Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Yadda Za Ka Faranta Ran Malaminka

Yadda Za Ka Faranta Ran Malaminka

 Malami mai ba da wuya

 A kwana a tashi, kusan kowane dalibi zai gamu da malamin da a ganin shi malamin yana rashin adalci, yana da wuya a faranta masa rai ko kuma yana mugunta gar-da-gar.

 •   Wata ’yar shekara 21 mai suna Luis, ta ce: “Na taba yin wata malama da ke yawan tsine wa dalinbanta kuma ba ta daraja su. Tana yin hakan ne domin ta san cewa ta kusan yin ritaya kuma ba za a kore ta daga aiki ba.”

 •   Melanie, ’yar shekara 25, ta tuna yadda malamarta takan ci zalin ta kuma ta ce: “A cewar ta, tana muzguna mini ne domin ni ba mabiyar manyan addinai ba ce. Ta ce tana koya mini abin da zan yi ne idan aka ci zali na domin idan na girma, abin da zai faru ke nan.”

 Idan malaminka yana ba ka wuya, akwai abubuwa da za ka iya yi don kada ka gaji da makaranta. Ga wasu shawarwarin da za ka iya bi.

 Yadda za ka magance matsalar

 •   Ka canja salo. Abin da malamai suke bukata daga wurin dalibansu ya bambanta. Ka yi kokari ka san abin da malaminka yake bukata daga gare ka kuma ka yi abin.

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Bari mai hikima ya ji ya kara karbar koyarwa.”​—Karin Magana 1:5.

   Wani mai suna Christopher ya ce: “Na ga cewa ina bukatar in canja halina bisa ga abin da malamar take so. Don hakan, na yi iya kokarina in soma yin aikin da malamar ta ba ni yadda take so. Hakan ya sa mun sami zaman lafiya tsakaninmu.”

 •   Ka rika daraja malaminka. Ka daraja malamanka yayin da kake magana da su. Kada ka yi musu bakar magana ko da sun bata maka rai. Ka tuna cewa kai dalibinsu ne ba tsararsu ba.

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “A koyaushe, bari maganarku ta kasance da alheri da kuma dadin ji, domin ku san irin amsar da ya yi kyau ku ba kowa.”​—Kolosiyawa 4:6.

   Wata mai suna Ciara ta ce: “Dalibai ba sa yawan daraja malamai. Don hakan, idan ka daraja malaminka, zai iya canja ra’ayinsa game da kai.”

 •   Ka fahimci yanayin malaminka. Malamai mutane ne kamar ka. Hakan ya nuna cewa su ma suna da matsaloli da ke damun su. Don haka, kada ka ce, ‘Malamina mugu ne’ ko kuma ‘Malamina ya ki jinina’ ba tare da ka fahimci yanayinsa ba.

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Dukanmu mukan yi kuskure.”​—Yakub 3:2.

   Wata mai suna Alexis ta ce: “Aikin koyarwa bai da sauki. Tattara hankalin dalibai da kuma koyar da su ba abu mai sauki ba ne. A kullum ina kokari in zama dalibar kirki don kada in kara wa malamarmu ciwon kai.”

 •    Ka gaya wa iyayenka. Iyayenka suna so ka yi nasara a makaranta. Don haka, shawarar da za su ba ka za ta taimaka maka ka iya faranta ma malaminka rai.

   Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Idan babu shawara, shiri yakan lalace.”​—Karin Magana 15:22.

   Wata mai suna Olivia ta ce: “Iyayenka sun riga sun magance matsaloli da yawa a rayuwa fiye da kai. Don haka, idan ka bi shawararsu za ka yi nasara.”

 Hanyar da za ka tattauna da malaminka

 A wasu lokuta, za ka bukaci ka tattauna da malaminka a kan rashin jituwa da ke tsakaninku. Kada ka ji tsoro cewa abin zai kai ga rigima, don ba gardama ka je yi da shi ba. Tattaunawa za ku yi da shi, kuma za ka iya mamakin yadda hakan zai taimaka maka.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Mu yi iyakacin kokarinmu don mu aikata abin da zai kawo salama.”​—Romawa 14:19.

 Wata mai suna Juliana ta ce: “Idan kai kadai ne malamar take ba wa wuya, ka tambaye ta ko akwai laifin da ka yi mata. Amsar da za ta ba ka zai taimaka maka ka san abin da ya kamata ka yi.”

 Wani mai suna Benjamin ya ce: “Idan kana samun matsala da wani malaminku, ka tattauna batun da shi, kuma ka yi hakan da ladabi. Za ka iya tattaunawa da shi kafin a soma makaranta ko kuma bayan an tashi. Mai yiwuwa malamin ya yi tunani a kan batun kuma ya daraja ka domin yadda ka bi da batun.”

 LABARI

 Wata mai suna Maria ta ce: “A lokacin da na soma fadi jarrabawa, malamata ba ta yi kome don ta taimaka mini ba. Na so in bar makaranta domin ta sa rayuwa ta mini wuya.

 “Sai na nemi shawara a wurin wani malami. Ya ce mini: ‘Ba ku fahimci juna sosai ba. Kina bukatar ki gaya mata cewa kina neman taimako. Idan kin yi hakan, za ki taimaka ma wasu dalibai da suke tsoron yi mata magana su iya yin hakan.’

 “Ban so in yi hakan ba! Amma na yi tunani a kan abin da ya fada kuma na ga cewa gaskiyarsa ne. Dole ne in je in yi mata magana idan ina son canji.

 “Washegari, na je na same ta kuma na gaya mata cewa ina godiya don yadda take koyar da mu, kuma ina so in amfana sosai daga ajinta. Amma hakan yana mini wuya kuma ban san abin da zan yi ba. Ta ba ni shawarwari kuma ta ce idan ina so, za ta iya taimaka mini bayan an tashi aji ko kuma ta wurin tura min sakon imel.

 “Na yi mamaki sosai! Tattaunawar ta sa na inganta dangantakata da malamar, kuma hakan ya sa na ji dadin makaranta.”

 Shawara: Idan kana samun matsala da malaminka, ka dauki yanayin a matsayin dama da za ka koyi yadda za ka bi da matsaloli in ka yi girma. Katie, wata ’yar shekara 22 ta ce: “Bayan ka gama makaranta ma, za ka iya haduwa da mutane masu iko da za su iya ba ka wuya. Idan ka iya zaman lafiya da malamin da ke ba ka wuya, za ka iya zaman lafiya da mutanen da za su ba ka wuya a nan gaba.”