Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kar Ka Ji Tsoro

Kar Ka Ji Tsoro
DUBA

Ka Saukar:

 1. 1. A lokutan da muke shan wahala,

  Za mu rikice muna bakin ciki.

  In muna cikin damuwa,

  Mu nemi taimako gun

  Allah;

  Uba.

  (AMSHI)

  Allah Yana nan, a kullayaumi,

  Zai rike hannunmu ya taimake mu.

  Kar mu manta da cewa,

  Allah ba zai manta amincinmu ba.

  Ba zai manta mu ba.

  Jim-re;

  Kar mu ji tsoro.

 2. 2. Allah ya ba mu abokan kirki.

  Da ke a shirye, kullum, su taimaka mana.

  Kuma ka ba mu Kalmar ka,

  Da ke ba mu karfin jimre

  Damuwarmu

  Koyaushe.

  (AMSHI)

  Allah Yana nan, a kullayaumi,

  Zai rike hannunmu ya taimake mu.

  Kar mu manta da cewa,

  Allah ba zai manta amincinmu ba.

  Ba zai manta mu ba.

  Jim-re.

  (KAFIN AMSHI)

  Ko abokanka sun guje ka,

  Kar ka damu.

  Kome zai yi kyau.

  (AMSHI)

  Allah Yana nan, a kullayaumi,

  Zai rike hannunmu ya taimake mu.

  Kar mu manta da cewa,

  Allah ba zai manta amincinmu ba.

  Ba zai manta mu ba.

  Jim-re.

  Kar mu ji tsoro.