Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Ya Dace na Auri Wannan Mutumin Kuwa?

Ya Dace na Auri Wannan Mutumin Kuwa?

 Kin sami wani da ya dace ya zama miki abokin auren? Yaya za ki sani ko mutumin ya dace miki?

 Ya kamata ki bincika sosai ba sama sama kawai ba. Saboda wani yaro n da yake da farin jini kila marar dabi’a ne kyakyawar yarinya kila marar gaskiya ce. Za ka so wata da za ku yi cudanya mai kyau wadda kun cancanci juna, halayenku kuma ya jitu sosai.​—Farawa 2:18; Matta 19:4-6.

Ki Yi Lura Sosai

 Ki yi bincike sosai game da wanda ki ke so. Amma ki mai da hankali! Za ki iya zabi ki ga abin da ki ke son gani daga halinsa. Saboda haka kada ki yi garaje. Ki yi kokari ki fahimci mutumin sosai.

 Mutane da yawa da suke fitar zance ba sa lura sosai. Maimako, sai ka ga nan da nan sun ambaci wani abin da biyun suke so: “Wakar da nake so ita shi ma yake so.” “Wasanninmu iri daya.” “Duk abin da muke so dai iri daya ne!” Amma, ya kamata ki yi bincike sosai ba sama sama kawai ba. Kina bukatar ki san “boyayyen mutum na zuciya.” (1 Bitrus 3:4; Afisawa 3:16) Ya fi kyau ku lura da yadda kuke ji sa’ad da wata jayayya ta taso tsakaninku maimakon maida hankali ga halayenku da ke iri daya kawai.

 Ga wani misali:

  •   Idan jayayya ta taso, yaya wannan mutumin yake bi da al’amari, yana nace sai abin da ya ce ne, ko kuma kila ma yi ta “fushi” ko ya yi “keta”? (Galatiyawa 5:19, 20; Kolosiyawa 3:8) Ko kuma shi mutum ne akida da yake tunanin kirki babu wata jayayya sa’ad da ba a karya doka ba?—Yaƙub 3:17.

  •   Mutumin yana yawan neman ya mallake wani, kuma mai mugun kishi ne? Yana son sani duk inda za ki ko kuma son sanin duk abin da ki ke yi? Nicole ya ce: “Na taba jin labarin yadda wasu da suke fitar zance suke fada saboda wai wane bai tambaya ko yaya wane yake ba. Wannan alamar za a sami matsala.”—1 Korintiyawa 13:4.

  •   Mene ne wasu suke fada game da mutumin? Yana da kyau ki bincika daga wadanda suka manyanta a cikin ikilisiya da suka san shi da dadewa. Ta yin haka za ki iya sanin ko ana ‘yabonta’ ko shi.—Ayyukan Manzanni 16:1, 2.