Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Me ya sa Yusufu ya yi aski kafin ya je gaban Fir’auna?

Hoton Mutanen da ake Musu Aski a Bangon Masar a Zamanin Dā

Kamar yadda littafin Farawa ya nuna, Fir’auna ya ce a kawo Yusufu Ba’ibrane wanda ke cikin fursuna zuwa wurinsa don ya fassara mafarkin da ke tayar da hankalinsa. A wannan lokacin, Yusufu ya riga ya yi shekaru da yawa a fursuna. Ko da yake Fir’auna yana so a kawo shi da gaggawa, amma sai da Yusufu ya fara zuwa ya yi aski tukun. (Farawa 39:​20-23; 41:​1, 14) Batun nan da marubucin wannan littafin ya ambata ya nuna cewa ya san al’adun Masarawa sosai.

Mutanen zamanin dā sun saba barin gemu, har da Ibraniyawa ma. Akasin haka, littafin nan McClintock and Strong’s Cyclopedia of Biblical, Theological, and Ecclesiastical Literature ya ce: “Masarawa ne kaɗai suke aske gemunsu a cikin mazaunan Gabashin Asiya a zamanin dā.”

Shin gemu kaɗai suke askewa? Mujallar nan Biblical Archaeology Review ya ce kafin Masarawa su zo gaban Fir’auna, suna gyara kansu kamar yadda suke yi sa’ad da suke so su shiga haikali. Hakan zai sa a bukaci Yusufu ya aske dukan sumar kansa da kuma na jikinsa kafin ya je gaban sarki.

Littafin Ayyukan Manzanni ya ce mahaifin Timotawus Baheleni ne. Shin hakan yana nufin cewa shi ɗan ƙasar Helas ne?

Ba lallai ba. A littattafan da aka hure manzo Bulus ya rubuta, yana yawan nuna bambanci tsakanin Yahudawa da Helenawa ko Girkawa. Kamar dai yana yin amfani da Helenawa don ya kwatanta mutanen da ba Yahudawa ba ne. (Romawa 1:16; 10:12) Abu ɗaya da ya jawo hakan shi ne yadda yaren Helenawa da al’adunsu suka yaɗu a dukan ƙasashen da Bulus ya yi wa’azi.

Su waye ne mutanen zamanin dā suke kira Helenawa? A ƙarni na huɗu kafin haihuwar Yesu, wani shahararren marubuci ɗan ƙasar Atina mai suna Isocrates ya yi alfahari don yadda al’adun Helenawa ke bazuwa a dukan duniya a lokacin. Ya ce a sakamakon haka, “ba ’yan ƙasan Helas kaɗai ake kiran Helenawa ba, amma har da mutanen da aka koya musu al­’adun ƙasar.” Saboda haka, zai yiwu cewa mahaifin Timotawus wanda ba Bayahude ba ne da kuma wasu da Bulus ya kira Helenawa ba ainihin ’yan ƙasar Helas ba ne, amma sun koyi al­’adun ne.—Ayyukan Manzanni 16:1.