Koma ka ga abin da ke ciki

Nakan Yi Sha’awar Irin Jinsina—Yana Nufin Ni Dan Daudu Ne?

Nakan Yi Sha’awar Irin Jinsina—Yana Nufin Ni Dan Daudu Ne?

 Ko kadan!

 Gaskiyar: A yawancin lokaci, yin sha’awar irin jinsinka abu ne mai wucewa.

 Abin da Lisette, ’yar shekara 16, wadda ta taba sha’awar wata yarinya ta ce ke nan. Ta ce: “A lokacin da ake koyar da mu a makaranta game da ilimin halittu, na koyi cewa a lokacin kuruciya, sinadarin da ke sa jiki girma yana canzawa sosai. Na tabbata cewa idan yawancin matasa sun san yanayin jikinsu, za su fahimci cewa sha’awar irin jinsinsu wani abu ne na dan lokaci da za ya zo ya wuce kuma ba za su ji wani matsin zama dan daudu ba.”

Dukan matasa suna da zabi, ko su bi mumunar ra’ayin duniya game da jima’i ko kuma su bi tafarkin dabi’a mai kyau da ke cikin Kalmar Allah

 Amma idan sha’awar irin jinsinka ta ki wucewa fa? Mugunta ce ta sa Allah ya ce wanda yake sha’awar irin jinsinsa ya guje wa luwadi?

 Idan ka ce e ga wannan tambayar ta karshe, kana tunanin da bai dace ba irin na ’yan Adam da suka ce mutum ya bi sha’awarsa ta jima’i. Littafi Mai Tsarki ya daraja mutane ta wurin ba su tabbaci cewa suna iya kin bin mummunar sha’awarsu ta jima’i.​—Kolosiyawa 3:5.

 Mizanan Littafi Mai Tsarki suna da kyau. Ya ce wadanda suke da sha’awar yin luwadi su yi abin da aka gaya wa wadanda suke sha’awar yin zina su yi—wato, su “guje wa fasikanci.” (1 Korintiyawa 6:18) Gaskiyar ita ce, miliyoyin wadanda suke da sha’awar yin zina amma suna da niyyar bin mizanan Littafi Mai Tsarki suna kame kansu ne kome tsananin jarabar. Wadanda suke da sha’awar luwadi ma za su iya yin hakan idan suna so su faranta wa Allah rai da gaske.​—Kubawar Shari’a 30:19.