Mahalicci Ya Saka Mutum a Cikin Aljanna

Mahalicci Ya Saka Mutum a Cikin Aljanna

Sashe 1

Mahalicci Ya Saka Mutum a Cikin Aljanna

Allah ya halicci sararin samaniya da muke gani da kuma rai a duniya; ya halicci mace da namiji kamiltattu, ya saka su a cikin lambu mai kyau, kuma ya ba su dokokin da za su bi

AN CE kalaman da ke gaba su ne kalaman da aka fi sani cikin kalaman farko da aka taɓa rubutawa. “A cikin farko Allah ya halitta sama da ƙasa.” (Farawa 1:1) Da wannan jimlar mai sauƙi amma mai muhimmancin gaske ce Littafi Mai Tsarki ya gabatar da mu ga Wanda shi ne ya fi muhimmanci a cikin Nassosi Masu Tsarki, wato, Allah mafi girma, Jehobah. Aya ta farko a cikin Littafi Mai Tsarki ta bayyana cewa Allah ne Mahaliccin dukan sararin samaniya har da duniyar da muke cikinta. Ayoyin da suka biyo bayanta sun bayyana cewa a cikin dogon lokaci, waɗanda aka kira ranaku a alamance, Allah ya tsara duniya don mu rayu a cikinta, kuma ya halicci dukan abubuwa masu ban al’ajabi da ke duniyarmu.

Mutum ne ya fi girma a cikin dukan halittun Allah a duniya. Shi ne halittar da aka yi cikin surar Allah, yana iya nuna halayen Jehobah, kamar ƙaunarsa da hikima. Allah ya halicci mutum daga cikin ƙasar da ke duniya. Allah ya kira shi Adamu, kuma ya saka shi cikin aljanna, wato, lambun da ke Adnin. Allah ne da kansa ya shuka lambun, kuma ya cika shi da kyawawan itatuwa masu ba da ’ya’ya.

Allah ya ga cewa namijin yana bukatan abokiyar zama. Ta wajen yin amfani da ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa, Allah ya halicci macen kuma ya kai ta ga Adamu a matsayin matarsa, wadda aka kira Hauwa’u. Domin farin ciki, sai Adamu ya ce: “Wannan yanzu ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne daga namana.” Allah ya ce: “Domin wannan mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa, ya manne ma matatasa: za su zama nama ɗaya kuma.”—Farawa 2:22-24; 3:20.

Allah ya ba Adamu da Hauwa’u dokoki biyu. Na farko, ya umurce su su nome kuma su kula da duniya, kuma daga baya su cika ta da yaransu. Na biyu, ya gaya musu kada su ci ’ya’yan itace guda a cikin lambun mai girma, “itace na sanin nagarta da mugunta.” (Farawa 2:17) Idan suka yi rashin biyayya, za su mutu. Da waɗannan dokokin, Allah ya ba mace da namijin daman nuna cewa sun karɓe shi a matsayin Sarkinsu. Biyayyarsu za ta nuna ƙaunarsu da godiyarsu. Suna da dukan dalilin amincewa da sarautarsa mai kyau. Babu wata alamar ajizanci a jikin waɗannan kamiltattun mutanen. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Allah kuma ya duba kowane abin da ya yi, ga shi kuwa, yana da kyau ƙwarai.”—Farawa 1:31.

—An ɗauko daga Farawa surori na 1 da na 2.

◼ Yaya ne Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yadda aka halicci mutane da kuma duniya?

◼ Wace irin rayuwa ce Allah ya tanadar wa namiji da macen?

◼ Waɗanne dokoki ne Allah ya ba mutane biyu na farko?

[Akwati a shafi na 4]

SUNAN ALLAH

Nassosi Masu Tsarki sun kira Allah da laƙabi dabam-dabam, kamar Mahalicci da Allah Maɗaukaki. Wasu cikin waɗannan laƙabin sun nanata halayen Allah, kamar tsarkinsa, ikonsa, adalcinsa, hikimarsa, da ƙaunarsa. Ban da haka, Allah ya ba kansa sunan da babu irin sa, wato, Jehobah. Kamar yadda aka rubuta a cikin harsuna na asali, wannan sunan ya bayyana sau 7,000 a cikin Littafi Mai Tsarki, na farko a cikin Farawa 2:4. Sunan nan Jehobah yana nufin “Yana Sa Ya Zama.” Sanin hakan yana da ban ƙarfafa, domin hakan na nufin cewa Allah yana iya cim ma duk wata manufa da yake da ita kuma ya cika duk wani alkawarin da ya yi.

[Taswira a shafi na 4]

Farawa

Fitowa

Levitikus

Littafin Lissafi

Kubawar Shari’a

Joshua

Alƙalawa

Ruth

1 Sama’ila

2 Sama’ila

1 Sarakuna

2 Sarakuna

1 Labarbaru

2 Labarbaru

Ezra

Nehemiya

Esther

Ayuba

Zabura

Misalai

Mai-Wa’azi

Waƙar Waƙoƙi

Ishaya

Irmiya

Makoki

Ezekiel

Daniyel

Hosiya

Joel

Amos

Obadiya

Yunana

Mikah

Nahum

Habakkuk

Zafaniya

Haggai

Zakariya

Malakai

Matta

Markus

Luka

Yohanna

Ayyukan Manzanni

Romawa

1 Korintiyawa

2 Korintiyawa

Galatiyawa

Afisawa

Filibiyawa

Kolosiyawa

1 Tasalonikawa

2 Tasalonikawa

1 Timotawus

2 Timotawus

Titus

Filimon

Ibraniyawa

Yaƙub

1 Bitrus

2 Bitrus

1 Yohanna

2 Yohanna

3 Yohanna

Wasiƙa ta Yahuda

Ru’ya ta Yohanna