Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Za a Taba Yin Duniyar da Babu Munafunci?

Za a Taba Yin Duniyar da Babu Munafunci?

PANAYIOTA wata ce da ta yi girma a wani tsibiri a Bahar Rum. A lokacin da take matashiya ta yi sha’awar siyasa sosai. Daga baya, ta yi aiki a matsayin sakatariyar wata ƙungiyar siyasa a ƙauyen da take da zama. Ta shiga gida-gida don ta tara wa ƙungiyarsu kuɗi. Amma daga baya, Panayiota ta yi sanyin gwiwa. Ko da yake ‘yan siyasa suna yi kamar su abokan juna ne, amma suna wariya da mugun buri da rashin yarda da juna da kuma kishi.

Wani mutum mai suna Daniel ya taso ne a wani iyali da suke son ibada sosai a ƙasar Ireland. Amma abin baƙin ciki, ya tuna da munafuncin da limaminsu yake yi. Yakan sha giya ya bugu, ya yi cāca kuma ya saci kuɗi daga asusun coci. Duk da haka, sai ya zo yana ta wa’azi cewa Allah zai ƙone Daniel da wuta idan ya yi zunubi.

Wani mai suna Jeffrey ya yi yawancin rayuwarsa yana kasuwanci da masu jiragen ruwa da suke da zama a Biritaniya da kuma Amirka. Ya tuna yadda kwastomomi da ‘yan kasuwa suke zamba sa’ad da suke ma’amala da ma’aikatan gwamnati. Waɗannan mutanen suna a shirye su yi kowane irin munafunci don a ba su kwangila.

Abin baƙin cikin shi ne, mutane sun saba yin hakan. Munafunci yana ko’ina a duk inda ɗan Adam yake a faɗin duniya. Ana munafunci a siyasa da addini da kuma kasuwanci. An ɗauko kalmar nan munafunci a wasu yaruka daga kalmar Helenancin nan hypokrites. Wannan kalmar tana nufin wani mai jawabi ko mai wasan kwaikwayo da ya rufe fuskarsa a lokacin da yake jawabi ko kuma wasa. Daga baya, an yi amfani da wannan kalmar don a kwatanta mutumin da yake yin wasu ayyuka don ya yaudari mutane ko kuma ya cim ma wani mugun buri.

Munafunci zai iya sa mutane su ji haushi da fushi kuma su fusata. A wasu lokuta, za mu iya jin wasu sun ce da ɓacin rai: “Wai yaushe ne za a daina munafunci?” Abin farin cikin shi ne, Kalmar Allah ta ba mu dalilan da za su taimaka mana mu gaskata cewa hakan zai yiwu.

YADDA ALLAH DA KUMA ƊANSA SUKE ƊAUKAN MUNAFUNCI

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa wani halittar ruhu ne ya soma munafunci ba mutane ba. A tarihin ‘yan Adam, Shaiɗan ko Iblis ya ɓad da kamaninsa ta wurin yin amfani da maciji kamar yadda  ɗan wasa yake rufe fuskarsa. Sai ya sa Hawwa’u ta gaskata cewa idan ta yi rashin biyayya, zai taimaka mata. (Farawa 3:​1-5) Tun daga lokacin, mutane da yawa sun ɓad da kamaninsu don su yaudari mutane da kuma cim ma wani mugun buri.

A lokacin da al’ummar Isra’ila suka soma munafunci da kuma bautar ƙarya, Allah ya gargaɗe su sau da sau a kan abin da zai faru da su. Jehobah ya gaya musu ta wurin annabinsa cewa: “Tun da wannan jama’a suna gusowa gareni, da bakinsu da leɓunansu suna girmama ni, amma sun nisantar da zuciyarsu daga gareni.” (Ishaya 29:13) A lokacin da Isra’ilawa suka ƙi tuba, Allah ya ƙyale wasu al’ummai su halaka wuraren bauta na Isra’ila, wato Urushalima da haikalinta. Da farko, Babiloniyawa sun yi hakan a shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu. Bayan haka, sai Romawa suka halaka ta a shekara ta 70 bayan haihuwar Yesu. Hakika, Allah ba ya ƙyale munafunci ya ci gaba har abada ba.

