Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Mene ne Amfanin Yin Addu’a?

Mene ne Amfanin Yin Addu’a?

 Wani bincike ya nuna cewa, kashi 80 cikin 100 na matasa a Amirka suna yin addu’a, amma rabinsu ne kawai suke yin haka kullum. Watakila wasu daga cikinsu za su iya tambaya cewa: ‘Shin, ana yin addu’a ne don a ji sauki a zuciya kawai ko akwai wani dalili dabam?’

 Mece ce addu’a?

 Addu’a hanya ce na yin magana da Mahaliccin sama da kasa. Hakan babban gata ne, ko ba haka ba? A ko wane hali, Jehobah ya fi ’yan Adam, duk da haka “ba shi da nisa da kowane dayanmu.” (Ayyukan Manzanni 17:27) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.”​—Yakub 4:8.

 Yaya mutum zai iya kusantar Allah?

  •   Na daya shi ne ta wurin addu’a, wato hanyar da kake magana da Allah ke nan.

  •   Na biyu kuma shi ne ta wurin nazarin Littafi Mai Tsarki, wato yadda Allah yake “magana” da kai ke nan.

 Idan kana yin addu’a da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka iya zama aminin Allah.

 Wani mai suna Jeremy ya ce: “Yin magana da Jehobah yana daya daga cikin gatan da ‘yan Adam suke da shi, da babu kamarsa.”

 Wata mai suna Miranda ta ce: “A duk lokacin da na gaya wa Jehobah yadda nake ji, ina dada kusantarsa.”

 Allah yana jin addu’o’inmu kuwa?

 Ko da ka yi imani da Allah kuma kana yin addu’a, wani lokaci, za ka iya ji kamar Allah ba ya jin addu’arka. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah shi ne “Mai jin addu’a.” (Zabura 65:2) Kuma ya dada da cewa ku “zuba dukan alhininku a bisansa.” Me ya sa? “Domin yana kula da ku.”​—1 Bitrus 5:7.

 Ka yi tunani a kan wannan: Kana yin magana da abokanka a kai a kai? Za ka iya yin haka ma da Allah. Ka rika magana da shi kullum ta wurin addu’a kuma ka yi amfani da sunansa, Jehobah. (Zabura 86:​5-7; 88:9) Littafi Mai Tsarki ya umurce mu ‘mu yi addu’a ba fasawa.’​—1 Tasalonikawa 5:17.

 Wani mai suna Moises ya ce: “Idan ina addu’a, ina tattaunawa ne da Ubana na sama, kuma ina gaya masa dukan abin da ke zuciyata.”

 Wata mai suna Karen ta ce: “Ina iya gaya wa Jehobah duk abin da ke dami na kamar yadda zan gaya wa mahaifiyata ko aminiyata ta kud da kud.”

 Me zan iya rokan Allah ya yi mini?

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roko tare da godiya, ku bar roke rokenku su sanu ga Allah.”​—Filibiyawa 4:6.

 Amma yana da kyau ka yi addu’a game da abubuwan da ke damunka? Kwarai kuwa! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ka.”​—Zabura 55:22.

 Idan kana addu’a, bai kamata ka rika gaya wa Allah abubuwan da ke damunka kawai ba. Wata mai suna Chantelle ta ce: “Idan kullum kana cikin rokon Jehobah ya taimake ka kawai, abotarku ba za ta yi karfi ba. A ganina, ya kamata in fara addu’ata da godiya, kuma ya kamata in yi godiya domin abubuwa da yawa da Allah ya yi min.”

 Ka yi tunani a kan wannan: Wadanne abubuwa ne kake ganin ya kamata ka yi godiya saboda su? Za ka iya lissafta abubuwa uku da Jehobah ya yi maka da ya kamata ka gode masa?

 Wata mai suna Anita ta ce: “Ko da mutum ya ga wani karamin abu ne mai ban sha’awa kamar fure, ya kamata ya yi wa Jehobah godiya.”

 Wani mai suna Brian ya ce: “Ka yi tunani mai zurfi a kan wani halittar Allah da ya burge ka ko wata ayar Littafi Mai Tsarki da ta taba zuciyarka, kuma ka gode wa Jehobah don wadannan tanadodin.”