Allah Ya Ceci ’Ya’yan Isra’ila
Sashe 7
Allah Ya Ceci ’Ya’yan Isra’ila
Jehobah ya jefi ƙasar Masar da annoba, kuma Musa ya ja-goranci ’ya’yan Isra’ila suka fice daga ƙasar. Allah ya ba Isra’ila Doka ta hanyar Musa
’YA’YAN Isra’ila sun yi shekaru da yawa suna zaune a ƙasar Masar, suna samun arziki kuma suna ƙara yin yawa. Amma, sai aka yi wani sabon Fir’auna. Wannan sarkin bai san Yusufu ba. Wannan azzalumin da ke jin tsoron ƙaruwar da Isra’ilawa suke yi, ya mai da su bayi kuma ya ba da umurni cewa a jefa dukan jarirai maza da suka haifa a cikin Kogin Nile. Amma wata uwa mai hikima ta kāre ɗanta, ta ɓoye shi a cikin kwando cikin ciyayi. Ɗiyar Fir’auna ta gano jaririn, ta sa masa suna Musa, kuma ta yi renonsa a cikin gidan sarautar Masar.
Sa’ad da Musa ya kai ɗan shekara 40, ya shiga matsala sa’ad da yake kāre wani bawa Ba’isra’ile daga hannun wani ɗan Masar mai ba da aiki. Musa ya gudu zuwa ƙasa mai nisa, inda ya yi zaman hijira. Sa’ad da Musa ya kai ɗan shekara 80, Jehobah ya sake aika shi zuwa ƙasar Masar don ya bayyana a gaban Fir’auna kuma ya gaya masa cewa ya saki mutanen Allah.
Fir’auna ya ƙi amincewa. Saboda haka, sai Allah ya jefi ƙasar Masar da annoba goma. A duk lokacin da Musa ya bayyana a gaban Fir’auna don ya ba shi damar kawar da annoba ta gaba, sai Fir’auna ya nuna taurin kai, kuma ya ƙi sauraron abin da Musa da Jehobah Allah suka ce ya yi. A ƙarshe, annobar ta goma ta kashe dukan ’ya’yan farin da ke ƙasar, waɗanda kawai ba su mutu ba su ne iyalan nan da suka yi biyayya ga Jehobah ta wajen yin alama da jinin ɗan tunkiya da suka yi hadaya da shi a saman ƙofarsu. Mala’ikan Jehobah da ya zo yin halaka bai taɓa waɗannan iyalan ba. Bayan hakan, Isra’ilawa suna tuna wannan ceto mai ban al’ajabi a kowace shekara ta wajen yin bikin nan mai suna Idin Ƙetarewa.
Bayan mutuwar ɗansa na fari, Fir’auna ya umurci Musa da dukan Isra’ilawa su bar ƙasar Masar. Nan da nan suka yi shirin Fitowa daga ƙasar, ƙwansu da kwarkwata. Amma sai Fir’auna ya canja ransa. Ya bi su tare da mayaƙa da karusai da yawa. Kamar dai Isra’ilawan sun faɗa tarko a bakin Jan Teku. Jehobah ya raba ruwan Jan Teku biyu, ya sa Isra’ilawa su bi kan busashiyar ƙasa, a tsakiyar bango biyu na ruwa! Sa’ad da Masarawa suka faɗa ciki don su kamo su, sai Allah ya sa ruwan ya haɗu kuma ya cinye Fir’auna da sojojinsa.
Daga baya, sa’ad da Isra’ilawa suka kafa sansani a gefen Dutsen Sinai, Jehobah ya yi alkawari da su. Ta wajen yin amfani da Musa a matsayin matsakaici, Allah ya ba Isra’ila dokoki don ta yi musu ja-gora kuma ta kāre su a dukan fasalolin rayuwarsu. Idan Isra’ilawa suka ci gaba da amincewa da sarautar Allah da aminci, Jehobah zai kasance tare da su kuma mutane za su amfana ta hanyar wannan al’ummar.
Amma, yawancin Isra’ilawa sun ɓata wa Allah rai ta wurin ƙi yin imani da shi. Saboda haka, Jehobah ya sa wannan tsarar ta yi ta yawo a cikin jeji har tsawon shekara 40. Musa ya naɗa Joshua mutum mai aminci ya gaje shi. A ƙarshe, Isra’ila tana shirye ta shiga ƙasar da Allah ya yi wa Ibrahim alkawari.
—An ɗauko daga Fitowa; Levitikus; Littafin Lissafi; Kubawar Shari’a; Zabura 136:10-15; Ayukan Manzanni 7:17-36.
◼ Waɗanne abubuwa ne da suka faru suka sa Allah ya yi amfani da Musa ya ceci Isra’ila?
◼ Menene tushen bikin Idin Ƙetarewa?
◼ Ta yaya ne Jehobah ya ’yanta Isra’ilawa daga bauta a ƙasar Masar?
[Akwati a shafi na 10]
DOKA MAFI GIRMA
Dokoki Goma da aka rubuta a Fitowa 20:1-17, wataƙila su ne aka fi sani a cikin dokoki 600 da aka ba da ta hanyar Musa. Amma, sa’ad da aka tambayi Yesu cewa cikin dokokin Allah wacce ta fi girma, ya zaɓi wannan: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka, da dukan ƙarfinka.”—Markus 12:28-30; Kubawar Shari’a 6:5.
[Taswira a shafi na 10]
Farawa
● Fitowa
● Levitikus
● Littafin Lissafi
● Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus

