Mu Yi Amfani da Dukan Dama

Mu Yi Amfani da Dukan Dama

Ka Saukar:

  1. 1. Ranmu kamar hazo ne yake;

    Ba zato mutuwa takan zo.

    Ƙaunarmu kamar rana ce take;

    Bari ƙaunar ta haskaka, yanzu fa.

    (AMSHI)

    Ina iya shagala da wasu abubuwa,

    Har in manta da muhimmancin ƙauna.

    Yau ina iya jinƙirin yin abu mai kyau fa,

    Amma ba na son yin da-na-sani fa.

    Ina ƙoƙartawa sosai, domin kar damar ta wuce.

  2. 2. Halittu masu kyau ko’ina,

    Na nuna min ƙaunar Allahnmu,

    Na san zan ba shi dukan ƙarfina

    Duk minti, duk sa’o’in raina na ba ka.

    (AMSHI)

    Ina iya shagala da wasu abubuwa,

    Har in manta da muhimmancin ƙauna.

    Yau ina iya jinkirin yin abu mai kyau fa,

    Amma ba na son yin da-na-sani fa.

    Ina ƙoƙartawa sosai, domin kar damar ta wuce.

  3. 3. Sabuwar duniya tana gaba

    Da Jehobah zai ba mu.

    Shi ya sa za mu ba da lokacinmu.

    Kafin ranarsa ta zo,

  4. (AMSHI)

    Zan yi duk abubuwan da ya kamata in yi

    Kamar nuna wa ’yan’uwana ƙauna.

    Ba zan taɓa jinkirin yin, nagarta ga mutane,

    Domin ba na son yin da-na-sani fa.

    Shi ya sa nake ƙoƙartawa, domin kar damar ta wuce.