Ayyukan Manzanni 16:1-40
16 Sai ya isa Darbe da kuma Listira. A wurin, akwai wani almajiri mai suna Timoti, mamarsa Bayahudiya ce kuma ta ba da gaskiya ga Yesu, amma babansa mutumin Girka ne,
2 kuma ꞌyanꞌuwa da ke Listira da Ikoniya sun faɗi abubuwa masu kyau game da shi.
3 Bulus ya ce yana so Timoti ya riƙa bin sa, sai ya ɗauke shi ya yi masa kaciya saboda Yahudawa da ke wuraren, domin dukansu sun san cewa baban Timoti mutumin Girka ne.
4 Yayin da suke tafiya zuwa birane dabam-dabam, sukan gaya ma ꞌyanꞌuwa da ke wuraren shawarwarin da manzanni da kuma dattawa da ke Urushalima suka yanke don su bi shawarwarin.
5 Ta hakan, ikilisiyoyin sun ci-gaba da tsayawa da ƙarfi cikin bangaskiya kuma sun ci-gaba da ƙaruwa kowace rana.
6 Ƙari ga haka, sun bi ta cikin Farijiya da Galatiya, domin ruhu mai tsarki ya hana su yin shelar kalmar Allah a yankin Asiya.
7 Ban da haka ma, da suka shiga cikin Misiya, sun yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma ruhun Yesu bai bar su su yi hakan ba.
8 Sai suka wuce* Misiya, suka gangara zuwa Toruwas.
9 A daren, Bulus ya ga wahayi, kuma a wahayin ya ga wani mutumin Makidoniya yana tsaye a wurin kuma yana roƙon shi yana cewa: “Ka shigo cikin Makidoniya ka taimaka mana.”
10 Da Bulus ya ga wahayin, nan take muka yi ƙoƙari mu shiga Makidoniya, don mun tabbata cewa Allah ne ya kira mu mu yi musu waꞌazin labari mai daɗi.
11 Sai muka tashi da jirgin ruwa daga Toruwas kuma muka miƙe zuwa Samotiras, washegari kuma muka shiga Niyafolis;
12 daga wurin kuma sai muka shiga Filibi, wani birni da ke ƙarƙashin mulkin Roma, kuma shi ne birni mafi muhimmanci a yankin Makidoniya. Mun zauna a birnin nan na ꞌyan kwanaki.
13 A Ranar Assabaci, mun fita ta ƙofar birnin zuwa kusa da wani kogi, mun yi tsammanin akwai wurin adduꞌa a wurin, sai muka zauna kuma muka fara yi wa matan da suka taru a wurin magana.
14 Sai wata mata mai suna Lidiya, daga birnin Tayatira, wadda take sayar da yaduna masu kalar jar garura, kuma ita mai bautar Allah ce, tana saurara, kuma Jehobah* ya buɗe zuciyarta don ta kasa kunne ga abubuwan da Bulus yake faɗa.
15 Bayan ita da iyalinta suka yi baftisma, sai ta roƙe mu tana cewa: “Idan kun ɗauke ni a matsayin mai ba da gaskiya ga Jehobah,* sai ku zo gidana ku sauka.” Yadda ta roƙe mu ya sa muka je.
16 Wata rana, yayin da muke zuwa wurin yin adduꞌa, sai ga wata yarinya da ke da aljani mai duba, ta same mu. Iyayengijinta kuma suna samun kuɗi da yawa ta wurin duban da take yi.
17 Yarinyar ta ci-gaba da bin mu da kuma Bulus, kuma tana ihu tana cewa: “Waɗannan mutanen bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, kuma suna yi muku shelar hanyar samun ceto.”
18 Ta ci-gaba da yin hakan na kwanaki da yawa, a ƙarshe Bulus ya gaji da hakan kuma ya juye ya ce wa aljanin: “Na umurce ka a cikin sunan Yesu Kristi, ka fita daga jikinta.” Sai aljanin ya fita nan da nan.
