Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Zan Guji Mugun Tunani?

Ta Yaya Zan Guji Mugun Tunani?

 Ta yaya kake daukan kanka?

 •   Mai kyakkyawan zato

   Valerie ta ce: “Ina kokari in rika farin ciki kuma ba na barin abu ya bata min rai. Ina so in rika murmushi da kuma farin ciki a kowace rana.”

 •   Mai shakka

   Rebecca ta ce: “Sa’ad da wani abu mai kyau ya faru, nakan yi shakka.”

 •   Mai daukan abubuwa yadda suke

   Anna ta ce: “Idan ina da ra’ayi cewa kome zai yi kyau, zan yi sanyin gwiwa idan hakan bai faru ba. Idan ina da ra’ayi cewa mugun abu zai faru, zan rika bakin ciki a kowane lokaci. Amma daukan abubuwa yadda suke yana taimaka min.”

 Me ya sa yake da muhimmanci?

 Littafi Mai Tsarki ya ce “zuciya mai murna kullum tana cikin jin dadi.” (Karin Magana 15:15) Mutane da suke guje wa mugun tunani, sukan kasance da ra’ayi mai kyau kuma sun fi farin ciki. Kuma sukan sami abokai sosai, domin ba wanda yake so yin abokantaka da mutane da suke bakin ciki a kowane lokaci.

 Ko da kana da ra’ayi cewa kome zai yi kyau, akwai abubuwan da za su shafe ka. Alal misali:

 •   A labarai kana yawan ji game da yake-yake da ta’addanci ko kuma aikata mugunta.

 •   Kana iya yin fama da matsaloli a iyalinka.

 •   Babu shakka, kana da ajizanci da kake fama da shi.

 •   Watakila abokinka ya bata maka rai don abin da ya fada.

 Maimakon ka yi banza da wadannan matsaloli ko kuma ka rika damuwa da su, ka yi kokari ka dauke su a matsayin abubuwa ne da ke faruwa a yau. Kasancewa da irin wannan ra’ayin zai sa ka guji yawan mugun tunani kuma ka jimre da matsalolin da kake fuskanta ba tare da yin sanyin gwiwa ba.

Za ka iya bi da matsaloli a rayuwa da tabbaci cewa da shigewar lokaci, za ka magance su

 Abin da za ka iya yi

 •   Ka kasance da ra’ayin da ya dace game da ajizancinka.

   Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babu mutum mai adalci a duniyar nan mai aikata abin da yake daidai a kowane lokaci, ba tare da yin zunubi ba.” (Mai-Wa’azi 7:20) Hakika, da yake kana da kasawa kuma kana yin kuskure ya nuna cewa kai dan Adam ne, kuma hakan bai rage maka mutunci ba.

   Yadda za ka kasance da ra’ayin da ya dace: Ka yi kokari ka yi canje-canje, amma ka tuna cewa kai ajizi ne. Wani matashi mai suna Caleb ya ce: “Ina kokari kada in rika mai da hankali ga kurakuraina don yin hakan zai iya sa ni sanyin gwiwa. Maimakon haka, nakan yi kokari na koyi darasi daga kuskuren.”

 •   Ka guji gwada kanka da mutane.

   Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada mu zama masu girman kai ko masu tā da hankalin juna ko masu kishin juna.” (Galatiyawa 5:26) Kallon hotunan da abokanka suka saka a dandalin sada zumunta na biki da ba su gayyace ka ba zai iya sa ka bakin ciki. Hakan zai sa ka rika ganin cewa abokanka ba sa son ka.

   Yadda za ka kasance da ra’ayin da ya dace: Ka amince cewa ba kowane biki ba ne za a gayyace ka. Ban da haka, hotunan da kake gani a dandalin sada zumunta suna nuna wasu bangarorin rayuwan mutane. Wata matashiya mai suna Alexis ta ce: “A yawancin lokaci, mutane sukan saka hotunan abubuwa masu kyau da suka faru da su a dandalin sada zumunta. Ba sa fadin matsalolinsu.”

 •   Ka zama mai son zaman lafiya, musamman a iyalinka.

   Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi iyakar kokarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.” (Romawa 12:18) A yawancin lokuta, ba za ka iya canja abin da mutane suke yi ba, amma za ka iya canja abin da kake yi. Kana iya zaban ka yi zaman lafiya da mutane.

   Yadda za ka kasance da ra’ayin da ya dace: Ka yi kokari kada ka zama mai jawo matsala a iyalinka, amma ka yi zaman lafiya da su yadda za ka yi da abokanka. Wata matashiya mai suna Melinda ta ce: “Dukanmu ajizai ne, kuma a wasu lokuta, muna iya bata wa juna rai. Mu ne za mu zaba ko za mu zauna lafiya da mutane ko a’a.”

 •   Ka zama mai nuna godiya.

   Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku kuma kasance masu godiya.” (Kolosiyawa 3:15) Idan kai mai nuna godiya ne, za ka mai da hankali ga abubuwa masu kyau da suka faru da kai, ba abubuwa marasa kyau da suka faru da kai ba.

   Yadda za ka kasance da ra’ayin da ya dace: Ka yarda da matsalolinka, amma kada ka mance da abubuwa masu kyau da suka faru a rayuwarka. Wata matashiya mai suna Rebecca ta ce: “A kowace rana, nakan rubuta abu mai kyau da ya faru da ni. Ina so ina tuna wa kaina cewa ko da ina da matsaloli, akwai abubuwa masu kyau da zan yi tunani a kai.”

 •   Ka yi tunanin irin abokan da kake da su.

   Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zama da mugaye yakan bata halayen kirki.” (1 Korintiyawa 15:33) Idan abokanka masu bakar magana ne, halinsu zai shafe ka.

   Yadda za ka kasance da ra’ayin da ya dace: Sa’ad da abokanka suke fuskantar matsaloli masu tsanani, suna iya yin bakin ciki da kuma sanyin gwiwa na dan lokaci. Ka taimaka musu, amma kada ka bar matsalolinsu ta shafe ka ainun. Wata matashiya mai suna Michelle ta ce: “Bai kamata mu rika yawan abokantaka da mutanen da ke gunaguni game da yanayinsu ba.”

 Ka rika karanta abu da zai taimaka maka

 Muna zama a zamanin da Littafi Mai Tsarki ya ce “za a sha wahala sosai.” (2 Timoti 3:1) Shin yana maka wuya ka kasance da ra’ayin da ya dace don matsaloli da yawa da ke wannan duniyar? Ka karanta talifin nan “Me Ya Sa Muke Shan Wahala Sosai?