Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Halittunka Suna da Ban Mamaki

Halittunka Suna da Ban Mamaki

Ka saukar:

  1. 1. Na ji kukar tsuntsaye da sassafe.

    Ina ganin taurari fa suna bacewa.

    Rana na haskaka itatuwa,

    Ga kuma iska mai kyau tana busawa.

    (KAFIN AMSHI)

    Na ce wa Allah, Mahaliccina

    “Muna yabon ka don aikinka.” Duk da ikonka,

    Kana kaunar dukan ’yan Adam.

    (AMSHI)

    Ina yabon ka, domin ikonka.

    Ina yabon ka, domin ikonka.

    Da aikinka.

  2. 2. Halittun, nan na da ban mamaki​—

    Da rana ko daddare za ka ji kukansu.

    Bari duk halittun sama da ƙasa,

    Da waɗanda ke teku su yabe ka.

    (KAFIN AMSHI)

    Na ce wa Allah, Mahaliccina,

    Muna yabon ka don aikinka.” Duk da ikonka,

    Kana ƙaunar dukan ’yan Adam.

    (AMSHI)

    Ina yabon ka, domin ikonka.

    Ina yabon ka, domin ikonka.

    Da aikinka.

    3

    Yin tunani a kan halittunsa,

    Zai sa mu koyi abubuwa game da Allah.

    (KAFIN AMSHI)

    Na ce wa Allah, Mahaliccina,

    “Muna yabon ka, don aikinka.” Duk da ikonka,

    Kana ƙaunar dukan ’yan Adam.

    (AMSHI)

    Ina yabon ka, domin ikonka.

    Ina yabon ka, domin ikonka.

    Ina yabon ka, domin ikonka.

    Ina yabon ka, domin ikonka.

    Ina yabon ka, domin ikonka.

    Da aikinka.