Ta Hannun Matiyu 6:1-34
6 “Ku yi hankali don kada ku yi ayyukan adalci a gaban mutane don su ga kuna yi; idan kuka yi haka, ba za ku samu lada daga wurin Ubanku wanda yake sama ba.
2 Don haka, saꞌad da za ku ba da kyauta ga talakawa, kada ku yi ta sanarwa* domin mutane su ji, kamar yadda munafukai suke yi a majamiꞌu da kan tituna, don mutane su riƙa yaba musu. A gaskiya ina gaya muku cewa, sun riga sun sami ladansu.
3 Amma a lokacin da kuke ba da kyauta ga talakawa, kada ku bar hannunku na hagu ya san abin da hannunku na dama yake yi,
4 domin kyautar da kuke bayarwa ta kasance a ɓoye. Idan kun yi hakan, Ubanku wanda yake ganin abin da mutane suke yi a ɓoye zai ba ku lada.
5 “Ƙari ga haka, a lokacin da kuke yin adduꞌa, kada ku yi kamar munafukai. Suna son yin adduꞌa a tsaye a cikin majamiꞌu da kuma a kan hanya domin mutane su gan su. A gaskiya ina gaya muku cewa, sun riga sun sami ladansu.
6 Amma a lokacin da kuke yin adduꞌa, sai ku shiga cikin ɗakinku, bayan kun rufe ƙofa, ku yi adduꞌa ga Ubanku wanda yake sama. Idan kun yi hakan, Ubanku wanda yake ganin abin da mutane suke yi a ɓoye zai ba ku lada.
7 Saꞌad da kuke yin adduꞌa, kada ku yi ta maimaita abubuwa iri ɗaya kamar yadda mutanen alꞌummai suke yi, domin suna ganin kamar yin maganganu da yawa zai sa Allah ya ji adduꞌarsu.
8 Saboda haka, kada ku zama kamar su, domin Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku tambaye shi.
9 “Sai ku yi adduꞌa haka:
“‘Ubanmu wanda yake cikin sama, a tsarkake sunanka.
10 Mulkinka ya zo. Bari a yi nufinka a duniya kamar yadda ake yin sa a sama.
11 Ka ba mu abincinmu na yau.
12 Ka yafe mana bashin da kake bin mu,* kamar yadda muka yafe ma waɗanda muke bin su bashi.*
13 Kada ka kai mu cikin jarraba, amma ka cece mu daga mugun nan.’
14 “Domin idan kun gafarta laifofin da mutane suka yi muku, Ubanku wanda yake sama zai gafarta laifofinku;
15 amma idan ba ku gafarta wa mutane laifofin da suka yi muku ba, Ubanku ma ba zai gafarta muku laifofinku ba.
16 “Idan kuna azumi, ku daina ɓata fuska kamar yadda munafukai suke yi, ba sa wanke fuskarsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. A gaskiya ina gaya muku cewa, sun riga sun sami ladansu.
17 Amma idan kuna azumi, ku shafa māi a kanku kuma ku wanke fuskarku,
18 domin kada mutane su ga cewa kuna azumi, sai dai Ubanku wanda yake sama ne kawai zai gani. Idan kun yi hakan, Ubanku wanda yake ganin abin da mutane suke yi a ɓoye zai ba ku lada.
19 “Ku daina tara wa kanku dukiya a duniya, wurin da ƙwari da tsatsa za su lalatar da ita, wurin da ɓarayi za su iya shiga su sata.
20 Maimakon haka, ku tara wa kanku dukiya a sama, wurin da ƙwari da tsatsa ba za su cinye ta ba, kuma ɓarayi ba za su iya shiga su sata ba.
21 Domin inda dukiyarku take, wurin ne zuciyarku za ta kasance.
22 “Ido ne fitilar jiki. Idan ba kwa yin rawan ido, jikinku zai kasance da haske.
23 Amma idan kuna rawan ido,* jikinku zai yi duhu. Idan hasken jikinku duhu ne da gaske, lallai duhun zai yi tsanani sosai.
24 “Babu wanda zai iya yi wa shugabanni biyu hidima; sai dai ya so ɗaya ya kuma ƙi ɗayan, ko ya yi wa ɗaya ladabi ya kuma rena ɗayan. Ba za ku iya bauta wa Allah da kuma Dukiya ba.
25 “Domin wannan, ina gaya muku: Ku daina yawan damuwa a kan yadda za ku rayu, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha. Kuma ku daina yawan damuwa a kan abin da za ku saka a jiki. Shin rai bai fi abinci ba? Kuma jiki bai fi abin da za ku saka ba?
26 Ku dubi tsuntsayen sama da kyau; ba sa shuka iri, ko girbi, ko ma su tara a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Shin ba ku fi su daraja ba?
27 Wane ne a cikinku ta yawan damuwa zai iya ƙara ko minti ɗaya* ga tsawon rayuwarsa?
28 Ƙari ga haka, me ya sa kuke yawan damuwa a kan abin da za ku saka? Ku koyi darasi daga yadda furannin daji suke girma, ba sa aiki, ko yin saƙa;
29 duk da haka, ina gaya muku, ko Sulemanu da dukan darajarsa bai taɓa yin ado kamar ɗaya daga cikin furannin nan ba.
30 Idan har Allah zai yi wa furannin daji ado kamar haka, waɗanda a yau suna nan, gobe su bushe kuma a jefa su cikin wuta, ba kwa ganin Allah zai tanada muku abin sakawa fiye da su ba, ku masu ƙarancin bangaskiya?
31 Saboda haka, kada ku riƙa yawan damuwa kuma ku ce, ‘Mene ne za mu ci?’ ko, ‘Mene ne za mu sha?’ ko kuma, ‘Mene ne za mu saka?’
32 Domin dukan abubuwan nan ne mutanen alꞌummai suke nema da dukan zuciya. Ubanku na sama ya san kuna bukatar dukan abubuwan nan.
33 “Don haka, ku ci-gaba da sa Mulkin Allah da kuma adalcinsa* farko a rayuwarku, kuma za a ƙara muku dukan abubuwan nan.
34 Saboda haka, kada ku riƙa yawan damuwa game da gobe, don gobe ma yana da abubuwan da za ku damu a kan su. Kowace rana na da nata isasshen matsaloli.
Hasiya
^ A yaren Girka, “ku yi ta busa kakaki.”
^ Ko kuma “zunubanmu.”
^ Ko kuma “waɗanda suka yi mana laifi.”
^ Wato, kishin wasu don abin da suke da shi.
^ A yaren Girka, “kubit 1.”
^ Ko kuma “abubuwan da suka dace a gaban Allah.”