19 Da iyayengijinta suka ga cewa hanyar samun kuɗinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sailas, kuma suka kai su kasuwa a gaban shugabanni.
20 Da suka kai su gaban hukumomi, sai suka ce: “Waɗannan mutanen suna ta da hankalin mutanen birninmu sosai. Su Yahudawa ne,
21 kuma suna shelar alꞌadu da bai kamata mu bi ba da yake mu Romawa ne.”
22 Sai jamaꞌar suka taru a kansu gabaki-ɗaya, bayan da hukumomin suka yayyage rigunansu, sai suka ba da umurni cewa a yi musu dūka da sanduna.
23 Bayan da suka yi musu dūka sosai, sai suka jefa su a cikin kurkuku, kuma suka umurci mai tsaron kurkukun ya yi gadin su da kyau.
24 Da yake an ba shi wannan umurnin, sai ya sa su can ciki-cikin kurkukun, ya sa ƙafafunsu a cikin katakon riƙe ƙafafu kuma ya kulle.
25 Wajen tsakar dare, Bulus da Sailas suna adduꞌa, suna waƙoƙin yabo ga Allah, sauran fursunonin kuma suna saurarar su.
26 Nan da nan sai aka yi wata girgizar ƙasa mai ƙarfi, har tushen ginin kurkukun ya girgiza. Ƙari ga haka, dukan ƙofofin sun buɗu, kuma sarƙoƙin dukan fursunonin sun kunce.
27 Saꞌad da mai tsaron kurkukun ya tashi, kuma ya ga cewa ƙofofin kurkukun a buɗe suke, sai ya zare takobinsa, yana so ya kashe kansa domin yana tsammanin fursunonin sun gudu.
28 Amma Bulus ya ɗaga murya kuma ya ce masa: “Kada ka ji wa kanka rauni, don dukanmu muna nan!”
29 Sai ya ce a kawo fitilu kuma ya shiga ciki da gudu, sai ya faɗi a gaban Bulus da Sailas, yana rawar jiki don tsoro.
30 Sai ya fitar da su waje kuma ya ce: “Masu girma, mene ne zan yi don in sami ceto?”
31 Sai suka ce masa: “Ka ba da gaskiya ga Ubangiji Yesu kuma za ka sami ceto, kai da mutanen gidanka.”
32 Sai suka yi masa da dukan waɗanda suke gidansa waꞌazin kalmar Jehobah.*
33 A cikin daren, ya ɗauke su ya wanke musu raunukansu. Sai aka yi masa da dukan mutanen gidansa baftisma ba tare da ɓata lokaci ba.
34 Sai ya kawo su cikin gidansa, ya shirya musu abinci a kan teburi, sai shi da dukan mutanen gidansa suka yi murna sosai, da yake yanzu ya ba da gaskiya ga Allah.
35 Da gari ya waye, sai hukumomin suka aiki ꞌyan sanda su ce: “Ka saki mutanen nan.”
36 Mai tsaron kurkukun ya gaya wa Bulus cewa: “Hukumomi sun aiki mutane su gaya mini in saki dukanku biyu. Don haka, ku fito yanzu, kuma ku sauka lafiya.”
37 Amma Bulus ya ce musu: “Sun yi mana dūka a fili, ba tare da yi mana shariꞌa ba, duk da cewa mu Romawa ne, suka kuma jefa mu cikin kurkuku, yanzu suna so su fitar da mu a ɓoye ne? Aꞌa, sai dai su zo su raka mu da kansu.”
38 Sai ꞌyan sandan suka gaya wa hukumomin abin da suka ce. Hukumomin sun ji tsoro da suka ji cewa Bulus da Sailas Romawa ne.
39 Sai suka zo suka roƙe su, kuma bayan da suka raka su waje, sai suka gaya musu su bar birnin.
40 Amma suka bar kurkukun kuma suka tafi gidan Lidiya; da suka ga ꞌyanꞌuwa a wurin, sai suka ƙarfafa su kuma suka tafi.
Hasiya
^ Ko kuma “suka bi cikin.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.