Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwar Sashe na 6

Gabatarwar Sashe na 6

Sa’ad da Isra’ilawa suka isa Ƙasar Alkawari, mazauni ne ya zama wurin da za su riƙa bauta wa Jehobah. Firistoci ne suke koya musu dokar Allah, alƙalai kuma ne suke musu ja-gorancin. Wannan sashen ya nuna yadda abin da mutum ya yi yake shafen mutane. Kowane mutum a cikinsu yana bukatar ya kasance da aminci ga Jehobah da kuma ɗan’uwansa. Ka ambata yadda halayen Deborah da Naomi da Joshua da Hannatu da ’yar Jephthah da kuma Sama’ila suka shafi mutane a zamaninsu. Ka nanata yadda Rahab da Ruth da Jael da kuma Gibeyonawa suka haɗa kai da Isra’ilawa don sun san cewa Allah yana tare da su duk da cewa su ba Isra’ilawa ba ne.

A WANNAN SASHEN

DARASI NA 29

Jehobah Ya Zabi Joshua

Dokokin da Allah ya ba Joshua za su iya taimaka mana a yau.

DARASI NA 30

Rahab Ta Boye ʼYan Leken Asiri

Katangar Yariko ta rushe gabaki daya. Amma gidan Rahab bai rushe ba duk da cewa gidan hade yake da katangar.

DARASI NA 31

Joshua da Gibeyonawa

Joshua ya roki Allah: “Rana ta tsaya cak!” Shin Allah ya amsa wannan addu’ar?

DARASI NA 32

Sabon Shugaba da Mata Biyu Masu Karfin Zuciya

Isra’ilawa sun soma bautar gumaka bayan Joshua ya mutu. Sun sha wahala sosai. Amma Jehobah ya yi amfani da Alkali Barak da annabiya Deborah da kuma Jael don ya cece su!

DARASI NA 33

Ruth da Naomi

Wadannan mata biyu da mazansu sun rasu sun koma Isra’ila. Daya daga cikinsu mai suna Ruth ta je aiki a wani gona. A gonar ce Boaz ya hadu da ita.

DARASI NA 34

Gidiyon Ya Ci Midiyanawa da Yaki

Isra’ilawa sun roki Jehobah ya taimaka musu bayan Midiyanawa sun wahalar da su sosai. Ta yaya sojojin Gidiyon guda 300 suka ci sojojin Midiyanawa guda 135,000 a yaki?

DARASI NA 35

Hannatu Ta Roki Allah Ya Ba Ta Yaro

Elkanah ya kai Hannatu da Peninnah, da kuma yaransa bauta a mazaunin da ke Shiloh. A nan ne Hannatu ta roki Allah ya ba ta yaro. An haifi Sama’ila bayan shekara daya!

DARASI NA 36

Alkawarin da Jephthah Ya Yi

Wane alkawari ne Jephthah ya yi, kuma me ya sa? Ta yaya ʼyar Jephthah ta ji don alkawarin da babanta ya yi?

DARASI NA 37

Jehobah Ya Yi Magana da Sama’ila

Yaran Eli Babban Firist guda biyu suna hidima a mazaunin, amma ba su yi biyayya ga dokokin Allah ba. Sama’ilawa wanda shi matashi ne bai bi halinsu ba, kuma Jehobah ya yi masa magana.

DARASI NA 38

Jehobah Ya Ba Samson Karfi

Allah ya sa Samson karfi sosai domin ya rika yaki da Filistiyawa. Amma sa’ad da ya yanke shawara marar kyau, Filistiyawa sun kama shi.