Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Zan Yi Idan Ana Cin Zalina ta Intane?

Me Zan Yi Idan Ana Cin Zalina ta Intane?

 Abin da ya kamata ka sani

 Yana da sauki a ci zalin mutum ta Intane. Intane yana iya sa mutane “har da yaran kirki su ci zalin mutane domin ba a ganinsu,” bisa ga abin da littafin nan CyberSafe ya fada.

 Akwai wadanda yake da sauki a ci zalinsu. Su ne wadanda suke shuru-shuru ko ana ganin ba su da gaba gadi ko kuma masu tsoro.

 Cin zali ta intane yana kawo mummunan sakamako. Cin zali ta intane zai iya sa mutum jin kadaici da kuma yin bakin ciki, har ma yana sa wasu su kashe kansu.

 Abin da za ka iya yi

 Abu na farko da ya kamata ka yi shi ne, ka tabbata ko ana cin zalinka ne da gaske. A wasu lokuta mutane suna iya fadin abin da zai bata maka rai, amma ba da saninsu ba ne. Idan hakan ya faru, zai yi kyau mu bi abin da Littafi Mai Tsarki ya fada cewa:

 “Kada ka yi garaje a ranka garin yin fushi; gama wawa ke rike da fushi cikin zuciyarsa.”​—Mai-Wa’azi 7:9.

 Idan wani yana zolayar mutum ko yana kunyatar da shi ko kuma yana tsoratar da shi ta intane, hakan cin zali ne.

 Ka tuna wannan, idan ana cin zalinka ta intane: Irin amsar da ka bayar zai iya sa al’amarin ya yi sauki ko ya dada muni. Ka gwada wani cikin shawarwarin da ke gaba.

 Ka yi banza da azzalumin. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda ya yi tsimi da maganatasa, ilimi ke gareshi: Shi kuma wanda ya ke mai sanyin ruhu mai fahimi ne.”​—Misalai 17:27.

 Abin da ya sa wannan nassin zai taimaka: Wata mai suna Nancy Willard ta rubuta a littafinta Cyberbullying and Cyberthreats, cewa: “Asalin dalilin da ya sa ake cin zali shi ne don a sa wanda ake cin zalinsa fushi.” Littafin ya dada da cewa: “Idan wanda ake cin zalinsa ya yi fushi, to, mai cin zalin ya yi nasara ke nan.”

 Gaskiyar al’amarin: Wani lokaci amsar da ta fi dacewa ita ce, ka yi banza da mutumin.

 Ka guji yin ramako. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi.”​—1 Bitrus 3:​9, Littafi Mai Tsarki.

 Abin da ya sa wannan nassin zai taimaka: Littafin nan Cyber-Safe Kids, Cyber-Savvy Teens ya ce: “Wanda yake fushi yana nuna cewa shi rago ne kuma hakan zai ba wa mai cin zalin damar ci gaba da abin da yake yi.” Idan ka rama za ka sa al’amarin ya dada muni.

 Gaskiyar al’amarin: Kar ka kara wa al’amarin wuta.

 Ka yi tunanin abin da za ka yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku rinjayu ga mugunta.” (Romawa 12:21) Akwai abin da za ka iya yi don a daina cin zalinka, ba tare da ka sa al’amarin ya dada muni ba.

 Ga wasu misalai:

  •    Ka hana sakonninsa shigowa wayarka. Littafin nan Mean Behind the Screen ya ce: “Ba za ka san abin da ke cikin sakon da aka tura maka ba idan ba ka karanta ba.”

  •   Ko da ba ka karanta sakon ba, ka adana shi a matsayin shaida. Irin sakonnin da za ka iya adanawa su ne sakonnin zagi ta tes ko imel ko sakonnin da ake yadawa a dandalin intane da dai sauransu.

  •   Ka gaya wa mai cin zali ta intane ya daina yin haka. Za ka iya tura masa sako cewa:

    •  “Kada ka kara tura min wani sako.”

    •  “Ka share abin da ka saka a dandalina.”

    •  “Idan ba ka daina ba, zan dauki matakan da za su tilasta maka ka daina.”

  •   Ka kasance mai gaba gadi. Ka rika tunanin abubuwan da ka iya yi ba wadanda ba ka iya ba. (2 Korintiyawa 11:6) Masu cin zali ta intane suna kama da azzalumai na zahiri da suke neman matsorata.

  •   Ka gaya wa wani da ya manyanta. Iyayenka ne ya kamata ka soma gaya musu. Za ka iya kai karar mai cin zalin a dandalin da yake amfani da shi. Idan yanayin ya yi tsanani, sai kai da iyayenka ku kai kara a makarantarku ko wajen ‘yan sanda ko kuma kotu.

 Gaskiyar al’amarin: Akwai matakan da za ka iya dauka don a daina cin zalinka ko wadanda za su rage yadda cin zali yake shafanka.