Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Ainihin Rai”

“Ainihin Rai”

Ka Saukar:

 1. 1. Da idanuna na kalli sama, na tuna da Aljanna.

  Ga ni ga kowa duk ba ma jin tsoro,

  Muna can muna morewa.

  Za mu ji dadin rayuwa cikin Aljanna.

  Allah zai sabunta kome, muna godiya.

  (KAFIN AMSHI)

  Yanzu za mu jira ranar nan

  (AMSHI)

  Da Allah zai cika duk nufinsa, don ya kosar da kowa.

  Za mu ta da murya don mu mika ma Allah yabo

  A Aljanna!

 2. 2. Ga ꞌyanꞌuwa, kowa na aikinsa don su gyara koꞌina.

  Sai dariya, hankalinmu na kwance, muna more rayuwa.

  A Aljanna ba damuwa, ai babu kunci.

  Wannan ne ainihin rai da muke so, zai zo.

  (AMSHI)

  Jehobah zai cika duk nufinsa, za ya kosar da kowa.

  Za mu ta da murya don mu mika ma Allah yabo

  A Aljanna!

  3. Yanzu kam, zan yi ta jiran lokacin da Allah

  Na sama zai mai da wannan duniya Aljanna.

  (AMSHI)

  Jehobah zai cika duk nufinsa, za ya kosar da kowa.

  Za mu ta da murya don mu mika ma Allah yabo

  (AMSHI)

  Allah zai cika duk nufinsa, za ya kosar da kowa.

  Za mu ta da murya don mu mika ma Allah yabo

  A Aljanna!

  (KARASHEN WAKAR)

  Ainihin rai ke nan.

  Aljanna.

  Ainihin rai ke nan.

  Aljanna.

  Ainihin rai ke nan.

  Aljanna.

  Ainihin rai ke nan.

  Aljanna.