Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Ya Sa Ba Ni da Abokai

Me Ya Sa Ba Ni da Abokai?

Kana intane kana kallon hotunan wani fati da aka yi. Abokanka duka sun hallara kuma suna liyafa. Amma wani ba ya wurin. Wane ne wannan? Kai ne!

Hakan ya sa ka bakin ciki, sai ka tambayi kanka: ‘Me ya sa ba a gayyace ni ba?’

Kana ganin an yi ban da kai! Kamar dai dangantakarka da wasu duk ya rushe kamar rumfar kara. Kana bakin ciki don ka kadaita, sai ka tambayi kanka, ‘Me ya sa ba ni da abokai?’

 Wasa kwakwalwa a kan batun kadaici

 Gaskiya ko Karya

 1.   Ba za ka taba jin kadaici ba idan kana da abokai da yawa.

 2.   Ba za ka taba jin kadaici ba idan kana shigar dandalin intane.

 3.   Ba za ka taba jin kadaici ba idan kana yawan aika sakonni da yawa ta wayar selula.

 4.   Ba za ka taba jin kadaici ba idan kana taimaka wa mutane.

 Amsar dukan wadannan kalamai hudu karya ce.

 Me ya sa?

 Gaskiya game da abokantaka da kuma kadaici

 •   Idan mutum yana da abokai da yawa ba zai hana shi jin kadaici ba.

    Anne ta ce: “Na damu da abokai na sosai, amma wani lokaci ina ganin kamar ba su damu da ni. Abin da zai fi sa ka ji kadaici shi ne idan kana da abokai da yawa amma ba sa nuna suna kaunarka ko kuma cewa sun damu da kai ba.”

 •   Shiga dandalin intane ba zai sa ka daina jin kadaici ba.

   Elaine ta ce: “Wasu mutane suna tara abokai yadda wasu ke tara kayan adon daki. Amma cika daki da kayan ado ba zai sa wani ya ji kana kaunarsa ba. Idan abokanka ba na kirki ba ne, ba bambancinsu da kayan adon daki.”

 •   Yawan aika da sako a waya ba shi zai sa ka daina jin kadaici ba.

   Serena ta ce: “Wani lokaci idan kana jin kadaici sai ka rika duba wayarka kana tsammanin wani ya aika maka sako. Yanayin zai fi muni idan kana jin kadaici kuma babu wanda ya aika maka sako!”

 •   Taimaka wa wasu ba ya nufin cewa ba za ka taba jin kadaici ba.

   Richard ya ce: “Nakan yi wa abokaina kyauta sosai amma na lura cewa ba su taba ba ni kyauta ba sam. Ko da yake ba na nadama cewa na yi musu kyauta amma ina mamakin cewa ba su taba yi mini alheri ba.”

 Gaskiyar al’amarin: A takaice, kadaici yadda mutum yake tunaninsa ne. Wata matashiya mai suna Jeanette ta ce: “Halin mutum ne, ba koya ya yi ba.”

 Me za ka iya yi idan kana ji kamar ba ka da abokai kuma kana jin kadaici?

 Yadda za ka yi nasara

Ka kasance da gabagadinka.

 Jeanette ta ce: “Rashin tabbata da kanka ya iya sa mutumin jin kadaici. Yin abota ba shi da sauki idan kana yawan ji kamar ka fi wasu.”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.” (Galatiyawa 5:14) Idan muna so mu more abokantaka mai kyau, dole ne mu so kanmu kuma mu kasance da saukin kai.​—Galatiyawa 6:3, 4.

Ka guji yin shagwaba.

 Erin ta ce: “Kadaici yana kama da kasa. Idan ka ci gaba da jin kadaici, zai zama maka da wuya ka bar halin. Idan ka kyale jin kadaici ya zama abin jikinka, za ka soma shagwaba kuma mutane za su rika guje maka.”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kauna . . . ba ta bida ma kanta.” (1 Korintiyawa13:​4, 5) Gaskiyar ita ce, idan mun fi damuwa da kanmu kawai, ba za mu yi tunanin wasu ba kuma hakan zai sa mutane su guje mu. (2 Korintiyawa 12:15) Batun shi ne: Idan yadda wasu za su aikata ne zai sa ka yi nasara, to lallai ba za ka yi nasara ba! Irin furucin nan “Babu wanda yake kirana” da kuma “Babu wanda yake gayyata ta zuwa wani wuri” yana nufin cewa idan wasu ba su yi maka alheri ba, ba za ka yi farin ciki ba. Ba ka ganin cewa kana sa su ga cewa ka dogara ne gare su?

Kada ka yi abokantaka da kowane irin mutum.

 Brianne ya ce: “Wadanda suke jin kadaici suna so a nuna musu cewa ana son su ko da wanene yake yin hakan. Su dai a so su ne kawai. Wasu mutane za su nuna suna son ka amma daga baya su cuce ka. Lokacin ne za ka dada jin kadaici.”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima: Amma abokin tafiyar wawaye za ya cutu dominsa.” (Misalai 13:20) Mayunwaci yakan ci duk abin da ya samu. Haka ma yake da wadanda suke neman abokai, za su iya neman abokai a inda bai dace ba. Har za su iya fadawa a hannun wadanda za su damfare su da jin cewa suna bukatar abokantaka.

 A karshen: Babu wanda ba ya jin kadaici; wasu suna jin kadaici fiye da wasu. Kadaici yadda mutum yake ji ne kawai ko da yake yana shafan kowa. Sau da yawa, abin da muke tunaninsa ne ke sa mu jin kadaici, kuma za mu iya sarrafa tunaninmu.

 Ka kasance da halin da ya dace game da wasu, kuma kada ka so kanka. Jeanette ta ce: “Ba kowa ba ne zai iya zama abokinka na kud da kud da dadewa, amma dai za ka iya samun mutane da sun damu da kai. Mutane sun fi son haka. Abin da zai taimake ka guje wa jin kadaici ke nan.”

 Kana bukatar karin taimako ne? Ka karanta talifin nan “ Yadda za ka shawo kan shakkar abokantaka.” Ka kuma sauko da wannan PDF mai jigo “Jure da Kadaici.”