Ayuba Ya Riƙe Amincinsa
Sashe 6
Ayuba Ya Riƙe Amincinsa
Shaiɗan ya ƙalubalanci amincin Ayuba a gaban Allah, amma Ayuba ya riƙe amincinsa ga Jehobah
AKWAI ɗan adam da zai iya riƙe amincinsa ga Allah idan aka jarraba shi sosai kuma idan yin biyayya ta zama kamar ba za ta kawo amfani na dukiya ba? An yi wannan tambayar kuma an ba da amsarta a wani batu da ya shafi wani mutumi mai suna Ayuba.
Sa’ad da Isra’ilawa suke ƙasar Masar, Ayuba, ɗan’uwan Ibrahim, yana zaune a ƙasar Arabiya ta yanzu. A wannan lokacin, mala’iku a sama sun taru a gaban Allah, kuma Shaiɗan ɗan tawaye yana cikinsu. A gaban dukan taro na samaniya, Jehobah ya furta gaba gaɗin da yake da shi a Ayuba, bawansa mai aminci. Hakika, Jehobah ya ce babu wani mutumin da ke da aminci irin ta Ayuba. Shaiɗan ya yi da’awar cewa Ayuba yana bauta wa Allah ne kawai domin Allah ya albarkace shi kuma ya kāre shi. Shaiɗan ya yi da’awar cewa idan Ayuba ya rasa dukan abubuwan da yake da shi, zai zagi Allah.
Allah ya ƙyale Shaiɗan ya ƙwace dukiyar Ayuba, ya kashe yaransa ya kuma cire lafiyar jikinsa. Domin bai san cewa Shaiɗan ne ya jawo dukan waɗannan abubuwan ba, Ayuba bai fahimci dalilin da ya sa Allah ya ƙyale shi ya fuskanci waɗannan wahalolin ba. Duk da haka, Ayuba bai juya wa Allah baya ba.
Abokan ƙarya guda uku suka zo wurin Ayuba. Cikin jerin furci da ya cika shafuffuka masu yawa na littafin Ayuba, waɗannan mazan sun yi ƙarya don su rinjayi Ayuba ya yarda cewa Allah yana yi masa horo ne domin wasu zunubai da ya yi a ɓoye. Sun yi da’awar cewa Allah ba ya farin ciki da bayinsa kuma ba ya amincewa da su. Ayuba ya yi watsi da wannan mugun ra’ayin da suke shi. Da gaba gaɗi, Ayuba ya faɗi cewa zai riƙe amincinsa har ya mutu!
Amma Ayuba ya yi kuskuren damuwa sosai da nuna cewa bai da laifi. Wani matashi mai suna Elihu, wanda ya saurari dukan tattaunawar da suka yi, ya yi magana don ya daidaita tunanin Ayuba. Elihu ya tsauta wa Ayuba domin ya ƙi nuna cewa kunita ikon mallakar Jehobah Allah ya fi muhimmanci sosai da na kowane ɗan adam. Elihu ya tsauta wa abokan ƙarya na Ayuba sosai.
Bayan haka, Jehobah ya yi magana da Ayuba, yana daidaita tunaninsa. Ta wajen yin nuni ga halittu da yawa masu ban al’ajabi, Jehobah ya koya wa Ayuba darasi a kan ƙanƙancin mutum idan aka kwatanta shi da girman Allah. Da tawali’u, Ayuba ya karɓi gyaran da Allah ya yi masa. Da yake Jehobah yana “cike da tausayi, mai-jinƙai ne kuma,” ya mai da wa Ayuba lafiyar jikinsa, ya riɓa arzikinsa sau biyu, kuma ya albarkace shi da yara goma. (Yaƙub 5:11) Ta wajen riƙe amincinsa ga Jehobah sa’ad da ya fuskanci jarraba mai tsanani, Ayuba ya yi nasara wajen amsa zargin ƙarya da Shaiɗan ya yi cewa mutane ba za su riƙe amincinsu ga Allah ba idan aka jarraba su.
—An ɗauko daga littafin Ayuba.
◼ Wane ƙalubale ne Shaiɗan ya yI GAME DA AYUBA?
◼ MENENE AKA CIM MA SA’AD DA AYUBA YA RIƘE AMINCINSA GA JEHOBAH?
[Akwati a shafi na 9]
BATUTUWA MASU MUHIMMANCI
Ta wajen furta cewa Ayuba, wanda shi ne ya fi jin tsoron Allah kuma ba shi da aibi a duniya a lokacin, yana bauta wa Jehobah Allah ne kawai domin abubuwan da zai samu, Shaiɗan yana nufin cewa dukan mutane da mala’iku suna bauta wa Allah ne domin wannan manufar. Da haka, Shaiɗan ya ƙalubalanci amincin mutum ga Jehobah. Wannan sashe ne na abin da Shaiɗan ya faɗa a Adnin, wato, iko da amincin ikon mallakar Jehobah. Littafin Ayuba ya nuna cewa mala’iku da mutane za su iya su ba da ta su gudummawar wajen kunita ikon mallakar Jehobah ta wajen riƙe amincinsu ga Jehobah.
[Taswira a shafi na 9]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba ●
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
kariya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus
2 Timotawus
Titus
Filimon
Ibraniyawa
Yaƙub
1 Bitrus
2 Bitrus
1 Yohanna
2 Yohanna
3 Yohanna
Wasiƙa ta Yahuda
Ru’ya ta Yohanna