A wani ɓangare kuma, Allah da Ɗansa, Yesu suna mutunta mutanen da suke faɗin gaskiya. Alal misali, a lokacin da Yesu ya soma hidima, wani mutum mai suna Natanayilu ya zo wurinsa. Da Yesu ya gan shi, sai ya ce: “Duba, ga mutumin Isra’ila na gaske, wanda ba shi da algus!” (Yohanna 1:47) Daga baya, Natanayilu wanda ake kira Barthalamawus, ya zama ɗaya cikin manzannin Yesu 12.​—⁠Luka 6:​13-16.

Yesu ya yi zama da abokansa kuma ya koya musu ra’ayin Allah. Bai kamata mabiyan Yesu su zama munafukai ba. Yesu ya yi tir da munafuncin da malaman addini suke yi a lokacin. Ka yi la’akari da wasu hanyoyin da ya yi hakan.

Suna yin ‘adalci’ don mutane su gani. Yesu ya ce: “Ku yi lura kada ku yi marmarin nuna adalcinku a gaban mutane, domin su gani . . . kamar yadda munafukai ke yi.” Ya ce su riƙa ba da kyauta a “ɓoye” kuma kada su riƙa addu’a don mutane su gansu. Idan suka bi wannan umurnin, Allah zai amince da bautar da suke masa.​—⁠Matta 6:​1-6.

Suna saurin kushe mutane. Yesu ya ce: “Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da ke idonka tukuna, sa’an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan’uwanka.” (Matta 7:​5, Littafi Mai Tsarki) Idan wani yana saurin hangen kura-kuran wasu kuma ya manta da nasa, wannan mutumin yana ƙoƙarin ɓad da kamaninsa ne. A gaskiya, “dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.”​—⁠Romawa 3:⁠23.

Suna da mugun manufa. Wata rana almajiran Farisawa da mabiyan Hiridus suka zo wurin Yesu don su tambaye shi game da haraji. Da daɗin baƙi suka ce ma Yesu: “Malam, mun sani kai mai-gaskiya ne, kana kuwa koyarwar tafarkin Allah cikin gaskiya.” Bayan haka, sai suka ɗana masa tarko da wannan tambayar: “Halal ne a ba da gandu ga Kaisar, ko kuwa ba haka ba?” Sai Yesu ya ce: “Don me kuke gwada ni, ku munafukai?” Yesu kai tsaye ya kira su munafukai don ba wai suna neman amsar tambayar ba ne amma suna so “su yi masa tarko cikin zancensa” ne.​—⁠Matta 22:​15-22.

Kiristoci na gaskiya suna ƙauna “mai-fitowa daga zuciya mai-tsabta da lamiri mai-nagarta da bangaskiya marar-riya.”—1 TIMOTAWUS 1:5

Mabiyan Kristi sun kasance da gaskiya sosai a lokacin da aka kafa ikilisiyar Kirista a Fentakos na shekara ta 33. Kiristoci na gaskiya sun yi aiki tuƙuru don su daina munafunci. Alal misali, Bitrus, ɗaya daga cikin manzannin Yesu sha biyu ya ƙarfafa ‘yan’uwansa Kiristoci su yi biyayya “ga gaskiya zuwa ga sahihiyar ƙauna ta ‘yan’uwa.” (1 Bitrus 1:22) Manzo Bulus ya ƙarfafa abokan aikinsa cewa ƙaunarsu ta zama mai “fitowa daga zuciya mai-tsabta da lamiri mai-nagarta da bangaskiya marar-riya.”​—⁠1 Timotawus 1:⁠5.

