Ta Hannun Matiyu 22:1-46
22 Yesu ya sake yi musu magana ta misalai, ya ce:
2 “Za a iya kwatanta Mulkin sama da wani sarki da ya shirya ma ɗansa bikin aure.
3 Sai ya ce wa bayinsa su je su kira waɗanda aka gayyato, amma mutanen ba sa so su zo.
4 Ya sake tura wasu bayi, ya ce musu, ‘Ku gaya ma waɗanda na gayyato: “Ga shi! Na shirya abinci, na yanka bijimai, da dabbobi masu ƙiba, kuma an gama shirya kome da kome. Ku zo bikin mana.”’
5 Amma ba su damu ba. Wani ya tafi gonarsa, wani kuma ya tafi sanaꞌarsa;
6 amma sauran suka kama bayinsa, suka yi musu dūkan tsiya, kuma suka kashe su.
7 “Sai sarkin ya yi fushi sosai, kuma ya aiki sojojinsa, suka kakkashe masu kisan kuma suka ƙona garinsu.
8 Sai ya gaya wa bayinsa cewa, ‘Mun gama shirin bikin auren, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba.
9 Don haka, ku je manyan tituna, kuma ku gayyaci duk wanda kuka gani, su zo bikin auren.’
10 Bayin nan, suka tafi tituna, suka tattara duk waɗanda suka gani, da masu kirki da mugaye; sai ɗakin bikin ya cika da mutanen da suke cin abinci.
11 “Da sarkin ya shiga don ya ga baƙin, sai ya ga wani mutum da bai saka rigar biki ba.
12 Sai ya ce wa mutumin, ‘Aboki, yaya aka yi ka shigo nan ba tare da ka sa rigar biki ba?’ Amma mutumin ya rasa abin da zai faɗa.
13 Sai sarkin ya ce wa bayinsa, ‘Ku ɗaura hannaye da ƙafafunsa, ku jefa shi waje cikin duhu, a wurin ne zai yi ta kuka da cizon haƙora.’
14 “Domin mutane da yawa ne aka gayyata, amma kaɗan ne aka zaɓa.”
15 Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara a kan yadda za su sa Yesu ya faɗi abin da zai sa ya shiga cikin tarkonsu.
16 Sai suka aika almajiransu tare da rukunin mutanen da ke goyan bayan Hirudus,* suka ce masa: “Malam, mun san cewa kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Allah a cikin gaskiya, ba ka neman farin jini a gaban kowa, domin ba siffar mutane ne kake dubawa ba.
17 To, ka gaya mana raꞌayinka. Ya dace ne mutum ya biya haraji ga Kaisar ko bai dace ba?”
18 Amma, da yake Yesu ya san mugun zuciyarsu, ya ce musu: “Me ya sa kuke gwada ni, ku munafukai?
19 Ku nuna mini tsabar kuɗi da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari* guda.
20 Sai ya ce musu: “Hoton nan da sunan nan na waye ne?”
21 Suka ce: “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu: “Ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, amma ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”
22 Da suka ji haka, sai suka yi mamaki sosai, kuma suka tafi suka bar shi.
23 A ranar, Sadukiyawa waɗanda suka ce babu tashin matattu, suka zo, suka tambaye shi cewa:
24 “Malam, Musa ya ce: ‘Idan mutum ya mutu ba shi da ꞌyaꞌya, dole ɗanꞌuwansa ya auri matar domin ya haifa wa ɗanꞌuwansa ꞌyaꞌya.’
25 Akwai ꞌyanꞌuwa maza guda bakwai. Na farkon ya yi aure kuma ya mutu ba tare da ya haifi ꞌyaꞌya ba. Da yake ba shi da ꞌyaꞌya, ya bar wa ɗanꞌuwansa matarsa.
26 Haka ya faru da na biyun da na ukun, har ya kai kan na bakwai.
27 A ƙarshe, sai matar ma ta mutu.
28 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Domin dukansu sun aure ta.”
29 Yesu ya ce musu: “Tunaninku ba daidai ba ne, saboda ba ku fahimci Nassosi ko ikon Allah ba;
30 domin a tashin matattu, maza ba za su yi aure ba, kuma mata ba za a aurar da su ba. Amma za su zama kamar malaꞌiku a sama.
31 Game da tashin matattu, ba ku karanta abin da Allah ya faɗa muku saꞌad da ya ce:
32 ‘Ni ne Allah na Ibrahim, da na Ishaku, da na Yakubu’ ba? Shi ba Allah na matattu ba ne, amma Allah na masu rai ne.”
33 Da jin haka, sai jamaꞌar suka yi mamaki sosai don abubuwan da ya koyar.
34 Da Farisiyawan suka ji cewa ya sa Sadukiyawan sun yi shuru, sai suka haɗa kai.
35 Sai wani a cikinsu, wanda ya san Doka* sosai, ya yi masa tambaya don ya gwada shi. Ya ce:
36 “Malam, wace doka ce mafi girma a cikin Dokoki?”
37 Yesu ya ce masa: “‘Dole ne ka ƙaunaci Jehobah* Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da kuma dukan tunaninka.’
38 Wannan ita ce doka ta farko da kuma mafi girma a cikin dokokin.
39 Ta biyu, makamancin doka ta farko, ita ce: ‘Dole ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’
40 Dukan abubuwan da ke cikin Doka da Littattafan Annabawa, sun rataya ne a kan dokoki biyun nan.”
41 Da Farisiyawan suka taru, sai Yesu ya tambaye su ya ce:
42 “Mene ne raꞌayinku game da Kristi? Ɗan waye ne shi?” Suka ce masa: “Shi ɗan Dauda ne.”
43 Sai ya tambaye su ya ce: “To, me ya sa Dauda ta wurin ikon ruhu mai tsarki ya kira shi Ubangiji, yana cewa,
44 ‘Jehobah* ya ce wa Ubangijina: “Ka zauna a hannun damana har sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin ƙafafunka”’?
45 To, idan Dauda ya kira shi Ubangiji, me ya sa aka ce da shi ɗan Dauda?”
46 Babu wani da ya iya ba shi amsa. Kuma daga ranar, babu wanda ya yi ƙarfin hali ya sake yi masa tambaya.
Hasiya
^ Wannan shi ne Hirudus mai suna Antifas. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Dinari ɗaya ya yi daidai da kuɗin da ake biyan lebura na aikin yini ɗaya.
^ Ko kuma “Dokar Musa.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.