Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Zan Bi da Canje-canjen da Ke Aukuwa a Lokacin Balaga?

Ta Yaya Zan Bi da Canje-canjen da Ke Aukuwa a Lokacin Balaga?

 Oksana ta ce: “Lokacin balaga ba abu mai sauki ba ne wa ’yammata. Yana da zafi, yana iya sa ki ji kamar kina cikin datti kuma yana rikitar da mutum. Kai babu wani abu da ke da dadi game da lokacin balaga.”

 Brian ya ce: “Nakan yi farin ciki sai nan da nan in soma bakin ciki. Ban san ko haka yake faruwa da dukan ’yan maza ba, amma abin da ya faru da ni ke nan.”

 Lokacin balaga yana iya zama lokaci mai ban sha’awa da kuma lokaci mai ban tsoro. Ta yaya za ka iya bi da canje-canje da ke aukuwa a lokacin balaga?

 Mene ne ake nufi da lokacin balaga?

 A takaice, lokacin balaga lokaci ne da yara suke manyanta kuma hakan yana jawo sauye-sauye a jikinsu da kuma yadda suke ji. A wannan lokacin, yara suna zama a shirye don haihuwa. Yayin da mutum yake balaga, jikinsa na sakewa nan da nan kuma kwayoyin jikinsa za su manyanta da wuri.

 Hakan ba ya nufin cewa yaron yana shirye ya zama uba ko yarinyar tana shirye ta zama uwa. Amma lokacin balaga alama ce da ke nuna cewa yaro ko yarinya tana fita daga halin yarinta zuwa halin manyantaka, kuma hakan na iya sa su ji tsoro da bakin ciki.

 Wasa kwakwalwa: A ganinka, daga wace shekara ce yaro ko yarinya take soma balaga?

 • 8

 • 9

 • 10

 • 11

 • 12

 • 13

 • 14

 • 15

 • 16

 Amsa: Duka shekarun nan shekaru ne da yara za su iya soma balaga.

 Hakan yana nufin cewa hankalinka ba ya bukatar ya tashi idan kana gab da shekaru 15 ko 16 amma ba ka soma ganin alamun balaga a jikinka ba tukun, ko kuma kana kasa da shekaru 10 amma ka riga ka soma ganin alamun balaga. Babu wanda zai iya sarrafa lokacin balaga.

Lokacin balaga yana kama da hawan wani babban lilo da ke jujjuyawa, kana iya jin dadi da kuma tsoro a lokaci daya. Amma za ka iya bi da wadannan canje-canjen da kyau

 Canje-canje a jiki

 Canjin da ake fara gani idan yara suka soma balaga shi ne girma nan take. Matsalar ita ce, gabobin jiki ba sa girma a lokaci daya. Saboda haka, wadanda suka soma balaga suna iya yin abubuwa babu tsari. Amma da wucewar lokaci, abubuwa za su daidaita.

 Kari ga wannan, akwai canje-canje da ke aukuwa a lokacin balaga.

 Sauye-sauyen da suka shafi samari:

 •   Girman al’aura

 •   Fitar gashi, wato gemu, saje, gashin baki, gashin kirji da gashin hammata da na mara

 •   Tsagewar murya

 •   Mafarki, wato, fitar maniyyi

 Sauye-sauyen da suka shafi ’yammata:

 •   Fitar nono

 •   Fitar gashi, wato gashin hammata da na mara

 •   Haila, wato al’ada

 Sauye-sauyen da ke shafan samari da ’yammata a lokacin balaga:

 •   Wārin jiki, saboda kwayoyin cuta (bacteria) a cikin zufa.

   Abin da zai taimaka: Za a iya rage wārin jiki ta wajen yin wanka a kai a kai da kuma yin amfani da turaren hammata.

 •   Kurajen fuska da kwayoyin cuta suke janyowa.

   Abin da zai taimaka: Ko da yake ba shi da sauki mutum ya kawar da kurajen fuska, wanke fuska a kai a kai da kuma yin amfani da sabulun wanke fuska zai iya taimakawa sosai.

