Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Zan Yi don A Daina Takura Mini?

Me Zan Yi don A Daina Takura Mini?

 Me ya sa iyaye suke sa baki a batun yaransu?

 Iyayenka suna cewa sun damu da kai shi ya sa. Amma kai kuma kana ganin shisshigi suke yi. Alal misali:

  •   Wata matashiya mai suna Erin, ta ce: “Mahaifina yakan karbi wayata kuma ya ce in ba shi lambar ba da izinin shiga wayata, sa’an nan ya karanta dukan sakonni da aka aiko mini. Idan na ce a’a zai ga kamar ina boye wani abu ne.”

  •   Denise, wadda yanzu ta wuce shekaru 20 ta tuna yadda mahaifiyarta take bincika yadda Denise take amfani da kudi a wayarta. Denise ta ce: “Takan bincika dukan lambobin da na kira sa’an nan ta tambaye ni ko su waye ne ke da lambobin da kuma abin da muka tattauna.”

  •   Kayla, wata ’yar shekara goma sha tara ta ce akwai ranar da mahaifiyarta ta karanta littafin da take rubuta yadda take ji a ciki. Kayla ta ce: “Littafin yana dauke da yadda nake ji, har ma game da mahaifiyata! Hakan ya sa na daina rubutu a littafin.”

 Gaskiyar al’amarin: Iyayenka ne suke da hakkin kula da kai kuma ba za ka iya gaya musu hanyar da za su yi hakan ba. Amma, za su iya wuce gona da iri? E, hakan zai iya faruwa. Albishirin shi ne akwai abubuwan da za ka iya yi don ka rage yadda kake ji kamar ana maka shisshigi.

 Abin da za ka iya yi

 Ka daina boye-boye. Littafi Mai Tsarki ya ce “mu yi gaskiya a cikin ayyukanmu duka.” (Ibraniyawa 13:18, New World Translation) Ka yi kokari ka yi hakan da iyayenka. Idan ba ka boye-boye, mai yiwuwa iyayenka ba za su rika sa baki a batunka ba.

 Ka yi tunanin wannan: Kai wanda da za a iya saurin yarda da kai ne? Kana bin dokoki da iyayenka suka kafa game da lokacin dawowa gida? Kana boye irin abokai da kake da su? Kana boye ayyukanka ne?

Delia ta ce: “Ina ba wa iyayena hadin kai ta wurin gaya musu duk abubuwan da nake yi. Hakan ya sa sun yarda da ni kuma sun daina yi mini shisshigi.”

 Ka yi hakuri. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku rika auna kanku.” (2 Korintiyawa 13:5, Littafi Mai Tsarki) Zai iya daukan lokaci kafin iyayenka su yarda da kai, amma kada ka daina kokartawa domin hakan zai kawo maka albarka.

 Ka yi tunanin wannan: Iyayenka su ma matasa ne a dā. Yaya kake ganin hakan zai shafi yadda suke damuwa da rayuwarka?

 Wani mai suna Daniel ya ce: “A ganina iyaye suna tuna da kurakuren da suka yi sa’ad da suke matasa, shi ya sa ba sa son yaransu su yi irin wadannan kuskuren su ma.”

 Ka yi kokari ka fahimci yadda iyayenka suke ji. Ka yi kokari don ka fahimci ra’ayin iyayenka. Littafi Mai Tsarki ya ce mace mai kirki “takan tsare al’amuran iyalinta da kyau,” ya kuma ce nagarin uba yana tabiyyartar da ’ya’yansa ta “hanyar Ubangiji.” (Misalai 31:27; Afisawa 6:4) Hakika, wajibi ne iyayenka su san yadda kake rayuwa domin hakan zai iya taimaka musu su cika wannan hakkin da aka ba su.

 Ka yi tunanin wannan: A ce kai mahaifi ne kuma ka san yadda matasa suke rayuwa, za ka kyale danka ko ’yarka ta yi abin da take so, ko kuma ka ce babu ruwanka?

  Wani mai suna James ya ce: “Sa’ad da kake matashi, za ka ji kamar iyayenka suna ‘matsa maka lamba’ ne. Amma yanzu da na yi girma, na fahimci dalilin da ya sa iyaye suke sa baki a maganata. Yadda za su nuna cewa suna kaunar ’ya’yansu ne.”