Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA IYA FAHIMTAR LITTAFI MAI TSARKI

Littafin da Za A Iya Fahimta

Littafin da Za A Iya Fahimta

Babu shakka, Littafi Mai Tsarki tsohon littafi ne sosai. Shekarunsa nawa ne? An soma rubuta Littafi Mai Tsarki a Gabas ta Tsakiya wajen shekaru 3,500 da suka shige. Wato a lokacin da aka kafa daula ta farko a ƙasar Caina ke nan, kuma kusan shekara dubu kafin a soma addinin Buddha a Indiya.​—⁠Ka duba akwatin nan “ Gaskiya Game da Littafi Mai Tsarki.”

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa mai gamsarwa ga muhimman tambayoyi na rayuwa

Idan ana son littafi ya kasance da amfani kuma ya ja-goranci mutane, wajibi ne ya zama mai sauƙin fahimta kuma ya tattauna abin da ya shafi mutane. Haka Littafi Mai Tsarki yake. Yana ɗauke da amsoshi masu gamsarwa ga muhimman tambayoyi.

Alal misali, ka taɓa yin wannan tambayar kuwa, ‘Me ya sa aka halicce mu?’ Wannan tambayar tana damun mutane da yawa. Duk da haka, za a iya samun amsar a littafin Farawa surori ɗaya da biyu a cikin Littafi Mai Tsarki. A cikin waɗannan ayoyin, Littafi Mai Tsarki ya ambata abin da ya faru a “farko,” wato biliyoyin shekaru da suka shige. A lokacin, ba a halicci sararin sama da taurari da kuma duniya ba tukun. (Farawa 1:⁠1) Bayan haka, ya ambata yadda aka halicci duniya don a zauna a cikinta da yadda aka halicci dabbobi da mutane da kuma dalilin da ya sa aka halicce su.

AN RUBUTA SHI DON A FAHIMTA

Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da shawarwari masu kyau da za su taimaka mana mu bi da matsalolinmu na yau da kullum. Yana da sauƙin fahimta. Akwai abubuwa biyu da suka tabbatar mana da hakan.

Na ɗaya, Littafi Mai Tsarki yana da sauƙi da kuma daɗin karantawa. Babu labarai masu ruɗarwa a ciki, maimakon haka, yana ɗauke da bayanan da suka shafe mu. An yi amfani da kalmomin da muke amfani da su yau da kullum don a bayyana batutuwa masu wuya.

Alal misali, Yesu ya yi amfani da kwatanci masu sauƙi da mutane suka sani don ya koyar da darussan da za su ratsa zukatansu. Za mu iya ganin irin waɗannan kwatancin a huɗubar Yesu a kan dutse da ke cikin littafin Matta surori 5 zuwa 7 a cikin Littafi Mai Tsarki. Wani masani ya ce wannan huɗubar “jawabi ne mai kyau domin ba a yi shi don a wayar da kanmu ba amma don mu kasance da ɗabi’a mai kyau.” Za  ka iya karanta waɗannan ayoyin cikin mintoci 15 zuwa 20, kuma za ka yi mamakin yadda kalmomin Yesu suke da sauƙi da kuma ma’ana.

Wani abu kuma da ya sa Littafi Mai Tsarki yake da sauƙin fahimta shi ne abin da ya tattauna. Ba littafin ƙage ba ne da kuma tatsuniya. Amma, Kundin Sani ya ce Littafi Mai Tsarki “ya yi magana game da attajirai da talakawa, kuma ya yi magana game da famansu da kasawarsu da kuma nasararsu.” Yana da sauƙi mu fahimci labaran mutanen da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki da kuma muhimman darussan da ke cikinsa.​—⁠Romawa 15:⁠4.

KOWA ZAI IYA KARANTA SHI

Idan ana so ka fahimci wani littafi, dole ne a rubuta shi a yaren da ka fahimta. Babu shakka, akwai Littafi Mai Tsarki a wani yaren da ka fahimta ko da a ina kake da zama kuma ko da kai ɗan wane ƙasa ne. Ka yi la’akari da abin da aka yi don hakan ya yiwu.

Fassara. Tun asali, an rubuta Littafi Mai Tsarki a Ibrananci da Aramaic da kuma Helenanci kuma hakan zai iya hana mutane da yawa karanta shi. Amma mafassara da yawa sun yi aiki tuƙuru don su juya shi cikin harsuna da dama. Famar da suka yi ya sa an sami Littafi Mai Tsarki a harsuna 2,700 a yau. Hakan yana nufin cewa sama da kashi 90 cikin 100 na mutane za su iya karanta wani sashe na Littafi Mai Tsarki a yarensu.

Wallafawa. An rubuta asalin Littafi Mai Tsarki a kan fata da kuma ganye kuma waɗannan abubuwan za su iya lalacewa da sauri. Daga baya, sai mutane dabam-dabam suka kofe Littafi Mai Tsarki da hannu sau da sau don wasu ma su samu su karanta. Irin waɗannan littattafan suna da tsada kuma mutane ƙalilan ne suke iya sayen su. Amma na’urar buga littattafai da wani mai suna Gutenberg ya ƙera sama da shekara 550 da suka shige, ya sa wallafa Littafi Mai Tsarki ta yi sauƙi sosai. Wani rahoto ya ce an riga an rarraba cikakken Littafi Mai Tsarki ko rabinsa sama da kofi biliyan biyar.

Babu littattafan addinai da za a iya gwadawa da Littafi Mai Tsarki. Babu shakka, Littafi Mai Tsarki littafi ne da za mu iya fahimta. A wasu lokuta, fahimtar sa zai iya kasancewa da ƙalubale. Amma, akwai abin da zai iya taimaka mana. A ina za mu iya samun wannan taimakon? Kuma yaya za ka iya amfana? Za ka sami amsar a talifi na gaba.