Saƙon da ke Cikin Littafi Mai Tsarki
Saƙon da ke Cikin Littafi Mai Tsarki
TAƘAITAWA
1 Jehobah ya halicci Adamu da Hauwa’u da damar yin rayuwa har abada a Aljanna. Shaiɗan ya yi wa sunan Allah tsegumi kuma ya zargi ikonsa na yin sarauta. Adamu da Hauwa’u sun yi tawaye tare da Shaiɗan, wanda hakan ya jawo wa su da yaransu zunubi da mutuwa
2 Jehobah ya yanke wa ’yan tawayen hukunci kuma ya yi alkawarin cewa Mai Ceto, ko Zuriya, zai fito wanda zai halaka Shaiɗan, kuma ya kawar da dukan abubuwan da tawaye da zunubi suka jawo
3 Jehobah ya yi wa Ibrahim da Dauda alkawari cewa za su kasance kakannin Zuriyar, ko Almasihu, wanda zai yi sarauta a matsayin Sarki har abada
4 Jehobah ya hure annabawa su annabta cewa Almasihu zai kawar da zunubi da mutuwa. Tare da abokan sarautarsa, zai yi sarauta a matsayin Sarkin Mulkin Allah, wanda zai kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe, rashin lafiya, har da mutuwa
5 Jehobah ya aiko Ɗansa zuwa duniya kuma ya ce Yesu ne Almasihun. Yesu ya yi wa’azi game da Mulkin Allah kuma ya ba da ransa a matsayin hadaya. Sai Jehobah ya ta da shi daga matattu a matsayin ruhu
6 Jehobah ya naɗa Ɗansa a matsayin Sarki a sama, wanda hakan ya nuna cewa an soma kwanaki na ƙarshe na wannan zamanin. Yesu yana yi wa mabiyansa a duniya ja-gora yayin da suke yin wa’azi a dukan duniya game da Mulkin Allah
7 Jehobah ya ja-goranci Ɗansa ya kawo sarautar Mulkinsa zuwa duniya. Mulkin zai halaka dukan mugayen gwamnatoci, ya kafa Aljanna, kuma ya mai da ’yan Adam masu aminci zuwa kamiltattu. Za a kunita ikon yin sarauta da Jehobah yake da shi, kuma za a tsarkake sunansa har abada