 Canje-canje a yadda mutum yake ji

 Karin kwayoyin jiki da ke sa gabobin jiki su manyanta suna iya jawo sauyi a yadda yara suke ji, kuma wannan sauyin yana iya aukuwa nan take ba da wani shiri ba.

 Oksana ta ce: “Kina iya yin farin ciki yanzu, amma kafin ki sani sai ki soma kuka. A wasu lokatai kuma za ki iya yin fushi yanzu-yanzu, amma farat daya sai ki soma damuwa.”

 A lokacin da yara suka soma balaga, sukan damu ainun da jikinsu, har su ga kamar kowa na zuba musu ido don ya kushe su. Kuma yadda suke girma da sauri-sauri yana dada sa su jin hakan.

 Janice ta ce: “A lokacin da na soma balaga, nakan sa manyan kaya kuma in tankware jikina sa’ad da nake tafiya. Duk da cewa na san dalilin da ya sa jikina yake canjewa, hakan ya sa ni jin kunya. Wani abu ne da ban saba da shi ba sam.”

 Mai yiwuwa sauyi mafi girma da yaran da suka balaga suke fuskanta shi ne a yadda suke soma sha’awar wadanda ba jinsinsu ba.

 Alexis ta ce: “Na daina ji kamar duka ’yan maza suna da ban haushi. Na soma kallon wasu da sha’awa kuma na soma tunanin fita zance da wani. Kai, hirar da muka soma jin dadin yi sosai shi ne na fita zance.”

 Amma wasu da suka soma balaga suna iya soma sha’awar wadanda suke da jinsi daya da su. Idan hakan ya faru da kai, kada ka dauka cewa ka zama dan luwaɗi. A yawancin lokatai, wannan sha’awar tana wucewa.

 Alan ya ce: “Na soma sha’awar ’yan maza domin ina yawan kallonsu don in gwada kaina da su. Sai can bayan na zama matashi kafin na soma sha’awar ’yammata. Amma yanzu na daina sha’awar ’yan maza.”

 Abin da za ka iya yi

 •    Ka kasance da tunani mai kyau. Balaga lokaci ne mai muhimmanci ga dukan yara domin suna bukatar sauye-sauye da ke aukuwa a lokacin. Za ka iya samun karfin gwiwa daga kalmomin Dauda da ya ce: “Kirata abin ban tsoro ce, abin al’ajabi ce kuwa.”—Zabura 139:14.

 •   Ka guji gwada kanka da wani kuma ka daina damuwa ainun da siffarka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum yana duban [‘kyan tsari,’ NW], amma Ubangiji yana duban zuciya.”—1 Sama’ila 16:7.

 •   Ka rika fita don motsa jiki kuma ka sami isasshen barci. Idan ka sami isasshen barci, hakan zai taimaka maka ka daina fushi da damuwa da kuma gajiya ainun.

 •   Kada ka yarda da kowane mummunan tunanin da ya zo zuciyarka. Ba kowa ba ne yake zuba maka ido. Ko da mutane sun yi magana game da canje-canje da suke gani a jikinka, kada ka bar hakan ya daga maka hankali. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Kada ka kula da dukan maganar da ake fadi.’—Mai-Wa’azi 7:21.

 •   Ka koyi yadda za ka kwantar da sha’awar yin jima’i idan ta taso domin kada ka fada jaraba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku guji fasikanci. . . . Mai yin fasikanci yana daukar alhakin jikinsa ne.”—1 Korintiyawa 6:18, Littafi Mai Tsarki.

 •   Ka tattauna da iyayenka ko kuma wani da ya manyanta. Hakan ba zai kasance maka da sauki ba, amma za su iya ba ka shawarar da za ta taimaka maka sosai.—Misalai 17:17.

 Gaskiyar al’amarin: Lokacin balaga yana tattare da kalubale. Amma lokaci ne da za ka manyanta a zahiri, kuma za ka manyanta a tunaninka da yadda kake ji da kuma a dangantakarka da Jehobah.—1 Sama’ila 2:26.