Sulemanu Sarki Ne Mai Hikima
Sashe 10
Sulemanu Sarki Ne Mai Hikima
Jehobah ya ba Sarki Sulemanu zuciya mai hikima; a lokacin sarautar Sulemanu, Isra’ilawa sun shaida salama da kuma arziki marar iyaka
YAYA rayuwa za ta kasance idan al’umma gabaki ɗaya da kuma sarkinta suka bi Jehobah a matsayin Mamallakinsu kuma suka yi biyayya ga dokokinsa? An kwatanta amsar a lokacin sarauta ta shekara 40 na Sarki Sulemanu.
Kafin Dauda ya mutu, ya naɗa ɗansa Sulemanu a matsayin wanda zai gaje shi. A cikin mafarki, Allah ya gaya wa Sulemanu ya roƙi abin da yake so. Sulemanu ya roƙi hikima da fahimi don ya yi wa mutanen ja-gora yadda ya dace kuma cikin hikima. Jehobah ya yi farin ciki kuma ya ba Sulemanu zuciya mai hikima da fahimi. Kuma Jehobah ya yi masa alkawarin arziki, ɗaukaka, da tsawon rai idan iya ci gaba da yi masa biyayya.
Sulemanu ya zama sananne don hukuncinsa na hikima. Akwai lokacin da wasu mata biyu suke gardama a kan yaro jariri, kowannensu na da’awar cewa ita ce uwar. Sulemanu ya ba da umurni cewa a raba jaririn biyu kuma a ba kowace mata rabi. Mace ta farko ta yarda, amma nan da nan ainihin uwar ta yi roƙo cewa a ba da jaririn ga ɗayan matar. A nan Sulemanu ya gane cewa matar nan mai tausayi ita ce uwar kuma ya ba ta jaririnta. Nan da nan dukan Isra’ila ta ji wannan hukuncin da ya yanke, kuma dukan mutanen suka gane cewa hikimar Allah tana tare da Sulemanu.
Ɗaya daga cikin abubuwa mafi girma da Sulemanu ya cim ma shi ne gina haikalin Jehobah, gini ne mai girma a Urushalima da zai kasance cibiyar bauta a Isra’ila. Sa’ad da ake keɓe haikalin, Sulemanu ya yi addu’a: “Ga shi, sammai da samman sammai ba su da iko su karɓe ka: balle fa wannan gida da na gina!”—1 Sarakuna 8:27.
Sunan Sulemanu ya yaɗu zuwa ƙasashe, har ƙasar Sheba da ke Arabiya. Sarauniyar Sheba ta yi tafiya don ta ga ɗaukakar Sulemanu da arzikinsa kuma ta gwada zurfin hikimarsa. Hikimar Sulemanu da arzikin ƙasar Isra’ila sun burge sarauniyar har ta yaba wa Jehobah da ya naɗa irin wannan sarki mai hikima. Hakika, domin albarkar Jehobah, sarautar Sulemanu ta kasancewa mafi ɗaukaka tare da salama a tarihin Isra’ila ta dā.
Abin baƙin ciki, Sulemanu ya daina yin abubuwan da suka jitu da hikimar Jehobah. Ta wajen yin watsi da dokar Allah, ya auri ɗarurruwan mata, kuma yawancinsu suna bauta wa allolin ƙarya. Da sannu-sannu matansa suka rinjayi zuciyarsa daga bin Jehobah kuma ya soma bauta wa gumaka. Jehobah ya gaya wa Sulemanu cewa za a ƙwace sashen mulkinsa daga hannunsa. Sashe ɗaya ne kawai zai rage a iyalinsa, in ji Allah, domin Dauda mahaifin Sulemanu. Duk da kaucewar da Sulemanu ya yi, Jehobah ya kasance da aminci ga alkawarin Mulki da ya yi wa Dauda.
—An ɗauko daga 1 Sarakuna, surori 1 zuwa 11; 2 Labarbaru, surori 1 zuwa 9; Kubawar Shari’a 17:17.
◼ Menene Allah ya yi a kan roƙon da Sulemanu ya yi?
◼ Ta yaya ne Sulemanu ya nuna hikimarsa?
◼ Ta yaya ne Sulemanu ya kauce daga hanyoyin Jehobah, kuma menene sakamakon?
[Taswira a shafi na 13]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna ●
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru ●
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya

