An Kashe Yesu Kristi
Sashe 20
An Kashe Yesu Kristi
Yesu ya kafa sabon abin da za mu kiyaye; an ci amanarsa kuma an tsire shi a kan gungume
BAYAN shekaru uku da rabi na yin wa’azi da koyarwa, Yesu ya san cewa lokacinsa a duniya ya zo ƙarshe. Shugabannin addinin Yahudawa suna ƙulle-ƙulle don su kashe shi, amma suna tsoron hargitsi daga mutanen da suka ɗauke shi a matsayin annabi. A lokacin, Shaiɗan ya rinjayi Yahuda Iskariyoti, ɗaya daga cikin manzanni Yesu guda 12, don ya zama maci amana. Shugabannin addinai sun ba Yahuda tsabar kuɗin azurfa 30 don ya ci amanar Yesu.
A darensa na ƙarshe, Yesu ya tara manzanninsa don su kiyaye Idin Ƙetarewa. Bayan ya sallami Yahuda, ya kafa sabon abin da za su riƙa kiyayewa, wato, Jibin Maraice na Ubangiji. Ya ɗauki gurasa, ya yi addu’a, kuma ya miƙa gurasan ga manzanni 11 da suka rage. “Wannan jikina ne wanda aka bayar domin ku,” in ji shi. “Ku yi wannan abin tunawa da ni.” Ya yi hakan kuma da ƙoƙon inabi, yana cewa, “Wannan ƙoƙo sabon alkawali ne, cikin jinina.”—Luka 22:19, 20.
Yesu yana da abubuwa da yawa da zai tattauna da manzanninsa a wannan daren. Ya ba su sabuwar doka, wato, su ƙaunaci juna babu son kai. Ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:34, 35) Ya aririce su kada su ƙyale zukatansu ta damu domin mugayen abubuwan da suke gab da aukuwa. Yesu ya yi addu’a sosai a madadinsu. Sun yi waƙoƙin yabo tare kuma suka fita tare a daren.
A lambun Jathsaimani, Yesu ya durƙusa kuma ya yi addu’a sosai ga Allah. Ba da daɗewa ba, rundunar sojoji riƙe da makamai, firistoci, da wasu suka iso don su kama shi. Yahuda ya isa wurin kuma ya nuna musu Yesu ta wajen yi masa sumba. Yayin da sojojin suka kama Yesu, sai manzannin suka gudu.
Sa’ad da yake tsaye a gaban babban kotun Yahudawa, Yesu ya bayyana kansa a matsayin Ɗan Allah. Kotun ya ce ya same shi da laifin yin saɓo kuma ya cancanci ya mutu. Sai aka kai Yesu wajen Gwamna Ɗan Roma Bilatus Ba-Bunti. Ko da yake bai sami Yesu da wani laifi ba, ya miƙa Yesu ga gungun mutanen da suke son su kashe shi.
An kai Yesu Golgota, inda sojojin Roma suka tsire shi a kan gungume. Ta hanyar mu’ujiza, rana tsaka ta koma duhu. Can da rana, Yesu ya mutu, kuma aka yi muguwar girgizar ƙasa. An kwantar da gawarsa a cikin kabarin da aka yi a cikin dutse. Washegari, firistoci suka rufe bakin kabarin kuma suka sa masu gadi. Yesu zai ci gaba da kasancewa ne a cikin kabarin? A’a. Mu’ujiza mafi girma tana gab da faruwa.
—An ɗauko ne daga Matta surori 26 da 27; Markus surori 14 da 15; Luka surori 22 da 23; Yohanna surori 12 zuwa 19.
◼ Wane sabon abin tunawa ne Yesu ya kafa?
◼ Waɗanne abubuwa ne suka kai ga mutuwar Yesu?
[Akwati a shafi na 23]
MATSAYIN YESU NA MUSAMMAN
Mutuwar Yesu ta cika matsayi na musamman wajen cika nufin Jehobah. Domin an yi cikin Yesu ta hanyar ruhu mai tsarki na Allah, an haife shi kamiltacce, kuma ba ya bukatan ya mutu. Duk da haka, ya ba da ransa domin mutane su sami damar yin rayuwa har abada kuma su more irin rayuwar da Adamu marar biyayya ya sa ’ya’yansa suka rasa. a—Matta 20:28; Luka 1:34, 35; Yohanna 3:16, 36; 2 Bitrus 3:13.
[Hasiya]
a Don tattauna tamanin mutuwar hadayar da Yesu ya yi, ka duba shafuffuka na 47-56 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
[Taswira a shafi na 23]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta ●
Markus ●
Luka ●
Yohanna ●
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa

