Duniya Ta Zama Aljanna!
Sashe 26
Duniya Ta Zama Aljanna!
Ta hanyar Mulki a ƙarƙashin Kristi, Jehobah Ya tsarkake sunansa, ya kunita ikon mallakarsa, kuma ya kawar da dukan mugunta
LITTAFI na ƙarshe a cikin Littafi Mai Tsarki, mai suna Ru’ya ko Wahayi, ya yi tanadin bege ga dukan mutane. Manzo Yohanna ne ya rubuta shi, littafin yana ɗauke da wahayi da suka kammala a cikar nufin Jehobah.
A wahayi na farko, Yesu da aka ta da daga matattu ya yabi da kuma daidaita ikilisiyoyi. Wahayi na gaba ya nuna mana kursiyin Allah a sama, inda halittun ruhohi suke yabonsa.
Yayin da nufin Allah ya ci gaba, Ɗan Tunkiyar, Yesu Kristi, ya karɓi naɗaɗɗen littafi da hatimi guda bakwai. Sa’ad da aka buɗe hatimi na ɗaya zuwa na huɗu, sai mahaya dawaki na alama suka shiga duniya. Na farko shi ne Yesu a kan farin doki kuma an ɗora masa kambi a matsayin Sarki. Bayan sa sai wasu mahayan suka fito a kan dawakai dabam-dabam, a annabce suna wakiltar yaƙi, yunwa, da cuta, kuma suna faruwa ne a kwanaki na ƙarshe na wannan zamanin. Hatimi na bakwai da aka buɗe ya kai ga busa ƙaho guda bakwai na alama, wanda ke nufin sanar da hukunce-hukuncen da Allah zai yi. Hakan ya kai ga annoba guda bakwai na alama, ko kuwa fushin Allah.
An kafa Mulkin Allah a sama, wanda jariri ke wakilta. Yaƙi ya ɓarke, kuma an jefo Shaiɗan da mugayen mala’ikunsa zuwa duniya. “Kaiton duniya,” in ji wata babbar murya. Iblis yana fushi sosai, domin ya san cewa lokacinsa ya ƙure.—Ru’ya ta Yohanna 12:12.
Yohanna ya ga Yesu a sama wanda ɗan tunkiya yake wakilta, kuma akwai mutane 144,000 tare da shi waɗanda aka zaɓa daga ’yan Adam. Su ne za su “yi mulki kuma tare” da Yesu. Ru’ya ta Yohanna ta bayyana cewa sashe na biyu na wannan zuriya su ne mutane 144,000.—Ru’ya ta Yohanna 14:1; 20:6.
Masu sarauta a duniya sun taru a Armageddon, “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka.” Sun yi yaƙi da wanda ke zaune a kan farin doki, wato, Yesu, wanda shi ne ya ja-goranci sojoji na samaniya. An halaka dukan sarakunan duniyar nan. An ɗaure Shaiɗan, kuma Yesu da mutane 144,000 za su yi sarauta bisa duniya har “shekara dubu.” A ƙarshen sarauta ta shekara dubu, an halaka Shaiɗan.—Ru’ya ta Yohanna 16:14; 20:4.
Wane amfani ne mutane masu biyayya za su samu daga Sarauta ta Shekara Dubu ta Kristi da abokan sarautarsa? Yohanna ya rubuta: “[Jehobah] zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Duniya ta zama aljanna!
Da hakan, littafin Ru’ya ta Yohanna ya kammala saƙon Littafi Mai Tsarki. Ta hanyar Mulkin Almasihu, za a tsarkake sunan Jehobah kuma a kunita ikon mallakarsa har abada!
—An ɗauko daga littafin Ru’ya ta Yohanna.
◼ Menene ma’anar mahaya dawaki na alama?
◼ Waɗanne abubuwa masu ban al’ajabi suka faru yayin da nufin Allah ya ci gaba?
◼ Menene Armageddon, kuma menene sakamakon?
[Akwati a shafi na 30]
“BABILA BABBA”
A cikin littafin Ru’ta ta Yohanna, dukan addinan ƙarya, wato, addinan da ke hamayya da Allah na gaskiya, gabaki ɗaya ana kiran su ne “babbar karuwa.” An kira ta “Babila Babba,” kuma tana sayar da, ko yin karuwanci da manyan ’yan siyasa na duniya. A lokacin da Jehobah Allah ya ƙayyade, in ji Ru’ya ta Yohanna, waɗannan sarakuna za su kai wa wannan karuwar hari kuma su halaka ta.—Ru’ya ta Yohanna 17:1-5, 16, 17.
[Taswira a shafi na 30]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus
2 Timotawus
Titus
Filimon
Ibraniyawa
Yaƙub
1 Bitrus
2 Bitrus
1 Yohanna
2 Yohanna
3 Yohanna
Wasiƙa ta Yahuda
● Ru’ya ta Yohanna

