Isra’ilawa Sun Ce a Naɗa Musu Sarki
Sashe 9
Isra’ilawa Sun Ce a Naɗa Musu Sarki
Saul, wanda shi ne sarki na farko a Isra’ila, ya yi rashin biyayya. Dauda, wanda Allah ya yi wa alkawarin mulki na har abada ne ya gaje shi
BAYAN zamanin Samson, Sama’ila ya yi hidima a matsayin annabi da alƙali a Isra’ila. Isra’ilawa sun ci gaba da gaya masa cewa suna son su zama kamar sauran al’ummai kuma suna son sarki ɗan Adam ya yi sarauta a kansu. Ko da yake wannan roƙon da suka yi ya ɓata wa Jehobah rai, ya umurci Sama’ila ya yi hakan. Allah ya zaɓi mutumi mai tawali’u mai suna Saul ya zama sarki. Bayan wani ɗan lokaci, Sarki Saul ya zama mai girman kai da marar biyayya. Jehobah ya ƙi shi a matsayin sarki kuma ya gaya wa Sama’ila ya je ya naɗa wani matashi mai suna Dauda. Amma an yi shekaru kafin Dauda ya soma sarauta a matsayin sarki.
Wataƙila sa’ad da yake matashi, Dauda ya ziyarci ’yan’uwansa waɗanda sojojin Saul ne. Duka sojojin suna jin tsoron wani barde maƙiyi, gwarzon mutumi mai suna Goliyat, wanda ya ci gaba da zaginsu da kuma Allahnsu. Domin abin ya ba shi haushi, Dauda ya amince ya yi yaƙi da wannan gwarzon mutumi. Riƙe da majajjawa da ’yan duwatsu, wannan saurayin ya je ya fuskanci abokin faɗansa, wanda ya fi shi tsawo da fiye da kafa tara. Sa’ad da Goliyat ya yi masa ba’a, Dauda ya gaya masa cewa makaminsa ya fi na gwarzon, domin Dauda ya yi faɗan ne da sunan Jehobah Allah! Dauda ya kashe Goliyat da dutse ɗaya tak kuma ya cire kansa da takobin gwarzon. Sojojin Filistiya suka gudu cikin tsoro.
Da farko, gaba gaɗin da Dauda ya nuna ya burge Saul kuma ya ba saurayin shugabancin sojojinsa. Amma nasarorin da Dauda ya samu sun sa Saul ya soma mugun kishi. Dauda ya gudu domin kada a kashe shi kuma ya yi shekaru yana gudun hijira. Duk da haka, Dauda ya kasance da aminci ga sarkin da yake son ya kashe shi, domin ya san cewa Jehobah Allah ne ya naɗa Sarki Saul. A ƙarshe, Saul ya mutu a bakin daga. Ba da daɗewa ba, Dauda ya zama sarki, kamar yadda Jehobah ya yi alkawari.
A matsayin sarki, Dauda yana da muradin gina haikali ga Jehobah. Amma, Jehobah ya gaya wa Dauda cewa wani daga cikin zuriyarsa ne zai yi hakan. Sulemanu ɗanɗan Dauda ne ya yi ginin. Allah ya saka wa Dauda ta wajen yin alkawari mai ban al’ajabi da shi: Zuriyarsa za ta yi sarakuna fiye da sauran. Mafi girma, ta nan ne za a haifi Mai Ceto, ko Zuriya, wanda aka yi alkawarinsa a Adnin. Shi ne zai zama Almasihu, wato, “Shafaffe,” da Allah ya naɗa. Jehobah ya alkawari cewa Almasihu zai zama Sarkin wata gwamnati, ko Mulki, wadda za ta kasance har abada.
Domin ya nuna godiyarsa, Dauda ya tara kayan gini masu yawa da kuma ƙarafa masu tamani don gina haikalin. Ya kuma rubuta hurarrun zabura masu yawa. Kusan ƙarshen rayuwarsa, Dauda ya ce: “Ruhun Ubangiji ya yi zance da ni, maganatasa kuma tana bisa harshena.”—2 Sama’ila 23:2.
—An ɗauko daga littafin Sama’ila na 1 da na 2; 1 Labarbaru; Ishaya 9:7; Matta 21:9; Luka 1:32; Yohanna 7:42.
◼ Me ya sa Jehobah ya sauya Sarki Saul da Dauda?
◼ Waɗanne halaye ne Dauda ya nuna kafin ma ya zama sarki?
◼ Wanene Zuriya, ko Mai Ceto da aka yi alkawarinsa, wanda aka annabta cewa zai fito ne daga zuriyar Dauda?
[Bayanin da ke shafi na 12]
“Zan tabbatadda kursiyin mulkinsa har abada.”—2 Sama’ila 7:13
[Taswira a shafi na 12]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
● 1 Sama’ila
● 2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
● 1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus
2 Timotawus
Titus
Filimon
Ibraniyawa
Yaƙub
1 Bitrus
2 Bitrus
1 Yohanna
2 Yohanna
3 Yohanna
Wasiƙa ta Yahuda
Ru’ya ta Yohanna

