Mutane Sun Tsira Daga Rigyawa
Sashe 3
Mutane Sun Tsira Daga Rigyawa
Allah ya halaka muguwar duniya amma ya ceci Nuhu da iyalinsa
YAYIN da mutane suke ci gaba da ƙaruwa, zunubi da mugunta sun yaɗu sosai a duniya. Wani annabi mai suna Anuhu, wanda wataƙila shi kaɗai ne mai wa’azi a zamaninsa, ya yi gargaɗi cewa Allah zai halaka muguwar duniyar wata rana. Duk da haka, mugunta sai ƙara daɗuwa take yi. Wasu mala’iku sun yi tawaye ga Jehobah ta wajen barin ayyukan da suke yi a sama, suka ɗauki siffar mutane, kuma cikin kwaɗayi, suka auri mata. Wannan dangantakar da ba ta dace ba ta haifar da ƙatta masu mugun ƙarfi da aka kira Nephilim, waɗanda suka ƙara zafin mugunta da zubar da jini a duniya. Allah ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da ya ga yadda aka halaka halittunsa a duniya.
Bayan mutuwar Anuhu, an sami wani mutumin da ya bambanta a wannan muguwar duniyar. Sunansa Nuhu ne. Shi da iyalinsa sun yi ƙoƙarin yin abin da ya dace a gaban Allah. Sa’ad da Allah ya yanke shawarar halaka mugayen mutanen wannan duniyar, yana son ya kāre Nuhu da dabbobin da ke duniya. Saboda haka, Allah umurce shi ya gina jirgin ruwa mai girma mai kusurwa huɗu. A cikinsa ne za a ceci Nuhu da iyalinsa a lokacin rigyawa, tare da dabbobi dabam-dabam masu yawa. Nuhu ya yi biyayya ga Allah. A wajen shekaru arba’in ko hamsin da Nuhu ya yi yana gina wannan jirgin, ya zama “mai-shelan adalci.” (2 Bitrus 2:5) Ya gargaɗi mutane game da Rigyawar da ke tafe, amma sun yi watsi da shi. Lokaci ya yi da Nuhu da iyalinsa za su shiga cikin jirgin tare da dabbobi. Sai Allah ya rufe ƙofar jirgin. Sai aka soma ruwan sama.
An yi ruwan saman ne kamar da bakin ƙwarya dare da rana har tsawon kwanaki arba’in, har sai da ruwan ya mamaye dukan duniya. An halaka miyagu. Watanni bayan hakan, yayin da ruwan ke raguwa, sai jirgin ruwan ya sauka a kan wani dutse. Mutane da dabbobin da ke cikin jirgin sun yi shekara ɗaya cir kafin su fita. Domin ya nuna godiya, Nuhu ya yi hadaya ga Jehobah. Allah ya karɓi hadayar ta wajen ba Nuhu da iyalinsa tabbaci cewa ba zai ƙara halaka dukan rai da ke duniya da ruwa ba. Jehobah ya yi tanadin bakan gizo a matsayin tabbacin da za a riƙa gani, wanda tunasarwa ce ta wannan alkawari mai ban ƙarfafa.
Bayan rigyawar, Allah ya ba mutane wasu sababbin dokoki. Ya ba su izinin cin naman dabbobi. Amma, ya hana cin jini. Ya kuma umurci zuriyar Nuhu su bazu a duniya, amma wasu sun ƙi yin biyayya. Mutane sun haɗa kai a ƙarƙashin wani shugaba mai suna Nimrod kuma suka soma gina hasumiya mai girma a cikin birnin Babel, wanda daga baya ya zama Babila. Manufarsu ita ce su ƙi yin biyayya ga dokar da Allah ya kafa game da bazuwa a duniya. Allah ya watsar da ’yan tawayen ta wajen birkice yarensu kuma ya sa suka soma yin harsuna dabam-dabam. Domin sun kasa tattaunawa da juna, sun yi watsi da aikin kuma kowa ya kama gabansa.
—An ɗauko daga Farawa surori ta 6 zuwa 11; Yahuda 14, 15.
◼ Ta yaya mugunta ta yaɗu a duniya?
◼ Ta yaya ne Nuhu ya nuna cewa shi mutumi ne mai aminci?
◼ Menene Allah ya hana mutane yi bayan Rigyawa?
[Akwati a shafi na 6]
BIN ALLAH
Yawancin zuriyar Adamu da Hauwa’u sun ƙi sarautar Jehobah. Amma akwai waɗanda ba su yi hakan ba, na farko shi ne ɗansu mai aminci, Habila. Daga baya, an ce Anuhu da Nuhu sun bi Allah, wato, sun bi tafarkin da Jehobah yake so. (Farawa 5:22; 6:9) Yawancin labaran da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun mai da hankali ne ga maza da mata da suka zaɓi Allah Ya zama Sarkinsu.
[Taswira a shafi na 6]
● Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus

