Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Taimaka Mini?​—Sashe na biyu: Ka Mai da Karatun Littafi Mai Tsarki Ya Zama Abin Marmari

Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Taimaka Mini?​—Sashe na biyu: Ka Mai da Karatun Littafi Mai Tsarki Ya Zama Abin Marmari

 Wani matashi mai suna Will ya ce, “karatun Littafi Mai Tsarki zai iya sa mutum ƙyuya, idan ba ka san yadda za ka bi da shi ba.”

 Za ka so ka san sirrin yadda za ka ji daɗin karatun Littafi Mai Tsarki? Wannan talifin zai taimaka maka.

 Ka yi marmarin labaran da ke Littafi Mai Tsarki

 Ka sa hankalinka sosai cikin abin da ka ke karatu. Za ka iya yin amfani da wannan:

 1.   Ka zaɓi wani labari cikin Littafi Mai Tsarki da za ka so ka yi nazarinsa. Za ka iya zaɓan wani labari ko wani wuri cikin Lingila, ko kuma wani labari daga wasan kwaikwayon Littafi Mai Tsarki da za a saurara a jw.org.

 2.   Ka karanta labarin. Za ka iya karanta shi kai kaɗai, ko kuma karanta da murya tare da abokai ko kuma iyalinka. Mutum ɗaya zai iya karanta sashen ainihin wanda yake bada labarin sai sauran su karanta matsayin wasu.

 3.   Ka gwada wasu cikin shawarwarin nan:

  •   Ka zana hotuna da zai kwatanta labarin. Ko kuma ka zana labarin yadda yake bi da bi yadda zai kwatanta daidai aukuwar. Ka rubuta ɗan bayani a kowane hoto don ya bayyana abin da ke faruwa.

  •   Ka zana abubuwan da za ku yi zance akai. Alal misali, yayinda ka ke karatu game da wani mai aminci, ka haɗa halaye da ayyuka tare da albarkun da ya ko ta samu.

  •   Ka mai da batun ya zama wani sabon labari. Ka kuma ba da labarin ta hanyoyi dabam-dabam, ka “gana” da ainihin waɗanda suke cikin labarin da kuma waɗanda suka shaida abin da ya faru ido da ido.

  •   Ka yi tsammanin yadda karshen labarin zai zama da a ce wani cikinsu ya tsai da wani shawara da ba daidai ba. Alal misali, ka yi la’akari da yadda Bitrus ya musunci sanin Yesu. (Markus 14:66-72) Dā me ya kamata Bitrus ya yi lokacin da aka gano shi?

  •   Za ka ma iya kalubalance kanka, ka rubuta wani labarin Littafi Mai Tsarki a wata hanya dabam. Ka haɗa da darussa da za a iya koya daga labarin.​—Romawa 15:4.

   Za ka iya jin dadin karatun Littafi Mai Tsarki!

 Ka yi bincike!

 In ka bincike dalla-dalla, za ka iya samu abubuwa masu tamani cikin labarin. A gaskiya, a wani lokaci za ka iske cewa kalma ɗaya ko biyu na cikin Littafi Mai Tsarki na da muhimmanci.

 Alal misali, ka gwada Matta 28:7 da Markus 16:7.

 •    Me ya sa Markus ya bayana dalla-dalla cewa ba da daɗewa ba Yesu zai bayyana ga almajiransa “da kuma Bitrus”?

 •  Abin taimako: Markus bai shaida waɗannan aukuwan ba; ya samo bayanin daga wurin Bitrus ne.

 •  Abu mai tamani: Me ya sa zuciyar Bitrus ya kwanta sa’ad da ya ji cewa Yesu yana son ganin shi kuma? (Markus 14:66-​72) Ta yaya Yesu ya nuna cewa shi aminin Bitrus ne sosai? Ta yaya za ka bi misalin Yesu kuma zama abokin kirki ga wasu.

 Idan ka mai da karatun Nassosi abin marmari kuma kana bincike su dalla-dalla, za ka ji daɗin karatun Littafi Mai Tsarki sosai.