Yesu Ya Koya wa Mutane Game da Mulkin Allah
Sashe 17
Yesu Ya Koya wa Mutane Game da Mulkin Allah
Yesu ya koya wa almajiransa abubuwa masu yawa, duk da haka, ya mai da hankali ne a kan jigo guda, wato, Mulkin Allah
WANE aiki ne Yesu ya zo yi a duniya? Shi da kansa ya ce: “Dole in kai bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luka 4:43) Ka yi la’akari da abubuwa guda huɗu da Yesu ya koyar game da Mulkin, wanda shi ne ainihin jigon wa’azinsa.
1. Yesu zai zama Sarki. Yesu ya faɗi kai tsaye cewa shi ne Almasihun da aka annabta. (Yohanna 4:25, 26) Ya kuma nuna cewa shi ne Sarkin da annabi Daniyel ya gani a wahayi. Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa wata rana zai zauna a kan “kursiyin daraja” su kuma za su zauna a kan kursiyi. (Matta 19:28) Ya kira waɗannan rukunin sarakuna a matsayin “ƙaramin garke,” kuma ya ambata cewa yana da “waɗansu tumaki,” waɗanda ba sa cikin wannan rukunin.—Luka 12:32; Yohanna 10:16.
2. Mulkin Allah zai ɗaukaka adalci na gaskiya. Yesu ya nuna cewa Mulkin zai kawar da rashin adalci mafi girma ta wajen tsarkake sunan Jehobah Allah da kuma kawar da dukan ƙaryar da Shaiɗan ya yi a kan sunan tun tawayen da aka yi a Adnin. (Matta 6:9, 10) Yesu ya nuna rashin son kai a kullum ta wajen koyar da maza da mata, masu arziki da talakawa, babu bambanci. Ko da yake aikinsa na ainihi shi ne koyar da Isra’ilawa, ya kuma taimaka wa Samariyawa da ’yan Al’ummai, ko kuwa waɗanda ba Yahudawa ba. Akasin shugabannin addinai na zamaninsa, bai nuna alamar bambanci ko son kai ba.
3. Mulkin Allah ba zai kasance sashen duniyar nan ba. Yesu ya rayu ne a lokacin da aka yi mugun hargitsi na siyasa. Ƙasarsu tana ƙarƙashin ikon wata ƙasa. Duk da haka, sa’ad da mutane suka nemi su jawo shi cikin al’amuran siyasar zamaninsa, ya janye. (Yohanna 6:14, 15) Ya gaya wa wani ɗan siyasa: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne.” (Yohanna 18:36) Ga mabiyansa, ya ce: “Ku ba na duniya ba ne.” (Yohanna 15:19) Ba zai yarda su yi amfani da makaman yaƙi ba, ko da shi ne za su kāre.—Matta 26:51, 52.
4. Sarautar Kristi za ta kasance ne a kan ƙauna. Yesu ya yi alkawarin kawo wa mutane hutu, ta wajen rage musu nauyi. (Matta 11:28-30) Ya cika alkawarinsa. Ya ba da shawara mai kyau wadda take cike da ƙauna game da yadda za a jimre alhini, kyautata dangantaka, yaƙar neman abin duniya, da kuma samun farin ciki. (Matta, surori 5-7) Domin yana nuna ƙauna, mutane daga wurare dabam-dabam suna zuwa wurin sa. Har da tsiyayyu, sun yi jerin gwano zuwa wurinsa, domin suna da tabbaci cewa zai nuna musu alheri kuma zai daraja su. Hakika, Yesu zai kasance Sarki nagari!
Akwai wata hanya mai girma sosai wadda Yesu ya koya wa mutane game da Mulkin Allah. Ya yi mu’ujizai masu yawa. Me ya sa ya yi hakan? Bari mu gani.
—An ɗauko daga littattafan Matta, Markus, Luka, da Yohanna.
◼ Ta yaya ne Yesu ya koyar da cewa shi ne Sarki Almasihu?
◼ A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna cewa zai yi sarauta cikin adalci?
◼ Ta yaya ne Yesu ya bayyana dalla-dalla cewa Mulkinsa ba zai kasance sashen wannan duniyar ba?
◼ Ta yaya Yesu ya nuna cewa sarautarsa za ta kasance bisa ƙauna?
[Bayanin da ke shafi na 20]
“Ya yi ta yawo a cikin . . . ƙauyuka, yana wa’azi, yana kawo bishara ta mulkin Allah.”—Luka 8:1
[Taswira a shafi na 20]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
● Matta
● Markus
● Luka
● Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus
2 Timotawus
Titus
Filimon
Ibraniyawa
Yaƙub
1 Bitrus
2 Bitrus
1 Yohanna
2 Yohanna
3 Yohanna
Wasiƙa ta Yahuda
Ru’ya ta Yohanna

