Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Shin, Ba Na So In Gan An Yi Kuskure Ne?

Shin, Ba Na So In Gan An Yi Kuskure Ne?

 Idan kana

  •   ganin ya kamata ka ci dari bisa dari a kowace jarrabawa

  •   guje wa yin abin da ba ka taba yi ba don kana ganin za ka yi kuskure

  •   ganin duk wata gyarar da aka yi maka bata sunanka ne

 . . .  to, amsar tambayar da ke sama e ce. Amma hakan laifi ne?

 Me ya sa wannan halin bai da kyau?

 Ba laifi ba ne mutum ya yi iya kokarinsa a duk abin da yake yi. Amma littafin nan, Perfectionism​—What’s Bad About Being Too Good? ya ce: “Akwai bambanci tsakanin mutum ya yi iya kokarinsa don ya kware a yin wani abu da kuma kokarin yin abin da babu kuskure ko kadan.” Littafin ya dada da cewa: “Irin wannan halin yana iya zama ma mutum kamar kaya mai nauyi, domin gaskiyar ita ce, dukanmu ajizai ne.”

 Littafi Mai Tsarki ya tabbatar da hakan, domin ya ce: “Babu wani mai adalci ko ɗaya cikin duniya, wanda yana aikata nagarta [‘a kowane lokaci,’ NW].” (Mai-Wa’azi 7:20) Mu ajizai ne shi ya sa a wani lokaci ba za mu iya samun dari bisa dari ba.

 Yana maka wuya ka amince da hakan? Idan haka ne, ka yi la’akari da hanyoyi hudu da wannan halin zai iya bata rayuwarka.

  1.   Yadda kake ganin kanka. Mutane masu irin wannan halin suna yawan kafa wa kansu ka’idodi da suka fi karfinsu kuma hakan zai iya sa su bakin ciki. Wata mai suna Alicia ta ce: “A gaskiya, zai yi wuya a ce mutum ba ya kuskure, kuma idan kana yawan fushi da kanka don ka yi kuskure, karshenta ba za ka sami gaba gadin yin wani abu ba. Hakan zai iya sa ka bakin ciki sosai.”

  2.   A yadda kake karban shawara. Mutum mai irin wannan halin yana ganin a duk lokacin da aka yi masa gyara, ana bata sunansa ne. Wani matashi mai suna Jeremy ya ce: “Duk lokacin da aka min gyara, ji nake kamar in mutu.” Ya dada da cewa: “Idan kana ganin sai ka yi kome daidai a kowane lokaci, ba za ka yarda cewa kana da kasawa ba balle ka karbi gyara.”

  3.   Yadda kake ganin mutane. Mutum mai nacewa sai kome ya yi daidai zai rika kushe mutane, kuma hakan ba abin mamaki ba ne. Wata ‘yar shekara 18 mai suna Anna ta ce: “Idan kana ganin bai kamata ka yi kuskure ba, to, za ka so kowa ma ya zama haka. Kuma idan mutane suka kasa yin abin da kake so, za ka rika bata rai da su.”

  4.   Yadda mutane za su dauke ka. Idan kana yawan son mutane su yi abin da ya fi karfinsu, mutane za su guje ka! Wata mai suna Beth ta ce: “Idan kana kokari ka burge mutumin da yake ganin ba ya kuskure, za ka gaji ne kawai.” Ta dada da cewa “babu wanda zai so ya yi abota da irin mutumin nan!”

 Shin, akwai mafita?

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku nuna sanin yakamata a kowane lokaci.” (Filibiyawa 4:​5, NW) Mutum mai sanin yakamata ba zai sa rai cewa shi ko wasu za su yi abin da ya fi karfinsu ba.

 Wata mai suna Nyla ta ce: “Muna fama da matsaloli da dama a duniyar nan. Don me za ka kara wa kanka matsala ta wurin kasancewa da irin wannan halin? Ai za ka wahalar da kanka ne kawai!”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi tafiya da [‘filako,’ NW] tare da Allahnka.” (Mikah 6:8) Masu filako sun san cewa akwai wasu abubuwan da ba za su iya yi ba. Ba sa yin abin da ya fi karfinsu; kuma ba sa bata lokaci a kan aiki fiye da yadda ya kamata.

 Wata mai suna Hailey ta ce: “Idan ina so in yi ayyukana da kyau, wajibi ne in karbi abin da ba zai fi karfina ba. Ba kome ne zan iya yi ba.”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan abin da hannunka ya iske na yi, ka yi shi da karfinka.” (Mai-Wa’azi 9:10) Saboda haka, ba kyuya ba ne zai sa ka daina wannan halin. Abin da zai taimaka shi ne yin aiki da kwazo da kuma kasancewa da sanin yakamata da filako.

 Wani mai suna Joshua ya ce: “Ina yin iya kokarina in yi aiki da kwazo da kuma dukan zuciyata. Na san cewa zan iya yin kuskure, amma ina farin cikin sanin cewa na yi iya karfina.”