Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA IYA FAHIMTAR LITTAFI MAI TSARKI

Me Ya Sa Ya Dace Ka Fahimci Littafi Mai Tsarki?

Me Ya Sa Ya Dace Ka Fahimci Littafi Mai Tsarki?

“Littafi Mai Tsarki sanannen littafi ne na addini. Amma a gani na, ba zai amfani ‘yan Caina ba.”​—⁠LIN, A ƘASAR CAINA.

“Ni ɗan addinin Hindu ne kuma ba na fahimtar littattafan addinin. To, ta yaya zan fahimci Littafi Mai Tsarki?”​—⁠AMIT, A ƘASAR INDIYA.

“Ina daraja Littafi Mai Tsarki domin tsohon littafi ne kuma na ji cewa littafi ne da aka fi sayarwa. Amma ban taɓa ganin sa ba.”​—⁠YUMIKO, A ƘASAR JAFAN.

Mutane da dama a duniya suna mutunta Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, ba su san abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba sosai ko kuma ba su ma san kome cikinsa ba. Yanayin da miliyoyin mutane a Asiya suke ciki ke nan, har da wasu ƙasashen da Littafi Mai Tsarki sananne littafi ne.

Amma, kana iya yin wannan tambayar, ‘Me ya sa nake bukata na fahimci Littafi Mai Tsarki?’ Fahimtar abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai sa ka san yadda za ka:

  • Sami gamsuwa da farin ciki

  • Bi da matsalolin iyali

  • Bi da alhini

  • Zama abokin kirki

  • Yi amfani da kuɗi yadda ya dace

Ka yi la’akari da misalin Yoshiko daga ƙasar Jafan. Ta karanta Littafi Mai Tsarki domin ta so ta san abin da ke cikinsa. Wane sakamako ta samu? Ta ce: “Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in san abin da ya sa aka halicce mu kuma in san abin da zan more a nan gaba. A yanzu, ba na ji kamar ina ɓata lokacina.” Wani mai suna Amit da aka ambata ɗazun ya tsai da shawarar karanta Littafi Mai Tsarki. Ya ce: “Abin da na karanta ya burge ni sosai. Littafi Mai Tsarki zai iya amfanar kowa da kowa.”

Babu shakka, Littafi Mai Tsarki ya shafi rayuwar miliyoyin mutane. Zai dace ka karanta shi don ka ga yadda za ka amfana.