Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kowa Zai Yabi Jehobah

Kowa Zai Yabi Jehobah

Ka Saukar:

 1. 1. Ba zaman lafiya

  A cikin duniyar nan.

  Babu bege, ba hadin kai,

  Koꞌina a duniya.

  Amma Allah na nan,

  Komen matsalolinmu.

  Muna marmarin ran da zai kawo

  Aljanna a duniya.

  (AMSHI)

  Mun gode ma

  Allahnmu.

  Da hadin kai

  Kowa zai bauta ma,

  Mu yabe ka tare.

 2. 2. Allah na kaunarmu.

  Ya ba mu ꞌyanꞌuwanmu.

  Zai sa mu jimre don muna zaman

  Hadin kai da salama.

  Kar mu ji tsoro sam!

  Zai share hawaye.

  Jehobah zai sa mu ji dadin

  Rai na har abada.

  (AMSHI)

  Mun gode ma

  Allahnmu.

  Da hadin kai

  Kowa zai bauta ma,

  Mu yabe ka tare.

  3. Za ka cire dukan

  Damuwar ꞌyan Adam.

  Ka nada Yesu ya yi sarauta.

  Kowa zai durkusa

  Ya yabi sunanka.

  (AMSHI)

  Mun gode ma

  Allahnmu.

  Da hadin kai

  Kowa zai bauta ma.

  Mun gode ma

  Allahnmu.

  Da hadin kai

  Kowa zai bauta ma,

  Mu yabe ka tare.

  Za a yi nufinka!