuba. Sun ce masa: ‘Allah yana maka horo ne domin akwai wani abu da ka yi da ba ka son kowa ya sani.’ Ayuba ya ce: ‘Ban yi laifi ba.’ Bayan haka, sai ya soma tunani cewa Jehobah ne yake jawo masa waɗannan matsalolin. Ya ce abin da Allah yake masa bai dace ba.

Wani saurayi mai suna Elihu ya yi shiru yana jin abin da suke faɗa. Bayan sun gama magana, sai ya ce: ‘Abin da kuka ce ba gaskiya ba ne. Jehobah ya fi mu ƙarfi. Ba zai iya yin mugunta ba. Yana ganin dukan abin da ke faruwa kuma yana taimaka wa mutane su yi maganin matsalolinsu.’

Sai Jehobah ya yi wa Ayuba magana. Ya ce: ‘A ina kake sa’ad da na yi sama da duniya? Me ya sa ka ce na yi maka abin da bai dace ba? Kana magana amma ba ka san dalilin da ya sa waɗannan abubuwan suke faruwa ba.’ Bayan haka, Ayuba ya yarda cewa ya yi laifi. Sai ya ce: ‘Na yi laifi. Na ji labarinka amma ban san ka ba sosai. Babu abin da ya fi ƙarfinka. Ka yafe mini.’

Sa’ad da Shaiɗan ya gama jarraba Ayuba, sai Jehobah ya sa Ayuba ya yi arziki fiye da wanda yake da shi a dā. Ayuba ya ji daɗin rayuwa kuma Jehobah ya ba shi tsawon rai. Jehobah ya albarkaci Ayuba domin ya yi biyayya sa’ad da yake shan wahala. Kai fa? Za ka zama kamar Ayuba ta wajen bauta wa Jehobah ko da mene ne ya faru?

“Kun dai ji irin jimirin da Ayuba ya yi, kun kuma ga irin ƙarshen da Ubangiji ya yi masa.”​—Yaƙub 5:​11, Littafi Mai Tsarki