Ta Hannun Luka 6:1-49
-
Yesu “Ubangiji ne na Assabaci” (1-5)
-
An warkar da mutumin da hannunsa ya shanye (6-11)
-
Manzannin Yesu goma sha biyu (12-16)
-
Yesu ya yi koyarwa da kuma warkarwa (17-19)
-
Farin ciki da kaito (20-26)
-
Ku ƙaunaci abokan gābanku (27-36)
-
Ku daina shariꞌanta mutane (37-42)
-
Ana gane itace ta wajen ꞌyaꞌyansa (43-45)
-
Gidan da aka gina da kyau da gidan da bai da tushe mai kyau (46-49)
6 A Ranar Assabaci, Yesu ya bi ta gonakin alkama, almajiransa kuma suna tsinka alkama, suna murzawa da hannayensu suna ci.
2 Da Farisiyawa suka ga hakan, sai suka ce: “Me ya sa kuke yin abin da Doka* ta hana a Ranar Assabaci?”
3 Amma Yesu ya amsa musu ya ce: “Shin ba ku taɓa karanta abin da Dauda ya yi saꞌad da shi da mutanen da ke tare da shi suke jin yunwa ba?
4 Yadda ya shiga gidan Allah, kuma ya karɓi burodin da ake miƙa wa Allah, wanda bai kamata shi da mutanen da suke tare da shi su ci ba, sai dai firistoci kaɗai?”
5 Sai ya ce musu: “Ɗan mutum Ubangiji ne na Assabaci.”
6 A wata Ranar Assabaci kuma, sai ya shiga majamiꞌa ya soma koyarwa. Akwai wani mutum da ke wurin da hannun damansa ya shanye.
7 Sai marubuta da Farisiyawa suna ta kallon Yesu don su ga ko zai yi warkarwa a Ranar Assabaci, don su sami abin da za su zarge shi a kai.
8 Amma da yake Yesu ya san abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin da hannunsa ya shanye: “Ka tashi, ka zo ka tsaya a tsakiya.” Sai mutumin ya tashi ya tsaya a wurin.
9 Sai Yesu ya ce musu: “Ina tambayar ku, Ya dace a yi alheri ko kuma mugunta a Ranar Assabaci? A ceci rai ko kuma a yi kisa?”
10 Bayan da Yesu ya kalli dukansu, sai ya ce wa mutumin: “Miƙo hannunka.” Sai mutumin ya yi hakan, kuma hannunsa ya warke.
11 Sai suka soma fushin banza, kuma suka soma shawara da juna a kan abin da za su yi wa Yesu.
12 A kwanakin, Yesu ya haura kan tudu don ya yi adduꞌa, kuma ya kwana yana yin adduꞌa ga Allah.
13 Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa, kuma ya zaɓi goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su manzanni, su ne:
14 Siman, wanda ya ba shi suna Bitrus, da ɗanꞌuwansa Andarawus, da Yaƙub, da Yohanna, da Filibus, da Bartalomi,
15 da Matiyu, da Toma, da Yaƙub ɗan Alfiyus, da Siman wanda ake kira “mai ƙwazo,”
16 da Yahuda ɗan Yaƙub, da Yahuda Iskariyoti, wanda ya ci amanarsa daga baya.
17 Sai Yesu ya sauko tare da manzanninsa, ya tsaya a wani fili, akwai almajiransa da yawa da suka taru, da mutane da yawa da suka fito daga dukan Yahudiya da Urushalima da kuma yankunan da ke bakin teku a Taya da Sidon, da suka zo don su saurare shi, kuma a warkar da cututtukansu.
18 Har waɗanda suke fama da ruhohi masu ƙazanta ma, an warkar da su.
19 Kuma dukan jamaꞌar suna neman su taɓa shi, domin iko yana fita daga jikinsa kuma duk waɗanda suka taɓa shi suna warkewa.
20 Sai ya kalli almajiransa kuma ya soma cewa:
“Ku talakawa, kuna farin ciki, domin Mulkin Allah naku ne.
21 “Ku da kuke jin yunwa yanzu, kuna farin ciki, domin za a ƙosar da ku.
“Ku da kuke kuka yanzu, kuna farin ciki, domin za ku yi dariya.
22 “Ku masu farin ciki a duk lokacin da mutane suka tsane ku, suka kore ku, suka zage ku, kuma suka ɓata sunanku saboda Ɗan mutum.
23 Ku yi farin ciki da murna sosai a ranar, saboda kuna da lada mai yawa a sama, domin irin abubuwan nan ne kakanninsu suka yi wa annabawa.
24 “Amma kaiton ku masu arziki, domin ba za ku samu fiye da abin da kuke da shi yanzu ba.
25 “Kaiton ku, ku da kuka ƙoshi yanzu, domin za ku ji yunwa.
“Kaiton ku, ku da kuke dariya yanzu, domin za ku yi makoki da kuka.
26 “Kaiton ku, a duk lokacin da mutane suka yi maganar kirki game da ku, domin abin da kakanninsu suka yi wa annabawan ƙarya ke nan.
