Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Yana da Muhimmanci Mutum Ya Sami Dimbin Abokai a Shafin Sada Zumunta?

Yana da Muhimmanci Mutum Ya Sami Dimbin Abokai a Shafin Sada Zumunta?

 Wata matashiya mai suna Elaine ta ce: “Da na ga cewa ’yan makarantarmu suna da daruruwan mabiya a shafin sada zumunta, sai na ce wa kaina, ‘Lallai su shahararru ne!’ A gaskiya, na dan yi kishin su.”

 Ka taba jin haka? Idan amsarka e ce, wannan talifin zai taimaka maka kada ka fada a tarkon neman suna ta shafin zumunta.

 Me ya sa yake da hadari?

 A Karin Magana 22:​1, Littafi Mai Tsarki ya ce “gwamma suna mai kyau da samun dukiya.” Don haka ba laifi ba ne mutum ya so ya sami suna mai kyau ko ma a ce mutane su so shi.

 Amma a wasu lokuta, neman a so ka zai iya sa ka kasa yin farin ciki idan ba a so ka ba. Neman yin suna yana da hadari kuwa? Wata matashiya ’yar shekara 16 mai suna Onya ta amince da hakan. Ga abin da ta ce:

 “Na taba ganin ’yan makarantarmu suna yin wasa da ransu don kawai suna so su yi suna. Har wasu sukan yi tsalle daga gidan sama su fado a kasa.”

 Garin kokarin jawo hankalin tsararsu, wasu sukan yi bidiyon wasan banza da suke yi kuma su saka shi a intane. Alal misali, wasu matasa sun taba saka wani bidiyo da ke nuna su suna cin sabulun wanki mai hadarin gaske, abin da bai kamata a ce mutum ya yi ba!

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku yi kome da . . . girman kai.”​—Filibiyawa 2:3.

 Ka yi tunani a kan wannan:

  •   Kana bala’in son mutane su san da kai a dandalin sada zumunta?

  •   Za ka iya sa ranka ko lafiyarka a cikin hadari don kawai ka burge tsararka kuma ka sa su so ka?

 Mutane suna karya don su nuna cewa su shahararru ne

 Ba a kowane lokaci ba ne masu neman suna suke sa ransu a cikin hadari. Wata ’yar shekara 22 mai suna Erica ta fadi wani abu kuma da mutane suke yi, ta ce:

 “Mutane sukan saka hotuna da yawa da za su sa a dauka cewa suna da abokai da yawa da suke shakatawa tare a kowane lokaci. Hakan zai sa mutane su ga kamar su shahararru ne.”

 Wata ’yar shekara 15 mai suna Cara ta ce mutane sukan yi karya don a ga kamar sun yi suna sosai. Ta ce:

 “Na taba ganin mutane sun saka hotuna da suka yi kamar suna wurin fati, alhali kuwa, a gida suke.”

 Matthew, wani dan shekara 22, ya fadi yadda ya taba yin hakan, ya ce:

 “Na taba saka wani hoto ya nuna cewa a Dutsen Everest na dauke shi, alhali ban taba zuwa wani wuri a Asiya ba!”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Nufinmu shi ne mu yi gaskiya a cikin ayyukanmu duka.”​—Ibraniyawa 13:​18, New World Translation.

 Ka yi tunani a kan wannan:

  •   Idan kana amfani da dandalin sada zumunta, kana yin karya don ka sa a san da kai?

  •    Kalamai da hotuna da kake sakawa suna nuna ainihin halinka da kuma imaninka?

 Yawan mabiya da masu son abin da ka saka yana da muhimmanci ne?

 Mutane da dama suna ganin idan kana so ka yi suna a intane, ka samo mabiya da yawa da masu son abin da kake sakawa a shafinka. Matthew wanda aka ambata dazu ya ce ra’ayinsa ke nan a dā. Ya ce:

 “Nakan tambayi mutane, ‘mabiya nawa kake da su a shafinka?’ ko ‘Mene ne adadi mafi girma na mutanen da suka so abin da ka saka a shafinka?’ Don in sami mabiya da yawa, nakan bi mutane barkatai da ban ma san su ba, da fatan su ma za su bi ni. Na zama mai bala’in so a san da ni kuma dandalin sada zumunta ya dada zuga ni.”

Neman suna a intane kamar kayan kwadayi yake, za ka ji dadinsa na dan lokaci amma ba zai cika ma ciki ba

 Maria, wata ’yar shekara 25, ta lura cewa wasu mutane suna ganin yawan mabiya da mutanen da ke son abin da suka saka ne yake nuna ko suna da daraja ko a’a. Ta ce:

 “Idan yarinya ta saka hotonta kuma mutane da yawa ba su danna alamar cewa suna son hoton ba, sai ta dauka cewa ba ta da kyau. Mutane da suke son saka hotonsu a intane sukan ji hakan. Amma ba gaskiya ba ne. Gaskiyar ita ce, suna ba wa kansu wahala ne kawai.”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada mu zama masu girman kai ko masu tā da hankalin juna ko masu kishin juna.”​—Galatiyawa 5:26.

 Ka yi tunani a kan wannan:

  •   Yin amfani da dandalin sada zumunta yana sa ka rika gwada kanka da wasu?

  •    Ka fi so ka sami mabiya da yawa maimakon ka kulla abota da mutanen kirki?