Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Zan Yi Idan Aka Matsa Mini Game Da Batsa?

Me Zan Yi Idan Aka Matsa Mini Game Da Batsa?

 Mene ne ake nufi da matsa wa mutum ya yi batsa?

 Matsa wa mutum game da batsa ya kunshi kowane irin rashin kunya game da jima’i​—har da shasshafa azzakari ko yin tadinsa ma. Amma a wani lokaci yana da wuya a gane bambanci tsakanin tsokana, kwarkwasa, da kuma matsa wa mutum game da yin batsa.

 Za ka iya bambanta su kuwa? Ka duba  wasa ƙwaƙwalwarmu a kan matsi game da batsa don ka gano wa kanka!

 Abin tausayi shi ne, ba a makaranta ba ne kawai ake matsa wa mutane game da batsa. Amma, idan kika kasance da karfin hali da kuma fahimi sa’ad da aka matsa miki game da batsa yanzu, za ki iya kasance da karfin halin bi da ita sa’ad da kika zama ma’aikaciya. Za ki iya taimakon masu matsa wa mutane game da batsa su daina yin hakan!

 Idan Aka Matsa Mini Game da Yin Batsa Fa?

 Idan kin san bambancin matsi game da batsa kuma kin san yadda za ki bi da shi, to za ki iya kasance da karfin hali sa’ad da aka matsa miki! Ka yi la’akari da yanayi uku kuma ka ga yadda za ka bi da kowanne cikinsu.

 YANAYI:

“A wajen aiki, wasu samari suna ta gaya mini cewa ni kyakkyawa ce, da ma a ce sun girme ni da shekara 10. Har wani cikinsu ya bi ni ya sansana suma ta!”​—Tabitha, 20.

 Tabitha tana jin cewa: ‘Idan na yi banza da shi, ƙila zai daina.’

 Abin da ya sa ƙila hakan ba zai taimaka ba: Gwanaye suka ce idan aka yi banza da masu matsi game da batsa, hakan zai ci gaba ne har ya daɗa muni.

 Gwada wannan: Ki gaya wa mai halin nan a hankali kuma filla-filla cewa ba ki son wannan zancen ko halin sam-sam. Taryn ’yar shekara 22 ta ce: “Idan wani ya taɓa ni a inda bai dace ba, sai na juya na gaya masa kada ya sake taba ni kuma. Hakan yakan sa su mamaki sosai.” Idan mai matsin ya ci gaba, kada ki daina, da karfin hali ki ci gaba da gaya masa ba ki so. Game da batun kasance da ɗabi’a mai tsarki, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku dage, kuna cikakku masu haƙƙaƙewa.”—Kolosiyawa 4:​12, Littafi Revised.

 Idan mai matsi game da yin batsa ya yi barazanar zai yi miki wani lahani fa? To, kada ki yi fito na fito. Ki bar wurin nan da nan, kuma ki gaya wa wani da kika amince da shi ko ita.

 YANAYI:

““Sa’ad da nake aji shida, ’yammata biyu suka kama ni a baranda. Ɗayansu ’yar maɗigo ce kuma tana son na bi ta zuwa liyafa. Ko da yake na ƙi, sun ci gaba da dami na a ko yaushe a aji. Wani lokaci ma, suka tura ni jikin bango!”—Victoria, 18.

 Victoria tana jin cewa: ‘Idan na gaya wa wani, za a ce da ni matsoraciya, kuma ƙila babu wanda zai yarda gaskiya ce.’

 Abin da ya sa wannan irin tunanin ba zai taimaka ba: Idan ba ki gaya wa kowa ba, mai matsin zai ci gaba, har ma ya matsa wa wasu kuma.—Mai-Wa’azi 8:11.

 Gwada wannan: Ki nemi taimako. Iyaye da kuma malamai za su iya taimakon ki a yadda za ki bi da mai matsin. Amma idan waɗanda kika gaya musu ba su ga muhimmancinsa ba fa? Gwada wannan: Duk lokacin da aka matsa miki game da batsa, ki rubuta abin da ya faru daki-daki. Ki sa kwanan wata, sa’ar, da wurin da faru, da kuma abin da mai matsin ya ce. Ki ba iyayenki ko kuma malaminki kofi ɗaya. Mutane da yawa suna ɗaukan abin da aka rubuta da muhimmanci fiye da maganar baki.

 YANAYI:

“Ina tsoron wannan yaron sosai don ɗan rukunin wani kwallon hannu ne. Tsayinsa kafa 6.5, kuma nauyinsa kilogiram 135! Yana fahariyar cewa sai ‘ya kwana da ni.’ Yana ta matsa mini kowace rana​—na tsawon shekara guda. Wata rana, da ni da shi kaɗai muke cikin aji, sai ya soma matsowa kusa da ni. Na tashi da tsalle kuma na gudu waje.”​—Julieta, 18.

 Julieta tana jin cewa: ‘Halin samari ke nan.’

 Abin da ya sa ƙila wannan ba zai taimaka ba: Wannan mai matsa miki zai iya ƙin gyara halin idan kowa yana jin haka samari suke yi.

 Gwada wannan: Kada ki yi dariyar abin ko kuma ki yi masa murmushi. Maimako, ki tabbata ya gane filla-filla cewa a halinki​—da fuskarki​—kin ƙi jinin haka.

 Mene ne zan yi?

 LABARI NA 1:

“Ba na son yi wa mutane rashin kunya sam. Saboda haka, idan samari suna matsi mini nakan ce musu su daina​—amma ba na tashi tsaye a game da hakan, kuma sau da yawa ma nakan yi murmushi sa’ad da nake gaya musu su daina. Suna ganin kamar ni ’yar kwarkwasa ce.”—Tabitha.

  •   Da ke ce Tabitha, yaya za ki bi da masu yin matsin nan? Me ya sa?

  •   Me zai iya sa wanda yake miki matsi ya yi tsammanin cewa ke ’yan kwarkwasa ce?

 LABARI NA 2:

“Wasu yara maza ne suka soma maganar banza a lokacin da ake koyar da ilimin kimiyyar jiki. Na yi banza da abin da suke fada na ’yan makonni, amma sai zancen ya dada muni. Sai yaran suka soma zama kusa da ni kuma suna sa mini hannu a kafada. Nakan ture su, amma sai su dawo. A karshe, sai daya cikin yaran ya rubuta mummunar sako a falle kuma ya ba ni. Na mika wa malamina. Aka kore yaron a makaranta. Dā na je wajen malamin tun farko ma!”—Sabina.

  •   Me kake tsammanin ya sa Sabina ba ta je wajen malamin ba tun farko? Kana jin ta tsai da shawara mai kyau? Me ya sa, ko kuma me ya sa ba ta je ba?

 LABARI NA 3:

“Wani yaro ya dumfare kanina Greg a gidan wanka. Yaron ya maso kusa da Greg kuma ya ce, ‘Mu yi sumba.’ Greg ya ce masa a’a, amma yaron ya ki barinsa. Har sai da Greg ya ture shi.”—Suzanne.

  •   Kana jin cewa an matsa wa Greg game da batsa? Me ya sa ko kuma me ya sa ba haka ba?

  •   Me ya sa wasu matasa suke jinkirin fadin cewa wani ya matsa musu game da batsa?

  •   Ka amince da yadda Greg ya bi da yanayin? Da kai ne me za ka yi?

Ka kara koyo: Dubi babi na 32, “How Can I Protect Myself From Sexual Predators?” na littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Volume 1.