Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Shin, Kwarkwasa Tana da Hadari?

Shin, Kwarkwasa Tana da Hadari?

 Mece ce kwarkwasa?

 Wasu mutane suna ganin kamar kwarkwasa hanya ce da mutum zai iya fada ko ya nuna cewa yana kaunar wani ko wata. Amma laifi ne mutum ya nuna cewa yana kaunar wata ko wani? A’a. Wata mai suna Ann ta ce: “Idan mutum ya riga ya kai fita zance kuma ya ga wacce yake so, ba laifi ba ne ya nuna ko ya gaya mata cewa yana son ta, don ta hakan ne zai gane ko ita ma tana son shi.”

 A wannan talifin, za mu tattauna abubuwan da mutum zai iya yi da za su nuna cewa kwarkwasa yake yi, ba wai yana niyar yin aure ba ne.

 Wata mai suna Deanna ta ce: “Ba laifi ba ne ka ga wanda kake kauna kuma ka gaya masa ko ka nuna masa cewa kana kaunar sa. Amma ba zai dace ka kai shi kuma ka baro shi, duk a cikin sunan wasa ba.”

 Me ya sa mutane suke yin kwarkwasa?

 Wasu suna kwarkwasa don suna ganin hakan zai sa su ji kamar suna da aji. Wata mai suna Hailey ta ce: “Wani lokaci idan mutum ya gane cewa yana iya jan hankalin mutane, hakan yana sa shi ya ci gaba da yi kwarkwasa.”

 Idan kwarkwasa ce kake yi da mutum, hakan ya nuna cewa ba ka damu da yadda mutumin yake ji ba. Idan kuma da gangan kake yi don kana ji dadin yi hakan, to ya kamata ka sake tunani. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wauta abin murna ce ga wanda ya rasa hikima.”​—Misalai 15:21.

 Hailey ta dada da cewa: “Wani lokaci ana fara yin kwarkwasa ba tare da sani ba, amma a karshe zai iya sa mutum ya fada cikin matsala.”

 Mene ne hadarin yin kwarkwasa?

 •   Yin kwarkwasa yana bata sunan mutum.

   Wani mai suna Jeremy ya ce: “Duk wacce take jin dadin yi kwarkwasa ba ta da wayo kuma ba za ta kasance a sake ba. Hakan zai sa ka ga cewa ba ta da gaskiya kuma tana kokari ne kawai ta ci kudinka ko ta yi wasa hankalinka.”

   Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kauna . . . ba ta bida ma kanta.”​—1 Korintiyawa 13:​4, 5.

   Ka yi tunani a kan wannan: Wadanne abubuwa ne zan iya yi da za su nuna cewa ina son yin kwarkwasa?

 •   Yin kwarkwasa zai iya sa wani ko wata bakin ciki.

   Wata mai suna Jaqueline ta ce: “Na tsane duk wanda na gane cewa shi mai son yin kwarkwasa ne. Don ina ji kamar yana min magana ne don ni mace ce. Kuma idan mutum yana son yin kwarkwasa da ni, hakan ya nuna cewa ba ya kauna ta, amma yana neman abin da zai sa shi ya ji kamar yana da aji ne kawai.”

   Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada kowa shi bida ma kansa, amma abin da za ya amfana makwabcinsa.”​—1 Korintiyawa 10:24.

   Ka yi tunani a kan wannan: Ka taba ji kamar wata tana kaunarka, amma daga baya ka gane cewa kwarkwasa ce kawai take yi? Idan e ce amsarka, yaya ka ji daga baya? Me za ka yi don kar ka jefa wata a cikin irin wannan yanayin?

 •   Kwarkwasa za ta iya sa mutum ya rasa masoyinsa.

   Wata mai suna Olivia ta ce: “Zai yi wuya in fita zance ko in aure mai son yin kwarkasa. Don ba zan iya gaskata da shi ba.”

   A cikin Littafi Mai Tsarki Dauda ya ce: “Ba ruwana da munafukai.”​—Zabura 26:​4, Littafi Mai Tsarki Juyi Mai Fitar da Ma’ana.

   Ka yi tunani a kan wannan: Su waye ne suke son masu yin kwarkwasa? Irin mutumin da kake so ya zama amininka kenan?