Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Ya Sa Kake bukatar Ka Rika Halartar Taro a Majami’ar Mulki?

Me Ya Sa Kake bukatar Ka Rika Halartar Taro a Majami’ar Mulki?

 Shaidun Jehobah suna halartar taro so biyu kowane mako a wurin ibadarsu da ake kira Majami’ar Mulki. Me ake yi a wurin, kuma ta yaya za ka amfana idan ka halarta?

 Me ake yi a Majami’ar Mulki?

 Majami’ar Mulki wuri ne da ake koyar da abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki da za su amfane mu a rayuwarmu. Taron da ake yi a wurin zai iya taimaka maka:

  •   Ka koyi gaskiya game da Allah

  •   Ka san dalilin da ya sa abubuwa suke faruwa a yau

  •   Ka zama mutumin kirki

  •    Ka sami abokai nagari.

 Ka sani? Ana kiran wurin taron Shaidun Jehobah Majami’ar Mulki domin Mulkin Allah ne ake tattaunawa a wurin.—Matiyu 6:9, 10; 24:14; Luka 4:43.

 Me ya sa kake bukatar ka rika Halarta?

 Abin da za ka koya zai taimaka maka. Ka’idodin Littafi Mai Tsarki da ake tattaunawa a taron Shaidun Jehobah zai taimaka maka ka zama mai ‘hikima.’ (Misalai 4:5) Hakan yana nufin cewa Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka rika tsai da shawarwari masu kyau a rayuwa. Kari ga haka, zai taimaka maka ka sami amsoshin wadannan tambayoyin:

 Ga kadan cikin wasu jawaban da ake yi a taronmu na karshen mako:

  •   Ka Sa Littafi Mai Tsarki Ya Yi Maka Ja-gora

  •   A Ina Ne Za Ka Sami Taimako a Lokacin Wahala?

  •   Abin da Mulkin Allah Yake Yi Mana a Yanzu

 Brenda ta ce: “Wani dan ajinmu ya halarci taronmu. Ya zauna tare da iyalinmu, kuma ya yi amfani da littattafanmu. Bayan haka, sai ya gaya mini cewa kalaman da mutane ke bayarwa lokacin da ake tattaunawa sun kayatar da shi. Ya kuma ce a cocinsu ba su da abubuwan nazarin Littafi Mai Tsarki kamar yadda muke da su.”

 Ka sani? Ba a biyan kudi don wurin zama a Majami’ar Mulki kuma ba a karban baiko.

 Tarayyar da kake yi a wurin zai karfafa ka. Littafi Mai Tsarki ya ce dalilin da ya sa Kiristoci suke bukatar su rika taro shi ne domin “karfafa wa juna zuciya.” (Ibraniyawa 10:24,25) Yin tarayya da mutanen da suke kaunar Allah da mutane na kawo kwanciyar hankali a wannan duniya da mutane suke son kansu kawai.

 Elisa ta ce: “Harkokin yau da kullum sukan gajiyar da ni kuma su sa ni bakin ciki, amma mutanen da ke Majami’ar Mulki sukan kwantar mini da hankali. Ina koma gida da farin ciki kuma ina shirye in fuskanci matsalolina.”

 Ka sani? Akwai ikilisiyoyin Shaidun Jehobah fiye da 120,000 a fadin duniya da suke yin taro a wurare fiye da 60,000. A kowace shekara, ana gina Majami’un Mulki kusan 1,500 domin masu halartan taro na dada karuwa. *

^ Don ka bincika wajen taro, ka je shafin “Taron Ikilisiya na Shaidun Jehobah” a wannan shafin sai ka bude “Ka Nemi Wurin da Ke Kusa da Kai”