Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Ya Sa Yake da Muhimmanci Ka Rika Fadin Gaskiya?

Me Ya Sa Yake da Muhimmanci Ka Rika Fadin Gaskiya?

 Abin da ya sa wasu ba sa fadin gaskiya

 A wannan zamanin, mutane suna ganin cewa fadin gaskiya ba shi da amfani. Ban da haka, wasu suna iya tunani cewa:

  •   ‘Idan ban yi wa iyayena karya ba, ba za su bar ni na yi wasu abubuwa ba.’

  •   ‘Idan ban yi satan amsa ba, ba zan ci wannan jarabawar ba

  •   ‘Idan ban saci wannan kayan ba, dole ne in yi ajiyar kudi don in saye shi.’

 Wasu kuma suna iya cewa, ‘Ai hakan ba laifi ba ne. Ai kowa ma yana rashin gaskiya’

 Amma hakan ba gaskiya ba ne. Mutane da yawa, har da matasa sun amince cewa fadin gaskiya yana da amfani kuma suna da hujja. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe.” (Galatiyawa 6:7) Saboda haka, abubuwan da muke yi suna iya kawo sakamako mai kyau ko marar kyau.

 Ka yi la’akari da mummunan sakamako na yin karya.

“Na yi wa mahaifiyata karya game da wani yaron da nake magana da shi. Tana da tabbaci cewa karya nake yi. Bayan na yi mata karya sau uku a kan batun, sai mahaifiyata ta yi fushi sosai. Hakan ya sa aka hana ni fita na sati biyu, aka kwace wayata kuma aka hana ni kallon talabijin na wata daya. Ban kara yi wa iyayena karya ba!”​—Anita.

 Ka yi tunani a kan wannan: Me ya sa zai dauki lokaci kafin mahaifiyar Anita ta amince da ita?

 Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Domin wannan fa sai ku rika fadi wa junanku da makwabtanku gaskiya, kuna kawar da karya.”​—Afisawa 4:25.

  “Na yi wa iyayena karya kuma na yi tunanin cewa na tsira amma sa’ad da suka sa na maimaita abin da na fada a dā. Saboda karyar da na yi, na kasa tunawa da ainihin abin da na gaya musu. Idan mutum yana fadin gaskiya, ba zai fuskanci wannan matsalar ba.”​—Anthony.

 Ka yi tunani a kan wannan: Da a ce Anthony ya dauki wani mataki da ya guji wannan abin kunya. Shin wane mataki ne wannan?

 Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Lebuna masu-karya abin ƙyama ne ga Ubangiji: Amma masu-aika gaskiya abin murnarsa ne.”—Misalai 12:22.

  “Ina da wata kawa da ta iya ba da labari sosai. Tana kara gishiri a labarinta. Ina kaunar ta kuma ba na yawan bincika ko abin da ta fada gaskiya ne. Amma, ba na yawan yarda da abin da ta fada.”​—Yvonne.

 Ka yi tunani a kan wannan: Ta yaya kara gishiri a labari da kuma fadan “kananan” karya ya shafi halin kawar Yvonne?

 Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.”—Ibraniyawa 13:18.

Idan harsashin gini ya tsage, hakan zai shafi ginin gaba daya, hakazalika, rashin gaskiya zai bata suna mai kyau da ka yi

 Fadin gaskiya yana da amfani

 Yanzu, bari mu yi la’akari da sakamako masu kyau na fadin gaskiya.

  “Wata mata tana tafiya a gabana kuma kudinta ya fadi ba ta sani ba. Na kira ta kuma na mayar mata da kudinta. Ta gode min sosai kuma ta ce: ‘Ke mai kirki ce. Ba kowa ba ne zai iya yin abin da kika yi ba.’ Na ji dadi da aka san cewa na yi abin da ya dace!”​—Vivian.

 Ka yi tunani a kan wannan: Me ya sa matar ta yi mamakin ganin cewa akwai masu fadin gaskiya? Ta yaya fadin gaskiya ya amfani Vivian?

  Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu-albarka ne su waɗanda ke . . . aika adalci kullayaumi.”—Zabura 106:3.

  “Ni da iyayena muna aikin shara. A wani lokaci mukan tsinci kudi a kasa sa’ad da muke share wani ofishi. Idan hakan ya faru, sai mu sa kudin a kan taburin da ke kusa da ofishin. Wata ma’aikaciya tana fushi da mu don muna hakan. Sai ta ce ‘ai wannan kwandala ne’! Duk da haka ta amince da mu sosai.”​—Julia.

 Ka yi tunani a kan wannan: Ta yaya halin Julia ya taimaka mata sa’ad da take neman wanda zai tsaya mata idan tana neman wani aiki?

 Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi kokari ka mika kanka yardaje ga Allah, ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gare shi.”—2 Timotawus 2:15.

  “An baya ni albashin kudin aikina fiye da yadda ya kamata. Ko da yake kudin zai biya mini bukata amma ba zan iya kashewa ba. Na gaya wa manajan mu kuma ta gode mini sosai. Kamfanin yana samun kudi sosai amma ba zan iya ajiye kudin b don zan rika jin na yi sata.”​—Bethany.

 Ka yi tunani a kan wannan: Shin akwai bambanci tsakanin yi wa kamfani sata da kuma yi wa mutum sata?

 Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mashiririci abin ƙyama ne ga Ubangiji: Amma asirinsa yana tare da masu-adalci.”—Misalai 3:32.