27 “Amma ina gaya muku ku da kuke saurara: Ku ci-gaba da ƙaunar abokan gābanku, kuma ku yi alheri ga waɗanda suka tsane ku,
28 ku yi ma waɗanda suke tsine muku fatan alheri. Ku yi adduꞌa domin waɗanda suke zagin ku.
29 Idan wani ya mare ku a kumatu ɗaya, ku juya masa ɗayan kumatun ya mara; idan wani ya ƙwace mayafinku, kada ku hana masa rigar ciki da kuka saka.
30 Idan wani ya roƙe ku abu, ku ba shi. Kuma wanda ya ƙwace abin da ke naku, kada ku ce masa ya mayar.
31 “Ƙari ga haka, abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma ku yi musu hakan.
32 “Idan kuna ƙaunar waɗanda suke ƙaunar ku kawai, wane lada ne kuke da shi? Ai, masu zunubi ma suna ƙaunar waɗanda suke ƙaunar su.
33 Kuma idan kuna yin alheri ga waɗanda suke yi muku alheri, wane lada ne kuke da shi? Masu zunubi ma suna hakan.
34 Ƙari ga haka, idan kuna ba da bashi* ga waɗanda kuka san za su biya ku, wane lada ne kuke da shi? Masu zunubi ma sukan ba wa masu zunubi bashi don a biya su kuɗinsu daidai.
35 A maimakon haka, ku ci-gaba da ƙaunar abokan gābanku, ku yi alheri, kuma ku ba da bashi ba tare da sa ran samun riba ba; za ku samu lada mai yawa kuma za ku zama ꞌyaꞌyan Mafi Ɗaukaka, domin shi mai alheri ne ga marasa godiya da kuma mugaye.
36 Ku ci-gaba da yin jinƙai kamar yadda Ubanku yake yin jinƙai.
37 “Ƙari ga haka, ku daina shariꞌanta mutane, don kada ku ma a shariꞌanta ku; ku daina hukunta mutane don kada ku ma a hukunta ku. Ku ci-gaba da gafarta wa mutane, don ku ma a gafarta muku.
38 Ku riƙa bayarwa, kuma mutane za su ba ku. Za su zuba muku a riga* mudun da ya cika har yana zuba. Domin da mudun da kuke auna wa mutane, da shi za a auna muku ku ma.”
39 Sai ya ba su wani misali, ya ce: “Makaho zai iya yi wa makaho ja-goranci ne? Idan ya yi hakan, dukansu za su faɗi a cikin rami, ko ba haka ba?
40 Babu ɗalibin da ya fi malaminsa, amma duk wanda aka koyar da kyau, zai zama kamar malaminsa.
41 Don me kake ganin ɗan tsinke da ke idon ɗanꞌuwanka amma ba ka lura da gungumen da ke cikin idonka ba?
42 Me ya sa za ka ce wa ɗanꞌuwanka, ‘Ɗanꞌuwa, bari in cire ɗan tsinke da ke idonka,’ amma kuma ba ka ga gungumen da ke naka idon ba. Munafuki! Ka soma da cire gungumen da ke naka idon tukuna, domin ka iya gani da kyau har ka iya cire ɗan tsinke da ke idon ɗanꞌuwanka.
43 “Babu itace mai kyau da zai ba da ꞌyaꞌya marasa kyau, kuma babu itace marar kyau, da zai ba da ꞌyaꞌya masu kyau.
44 Ana iya gane itace ta wajen ꞌyaꞌyansa. Alal misali, mutane ba sa tsinka ꞌyaꞌyan ɓaure daga cikin ƙaya, ko kuma inabi daga itacen ƙaya.
45 Mutumin kirki yakan fitar da abubuwa masu kyau daga zuciyarsa, amma mugun mutum yakan fitar da mugayen abubuwa daga ajiyarsa na mugunta, domin abin da ya cika zuciya, shi yake fitowa a bakinsa.
46 “Me ya sa kuke kira na, ‘Ubangiji!’ ‘Ubangiji!’ amma ba kwa yin abubuwan da nake faɗa?
47 Duk wanda ya zo wurina, ya ji kalmomina kuma ya aikata su, zan nuna muku wanda yake kama da shi:
48 Yana kama da mutumin da yake so ya gina gida, sai ya tona ƙasa da zurfi, kuma ya kafa tushen ginin a kan dutse. Saꞌad da aka yi ambaliyar ruwa, sai ruwan kogi ya bugi gidan, amma bai iya jijjiga gidan ba, domin an gina gidan da kyau.
49 Amma duk wanda ya ji kalmomina, kuma bai aikata su ba, yana kama da mutumin da ya gina gida a ƙasa ba tare da tushe ba. Da ruwan kogi ya bugi gidan, sai nan take gidan ya rushe, kuma rushewar ya yi muni sosai.”
Hasiya
^ Ko kuma “Dokar Musa.”
^ Wato, ba tare da riba ba.
^ Mutane a zamanin dā suna ɗauka da kuma karɓan abubuwa a cikin rigarsu.