Allah Ya Albarkaci Ibrahim da Iyalinsa
Sashe 5
Allah Ya Albarkaci Ibrahim da Iyalinsa
Zuriyar Ibrahim sun sami albarka. Allah ya kāre Yusufu a ƙasar Masar
JEHOBAH ya san cewa Ƙaunataccensa zai sha wahala kuma zai mutu wata rana. Annabcin da ke rubuce a Farawa 3:15 ya ɗan ambata wannan gaskiyar a kaikaice. Allah zai iya nuna wa mutane yadda zai ji game da wannan mutuwar kuwa? Littafi Mai Tsarki ya kwatanta hakan. Allah ya gaya wa Ibrahim ya yi hadaya da ƙaunataccen ɗansa Ishaku.
Ibrahim yana da bangaskiya mai girma. Ka tuna, Allah ya yi masa alkawari cewa Mai Ceto, ko Zuriya, da aka annabta, zai fito daga Ishaku. Domin ya gaskata cewa Allah zai ta da Ishaku daga matattu idan da bukata, cikin biyayya Ibrahim ya tafi ya yi hadaya da ɗansa. Amma wani mala’ikan Allah ya hana Ibrahim yin hakan. Sa’ad da yake yaba wa Ibrahim domin ya amince ya yi hadaya da abu mafi tamani a wurinsa, Allah ya sake maimaita alkawuransa ga wannan uban iyali mai aminci.
Bayan haka, Ishaku ya haifi ’ya’ya biyu maza, Isuwa da Yakubu. Ba kamar Isuwa ba, Yakubu ya ɗauki abubuwa na ruhaniya da tamani kuma ya sami lada. Allah ya canja sunan Yakubu zuwa Isra’ila, kuma ’ya’yan Isra’ila su sha biyu sun zama shugabannin ƙabilun Isra’ila. Amma ta yaya wannan iyalin ta zama al’umma mai girma?
Hakan ya soma ne sa’ad da yawancin ’ya’yan Isra’ila suka soma kishin ƙaninsu Yusufu. Sun sayar da shi a matsayin bawa, kuma aka kai shi ƙasar Masar. Amma Allah ya albarkaci wannan matashi mai hikima da gaba gaɗi. Duk da wahalolin da ya sha, Fir’auna, sarkin Masar, ya zaɓi Yusufu, kuma ya ba shi iko mai girma. Hakan faɗuwa ce da ta zo daidai da zama, domin yunwa ta sa Yakubu ya aika wasu cikin ’ya’yansa zuwa ƙasar Masar don su sayo abinci, sai ya zamana cewa Yusufu ne ke kula da dukan abincin! Bayan sake haɗuwar da ya yi da ’yan’uwansa wanda hakan ke cike da motsin rai da mamaki, Yusufu ya gafarta musu kuma ya ce dukan iyalin ta komo ƙasar Masar. An ba su ƙasa mafi ni’ima, inda za su iya ci gaba da yaɗuwa kuma su sami albarka. Yusufu ya fahimci cewa Allah ne ya shirya al’amuran a wannan hanyar don Ya cika alkawuransa.
Yakubu wanda ya riga ya tsufa sosai, ya ci gaba da rayuwa ne a ƙasar Masar tare da iyalinsa da take ci gaba da girma, har mutuwarsa. Kafin ya mutu, ya annabta cewa Zuriya da aka yi alkawarinsa, ko kuwa Mai Ceto, zai kasance Sarki mai iko wanda zai fito ta hanyar ɗansa Yahuda. Kafin tasa mutuwar, Yusufu ya annabta cewa wata rana, Allah zai fitar da iyalin Yakubu daga ƙasar Masar.
—An ɗauko daga Farawa surori 20 zuwa 50; Ibraniyawa 11:17-22.
◼ Menene Allah ya gaya wa Ibrahim ya yi, kuma menene yake nuna wa ’yan Adam?
◼ Ta yaya Yusufu ya sami kansa a ƙasar Masar, kuma menene sakamakon?
◼ Menene Yakubu ya annabta kafin ya mutu?
[Taswira a shafi na 8]
● Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus
2 Timotawus
Titus
Filimon
Ibraniyawa
Yaƙub
1 Bitrus
2 Bitrus
1 Yohanna
2 Yohanna
3 Yohanna
Wasiƙa ta Yahuda
Ru’ya ta Yohanna