IKON KALMAR ALLAH

Koyarwar Yesu da na manzanninsa da ke cikin Littafi Mai Tsarki suna taimaka mana sosai, kamar yadda suka taimaka wa Kiristoci a ƙarni na farko. Game da wannan, manzo Bulus ya ce: “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa, ta fi kowane takobi mai-kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa mararrabar rai da ruhu, da gaɓaɓuwa da ɓargo kuma,  tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.” (Ibraniyawa 4:12) Sanin koyarwar Littafi Mai Tsarki da kuma yin rayuwa daidai da koyarwar, ta taimaka wa mutane da yawa su daina yin munafunci kuma su kasance da gaskiya. Ka yi la’akari da labaran mutane uku da aka ambata a baya.

“Na ga yadda ‘yan’uwa suka damu da mutane da kuma yadda ake nuna ƙauna ta gaskiya.”—PANAYIOTA

Rayuwar Panayiota ta canja sa’ad da aka gayyace ta zuwa taron Shaidun Jehobah. Ta ga mutane suna nuna halin kirki da zuciya ɗaya ba da munafunci ba. Ta ce: “Na ga yadda ‘yan’uwa suka damu da mutane da kuma yadda ake nuna ƙauna ta gaskiya, kuma ban saba gani haka ba a duk shekarun da na yi ina siyasa.”

Panayiota ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ta yi baftisma. Hakan ya faru shekaru 30 da suka shige. Ta ce: “Yanzu na gano cewa rayuwa mai ma’ana bai dangana ga zuwa gida-gida ana siyasa ba, a maimakon hakan, yin wa’azi game da Mulkin Allah ne kaɗai za ta sa duniya ta gyaru.”

“Ban so ‘yan’uwa suna mini kallon mutumin kirki, amma a gaskiya ba haka nake ba.”—DANIEL

Daniel ya sami ci gaba sosai a ƙungiyar Jehobah kuma an ba shi wasu ayyuka. Bayan ‘yan shekaru kaɗan, sai ya yi kuskure kuma zuciyarsa ta soma damunsa. Ya ce: “Da na yi tunani a kan munafunci da na gani ake yi a coci, sai na tsai da shawara cewa zan kai ƙarar kaina wajen dattawa ko da hakan zai sa na daina wasu ayyukan da nake yi a ikilisiya. Ban so ‘yan’uwa suna mini kallon mutumin kirki, amma a gaskiya ba haka nake ba.”

Abin farin cikin shi ne, bayan ɗan lokaci da aka ma Daniel horo, sai ya soma ayyukan da yake yi a dā a ikilisiya da zuciya ɗaya. Mutanen da suke bauta wa Allah ba tare da munafunci ba ne za su iya kasancewa da gaskiya irin wannan. Sun koya su “cire gungume” da ke idanunsu kafin su “cire ɗan hakin” da ke idanun ‘yan’uwansu.

“Na fahimci cewa bai kamata na yi maguɗi ba. . . . Littafin Misalai 11:1 ya ratsa zuciyata.”—JEFFERY

Jeffery, da ya daɗe yana kasuwanci ya ce: “Da na ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki, sai na fahimci cewa bai kamata na yi maguɗi don in sami kwangila ba. Littafin Misalai 11:1 ya ratsa zuciyata. Ayar ta gaya mana cewa ‘mizani na algus abin ƙyama ne ga Ubangiji.’” Hakika, Jeffery bai kasance kamar waɗanda suka yi wa Yesu tambaya game da haraji ba, domin ya tsai da shawarar kasancewa da gaskiya ga ‘yan’uwansa Shaidu da waɗanda ba Shaidu ba.

Miliyoyin Shaidun Jehobah a faɗin duniya suna ƙoƙarin yin abin da suka koya daga Littafi Mai Tsarki. Suna aiki tuƙuru don su “ɗauki sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.” (Afisawa 4:24) Muna ƙarfafa ku ku yi bincike don ku san Shaidun Jehobah sosai da abubuwan da suka gaskata da kuma yadda za su taimaka muku ku san abubuwa game da sabuwar duniya. Za a yi “adalci” a “sabuwar duniya” inda ba za a sake yin munafunci ba.​—⁠2 Bitrus 3:13.