Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

In Bar Makaranta Ne?

In Bar Makaranta Ne?

 “Na ki jinin makaranta!” Idan kai ma haka kake ji, za ka iya soma tunanin barin makaranta. A wannan talifin, za mu tattauna wasu shawarwarin da za ka iya yankewa.

 Me ya sa wasu suke barin makaranta?

 Ga wasu dalilai da kwararru suka bayar da ke sa wasu barin makaranta:

 •   Koyan abu yana musu wuya. ‘Sai faɗi jarrabawa nake yi.’

 •   Halin ba ruwanmu. ‘Ban ga amfanin abin da nake koya ba.’

 •   Rashin kudi. ‘Ina bukatar in yi aiki don in tallafa wa iyalina.’

 Ka yi tunanin sakamakon

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai hankali yakan yi tunani kafin ya fara wani abu.” (Karin Magana 14:15) Mene ne hakan ya koya mana? Idan kana tunanin barin makaranta, ka yi tunanin sakamakon yin hakan.

 Ka tambayi kanka:

 •   ‘Idan na bar makaranta, zan iya samun aiki a nan gaba?’

   Wata mai suna Julia ta ce: “Ka tuna cewa wata rana za ka bukaci ka nemi aikin yi don ka kula da iyalinka. Ta yaya za ka yi hakan idan yawancin mutane suna daukan wadanda suka gama makarantar sakandare ne a aiki?”

 •   ‘Idan na bar makaranta, zai yi mini sauki in jimre matsaloli da zan iya fuskanta a gaba?’

   Wani mai suna Daniel ya ce: “Makaranta za ta iya koya maka yadda za ka yi rayuwa idan ka yi girma. Mutanen da za ka hadu da su da matsalolin da za ka fuskanta da kuma irin aikin da za ka yi, duk za su yi kama da abin da ka fuskanta a makaranta.”

 •   ‘Idan na bar makaranta, zan iya koyan aikin da zan yi sa’ad da na yi girma?’

   Wata mai suna Anna ta ce: “Za ka iya dauka cewa abin da kake koya a makaranta bai da amfani a lokacin da kake koyan su, amma sa’ad da ka kai shekara 23 kuma ka soma lissafta kudaden da kake samu, za ka gode Allah cewa ka koyi yin lissafi a makaranta.”

 Abin da ya dace ka yi

 •   Ka nemi taimako. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yawan masu ba da shawara yakan kawo wa al’umma zaman lafiya.” (Karin Magana 11:14) Idan ka ga ba ka cin jarrabawa, ka yi magana da iyayenka ko malaminku ko mai ba da shawara a makaranta ko kuma wani abokinka da ya manyanta don su ba ka shawara.

   Wani mai suna Edward ya ce: “Ka gaya wa malaminku idan yana yi maka wuya ka ci jarrabawa. A wasu lokuta, za ka iya ganin kamar malaminku ne yake sa ba ka cin jarrabawa. Amma sau da yawa za ka ga cewa neman shawararsa ce za ta taimaka maka ka sami ci gaba.”

 •   Ka yi tunanin yadda abubuwan da ka koya za su taimaka maka a gaba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwamma karshen abu da farawarsa.” (Mai-Wa’azi 7:⁠8) Kafin ka gama makaranta, za ka koyi abubuwan da ake koyarwa a makaranta. Kari ga haka, za ka koyi halaye da ayyuka da za su taimaka maka a rayuwa.

   Wata mai suna Vera ta ce: “Mai yiwuwa ba za a bukace ka ka yi nazari don jarrabawa bayan ka gama makaranta ba, amma idan ka koyi yadda za ka rika magance matsaloli a makaranta, hakan zai taimaka maka ka iya magance matsaloli a rayuwa.”

  Barin makaranta yana kama da sauka daga jirgin ruwa kafin ya isa tasha, za ka iya yin da-na-sani!

 •   Ka yi tunanin matakin da kake so ka dauka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk mai yin abu da gaggawa lallai ba zai sami biyan bukata ba.” (Karin Magana 21:⁠5) Kada ka yi saurin yanke shawara cewa barin makaranta shi ne ya fi dacewa.

   Wani mai suna Benjamin ya ce: “A makaranta za ka koyi yin aiki da kwazo, da yadda za ka rika magance matsaloli da kuma yin aiki tare da wasu. Za ka amfana sosai a nan gaba idan ka gama makaranta.”

 Gaskiyar batun: Kafin ka gama makaranta, za ka koyi abubuwan da za su taimaka maka sa’ad da ka yi girma.