Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Maraba!

Maraba!

Ka Saukar:

 1. 1. Na san na bijire,

  Na bar kaunar Allahna.

  Damuwar rayuwa

  Ta sa na zame, na bar Jehobah.

  Amma Allah na kauna ta,

  Ya nemo ni, ya ji kukana.

  (AMSHI)

  Jehobah ya daga ni sama,

  Ya kawo ni cikin iyalinsa.

  Su ne suke kauna ta, su ne iyalina.

  Jehobah Allahna, na gode.

 2. 2. Ba inda ni zan je

  In sami kwanciyar rai,

  Sai gun mutanenka.

  Na sami abokanai da ’yan’uwa

  Da suke kiyaye ni sosai.

  Jehobah Allah na gode maka.

  (AMSHI)

  Jehobah ya jawo ka gunsa,

  Ka tuna cewa nan ne hanyar rai.

  Mutanensa suna kaunar ka da gaskiya.

  Jehobah Allahnmu, mun gode.

  3. Za mu yi murna

  Mu ce maka, “Maraba!”

  Muna kaunar ka.

  Muna godiya ga Allah.

  Maraba!

  Maraba!

  (AMSHI)

  Jehobah ya jawo ka wurinsa.

  Ya kawo ka cikin iyalinsa.

  Su ne suke kaunar ka.

  Su iyalinka ne fa,

  Maraba!