Wani Annabi da ke Zaman Bauta Ya Sami Wahayi Game da Gaba

Wani Annabi da ke Zaman Bauta Ya Sami Wahayi Game da Gaba

Sashe 15

Wani Annabi da ke Zaman Bauta Ya Sami Wahayi Game da Gaba

Daniyel ya yi annabci game da Mulkin Allah da zuwan Almasihu. Babila ta faɗi

AN KAI Daniyel matashi mai aminci sosai zaman bauta a Babila kafin a halaka Urushalima. Shi da wasu Yahudawa da aka ɗauke daga masarautar Yahuda don zuwa zaman bauta, sun sami ’yanci daga waɗanda suka kamo su. A dukan rayuwarsa a Babila, Allah ya albarkaci Daniyel sosai, ya cece shi daga mutuwa a ramin zakuna kuma ya sami wahayin da ya sa ya ga abubuwan da za su faru a gaba. Annabce-annabce mafi muhimmanci na Daniyel sun mai da hankali ne a kan Almasihu da sarautarsa.

An gaya wa Daniyel lokacin da Almasihu zai bayyana. An gaya wa Daniyel lokacin da ya kamata mutanen Allah su yi zaton bayyanuwar ‘Almasihu Sarki’: makonni 69 na shekaru bayan umurnin da aka ba da a mai do da kuma sake gina bangwayen Urushalima. Mako guda yana ɗauke ne da kwanaki bakwai; makon shekaru ya ƙunshi shekaru bakwai. An ba da wannan umurnin ne da daɗewa bayan zamanin Daniyel, wato, a shekara ta 455 K.Z. Somawa daga lokacin, “bakwai” 69 ta yi daidai da shekaru 483, wadda ta ƙare a shekara ta 29 A.Z. A sashe na gaba a wannan mujallar, za mu ga abin da ya faru a wannan shekarar. Daniyel ya ga cewa za a “datse,” ko kashe Almasihu don gafarta zunubi.—Daniyel 9:24-26.

Almasihu zai zama Sarki a sama. A wahayi na musamman game da sama, Daniyel ya ga Almasihu, wanda aka kira “mai-kama da ɗan mutum,” ya nufi kursiyin Jehobah. Jehobah ya ba shi “sarauta da daraja, da mulki.” Wannan mulkin zai kasance har abada. Daniyel ya ji wani batu mai ban al’ajabi game da Mulkin Almasihu, wato, Sarkin zai yi sarauta tare da wasu, rukunin da aka kira “tsarkakan Maɗaukaki.”—Daniyel 7:13, 14, 27.

Mulkin zai halaka gwamnatocin duniyar nan. Allah ya ba Daniyel iyawa ta fassara mafarkin da ya ba Nebuchadnezzar, sarkin Babila mamaki. Sarkin ya ga babbar siffa da ke da kan zinariya, kirji da hannayen azurfa, ciki da cinyoyin jangaci, ƙafafuwan ƙarfe, da kuma sawun ƙarfe da aka haɗa da yumɓu. Dutsen da ya faɗo daga babban dutse ya faɗa kan sawun nan marar ƙwari kuma ya rugurguje siffar ya mai da ta gari. Daniyel ya bayyana cewa ɓangarorin wannan sifar suna wakiltar ƙasashe masu iko, somawa da Babila wadda ita ce kan zinariya. Daniyel ya ga cewa a lokacin sarauta ta ƙarshe ta sarakuna masu iko na wannan muguwar duniyar, Mulkin Allah zai ɗauki mataki. Zai halaka dukan gwamnatocin wannan duniyar. Bayan haka zai yi sarauta har abada.—Daniyel, sura ta 2.

A matsayin tsohon mutum, Daniyel ya ga faɗuwar Babila. Sarki Sairus ya kame birnin kamar yadda annabawa suka annabta. Ba da daɗewa ba, a ƙarshe an ’yanta Yahudawa daga zaman bautar da suke yi, daidai kan lokaci, bayan zama kango na shekaru 70 da aka annabta. A ƙarƙashin ja-gorancin gwamnoni, firistoci, da annabawa masu aminci, Yahudawa sun sake gina Urushalima da kuma haikalin Jehobah. Amma, menene zai faru bayan shekaru 483?

An ɗauko daga littafin Daniyel.

◼ Menene aka gaya wa Daniyel game da Almasihu da kuma Mulkin Allah?

◼ Yaya ne Mulkin Allah zai shafi gwamnatocin wannan duniyar?

[Taswira a shafi na 18]

Farawa

Fitowa

Levitikus

Littafin Lissafi

Kubawar Shari’a

Joshua

Alƙalawa

Ruth

1 Sama’ila

2 Sama’ila

1 Sarakuna

2 Sarakuna

1 Labarbaru

2 Labarbaru

Ezra

● Nehemiya

Esther

Ayuba

Zabura

Misalai

Mai-Wa’azi

Waƙar Waƙoƙi

Ishaya

Irmiya

Makoki

Ezekiel

● Daniyel

Hosiya

Joel

Amos

Obadiya

Yunana

Mikah

Nahum

Habakkuk

Zafaniya

Haggai

Zakariya

Malakai

Matta

Markus

Luka

Yohanna

Ayyukan Manzanni

Romawa

1 Korintiyawa

2 Korintiyawa

Galatiyawa

Afisawa

Filibiyawa

Kolosiyawa

1 Tasalonikawa

2 Tasalonikawa

1 Timotawus

2 Timotawus

Titus

Filimon

Ibraniyawa

Yaƙub

1 Bitrus

2 Bitrus

1 Yohanna

2 Yohanna

3 Yohanna

Wasiƙa ta Yahuda

Ru’ya ta Yohanna