Sarakunan Kirki da Marasa Kirki

Sarakunan Kirki da Marasa Kirki

Sashe 13

Sarakunan Kirki da Marasa Kirki

An raba Isra’ila. A kai a kai, sarakuna masu yawa sun yi sarauta bisa Isra’ilawa, kuma yawancinsu ba su kasance da aminci ba. Babiloniyawa sun halaka Urushalima

KAMAR yadda Jehobah ya annabta, an raba Isra’ila bayan da Sulemanu ya yi watsi da bautar gaskiya. Ɗansa kuma magajinsa, Yerobowam, mugu ne. Saboda haka, ƙabilu goma na Isra’ila suka yi tawaye kuma suka kafa masarautar arewa ta Isra’ila. Ƙabilu biyu ne suka kasance da aminci ga sarkin da ke kan karagar mulki na Dauda a Urushalima, kuma hakan ya kafa masarautar kudu ta Yahuda.

Waɗannan masarautar biyu sun kasance da tarihi da ke cike da hargitsi, yawanci domin sarakuna marar bangaskiya da kuma marasa biyayya. Masarauta ta Isra’ila ta fi na Yahuda muni, domin sarakunanta sun ɗaukaka bautar ƙarya tun daga farko. Duk da ayyuka masu girma da annabawa kamar Elisha da Iliya suka yi, har da ta da matattu, Isra’ila ta ci gaba da nitsewa cikin tafarkin mugunta. A ƙarshe, Allah ya ƙyale Assuriyawa su halaka masarautar arewa.

Bayan halakar Isra’ila, Yahuda ta wanzu fiye da ƙarni ɗaya, amma ita ma ta fuskanci horo daga Allah. Sarakuna kaɗan daga Yahuda ne kawai suka saurari gargaɗin da annabawan Allah suka yi kuma suka yi ƙoƙarin mai da mutanen ga Jehobah. Alal misali, Sarki Yosiya ya soma tsabtace Yahuda daga bautar ƙarya kuma ya sake gyara haikalin Jehobah. Sa’ad da aka sami ainihin Dokar Allah da aka rubuta ta hanyar Musa, hakan ya motsa Yosiya sosai kuma ya daɗa ba da ƙarfi ga yin gyara.

Abin baƙin ciki, waɗanda suka gaji Yosiya ba su bi misali mai kyau na sarkin ba. Saboda haka, Jehobah ya ƙyale ƙasar Babila ta kame ƙasar Yahuda, kuma ta halaka Urushalima da haikalinta. An kai waɗanda suka tsira zuwa zaman bauta a Babila. Allah ya annabta cewa za su yi zaman bautar ne har shekaru 70. Yahuda ta kasance kango a dukan waɗannan shekarun, har sa’ad da al’ummar ta koma ƙasarta kamar yadda aka yi alkawari.

Amma, babu wasu sarakuna a zuriyar Dauda da za su sake yin sarauta har sai Mai Ceto da aka yi alkawarinsa, wato, Almasihu da aka annabta, ya soma sarauta. Yawancin sarakuna da suka zauna a kan karagar Dauda a Urushalima sun tabbatar da cewa mutane ajizai ba su cancanci yin sarauta ba. Almasihu kaɗai ne ainihi ya cancanta. Shi ya sa Jehobah ya gaya wa sarki na ƙarshe a zuriyar Dauda: “A tuɓe ƙambi . . . wannan kuma ba za ya sake zama kamar dā ba, har lokacin da wannan ya zo wanda wajibinsa ne, ni ma in ba shi.”—Ezekiyel 21:26, 27.

—An ɗauko daga Sarakuna na 1 da 2; 2 Labarbaru surori 10 zuwa 36; Irmiya 25:8-11.

◼ Ta yaya aka raba Isra’ila, kuma menene ya sami masarautun guda biyu?

◼ Menene ya sami sarakunan da suka fito daga iyalin Dauda, kuma me ya sa?

◼ Menene labarin Yunana ya koya mana game da Jehobah? (Duba akwati.)

[Akwati a shafi na 16]

YUNANA

A zamanin da aka raba masarautun, Allah ya aiki Yunana ya je ya yi wa’azin saƙon gargaɗi ga mutanen da ke mugun birnin da ke ƙasar Nineba. Maimakon hakan, Yunana ya shiga jirgin ruwa da zai je wani wajen dabam. Hakan ya kai ga mu’ujiza, Allah ya sa wani ƙaton kifi ya haɗiye Yunana. A cikin kifin, Yunana ya yi addu’a ga Jehobah, wanda ya sa kifin ya yi amansa a kan busasshiyar ƙasa. Bayan haka, Yunana ya tafi ya cika aikin da aka ba shi.

Bayan Allah ya koya wa Yunana wannan darassi na biyayya, sai matsala na biyu ta taso: Yunana ya yi wa’azi ga ’yan Nineba, amma ya yi mugun baƙin ciki domin Allah ya ji tausayinsu kuma bai yi musu horo ba domin sun tuba. Ka karanta wannan littafin mai ban sha’awa don ganin yadda Allah ya yi amfani da mu’ujiza na biyu ya koya wa Yunana ya kasance da tausayi.

[Taswira a shafi na 16]

Farawa

Fitowa

Levitikus

Littafin Lissafi

Kubawar Shari’a

Joshua

Alƙalawa

Ruth

1 Sama’ila

2 Sama’ila

● 1 Sarakuna

● 2 Sarakuna

1 Labarbaru

● 2 Labarbaru

Ezra

Nehemiya

Esther

Ayuba

Zabura

Misalai

Mai-Wa’azi

Waƙar Waƙoƙi

Ishaya

Irmiya

Makoki

Ezekiel

Daniyel

Hosiya

Joel

Amos

Obadiya

● Yunana

Mikah

Nahum

Habakkuk

Zafaniya

Haggai

Zakariya

Malakai