Allah Ya Yi Magana ta Hanyar Annabawansa

Allah Ya Yi Magana ta Hanyar Annabawansa

Sashe 14

Allah Ya Yi Magana ta Hanyar Annabawansa

Jehobah ne ke naɗa annabawa don su isar da saƙonsa game da hukunci, bauta ta gaskiya, da begen bayyanuwar Almasihu

AZAMANIN sarakunan Isra’ila da Yahuda, an yi wasu rukunin maza na musamman, wato, annabawa. Waɗannan maza ne masu bangaskiya sosai da gaba gaɗi kuma sun sanar da abubuwan da Allah ya ce. Yi la’akari da jigo guda huɗu masu muhimmanci da waɗannan annabawan suka tattauna.

1. Halakar Urushalima. Tun da daɗewa, annabawan Allah, musamman Ishaya da Irmiya, sun soma yin gargaɗi cewa za a halaka Urushalima kuma za ta zama kango. Sun bayyana dalla-dalla dalilin da ya sa Allah yake fushi da wannan birnin. Ayyukan addinan ƙarya, cin hanci, da mugunta da take yi sun ƙaryata da’awar da take yi na wakiltar Jehobah.—2 Sarakuna 21:10-15; Ishaya 3:1-8, 16-26; Irmiya 2:1–3:13.

2. Mai da bautar gaskiya. Bayan sun yi shekaru 70 a zaman bauta, za a ’yantar da mutanen Allah daga Babila. Za su koma ƙasarsu da ta zama kango kuma su sake gina haikalin Jehobah da ke Urushalima. (Irmiya 46:27; Amos 9:13-15) Wajen shekaru ɗari biyu kafin aukuwar, Ishaya ya annabta sunan wanda zai kame ƙasar, wato, Sairus, wanda zai kame ƙasar Babila kuma ya ƙyale mutanen Allah su mai do bautar gaskiya. Ishaya ya ambata dalla-dalla dabarun yaƙin da Sairus zai yi amfani da su.—Ishaya 44:24–45:3.

3. Bayyanuwar Almasihu da abubuwan da zai shaida. Za a haifi Almasihu a garin Bai’talami. (Mikah 5:2) Zai kasance mai tawali’u, zai gabatar da kansa a Urushalima, haye a kan jaki. (Zakariya 9:9) Ko da yake mutumi ne mai sauƙin kai kuma mai kirki, ba zai yi suna ba, kuma mutane da yawa za su ƙi shi. (Ishaya 42:1-3; 53:1, 3) Za a yi masa mugun kisa. Hakan zai kasance ƙarshen rayuwarsa ne? A’a, domin hadayarsa za ta sa mutane da yawa su sami gafarar zunubansu. (Ishaya 53:4, 5, 9-12) Tashinsa daga matattu ne kawai zai iya cim ma hakan.

4. Sarautar Almasihu a kan duniya. Mutane ajizai ba za su iya mulka kansu ba cikin salama, amma za a kira Sarki Almasihu, Sarkin Salama. (Ishaya 9:6, 7; Irmiya 10:23) A ƙarƙashin sarautarsa, salama za ta kasance tsakanin dukan mutane har da dukan dabbobi. (Ishaya 11:3-7) Za a daina rashin lafiya. (Ishaya 33:24) Za a haɗiye mutuwa har abada. (Ishaya 25:8) A lokacin sarautar Almasihu, za a ta da mutanen da suka mutu don su rayu a duniya.—Daniyel 12:13.

An ɗauko daga littattafan Ishaya, Irmiya, Daniyel, Amos, Mikah, da Zakariya.

◼ Waɗanne irin saƙonni ne annabawan Allah suka sanar?

◼ Ta yaya ne annabawa suka annabta halakar Urushalima da kuma sake gina ta?

◼ Menene annabawan Jehobah suka ce game da Almasihu da kuma abubuwan da zai shaida?

◼ Yaya ne annabawan suka kwatanta sarautar Almasihu a kan duniya?

[Taswira a shafi na 17]

Farawa

Fitowa

Levitikus

Littafin Lissafi

Kubawar Shari’a

Joshua

Alƙalawa

Ruth

1 Sama’ila

2 Sama’ila

1 Sarakuna

2 Sarakuna

1 Labarbaru

2 Labarbaru

Ezra

Nehemiya

Esther

Ayuba

Zabura

Misalai

Mai-Wa’azi

Waƙar Waƙoƙi

Ishaya ●

Irmiya ●

Makoki ●

Ezekiel ●

Daniyel ●

Hosiya ●

Joel ●

Amos ●

Obadiya ●

Yunana ●

Mikah ●

Nahum ●

Habakkuk ●

Zafaniya ●

Haggai ●

Zakariya ●

Malakai ●

Matta

Markus

Luka

Yohanna

Ayyukan Manzanni

Romawa

1 Korintiyawa

2 Korintiyawa

Galatiyawa

Afisawa

Filibiyawa

Kolosiyawa

1 Tasalonikawa

2 Tasalonikawa

1 Timotawus

2 Timotawus

Titus

Filimon

Ibraniyawa

Yaƙub

1 Bitrus

2 Bitrus

1 Yohanna

2 Yohanna

3 Yohanna

Wasiƙa ta Yahuda

Ru’ya ta Yohanna