Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE

2 | Kar Ka Rama da Mugunta

2 | Kar Ka Rama da Mugunta

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:

“Idan wani ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta . . . Ku yi iyakar ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa. Kada ku zama masu ramuwa . . . Don kuwa a rubuce yake cikin Maganar Allah cewa, ‘Ramuwa tawa ce, ni kuwa zan rama, in ji Ubangiji.’”​ROMAWA 12:​17-19.

Abin da Ayar Take Nufi:

Ba laifi ba ne mu yi fushi idan wani ya mana laifi, amma Allah ba ya so mu rama. Ya ce mu yi haƙuri domin nan ba da daɗewa ba, zai gyara kome.​—Zabura 37:​7, 10.

Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:

Idan mutane suka rama mugunta da mugunta, yakan sa su ƙara tsanan junansu. Don haka, idan an maka laifi ko an cutar da kai, kada ka rama. Ka yi iya ƙoƙari ka kame kanka don kar ka ta da hankali. Wani lokaci gwamma ka yi kamar ba abin da ya faru. (Karin Magana 19:11) A wasu lokuta kuma, za ka iya kai ƙarar mutumin a wurin hukuma. Alal misali, idan aka maka ɓarna ko wani laifi da hukuma za su iya riƙe mutumin da shi, za ka iya kai ƙararsa.

Idan aka yi maka abu kuma ka rama, kanka kake cuta

Amma idan babu yadda za ka warware matsalar cikin kwanciyar hankali kuma fa? Ko kuma idan ka yi duk iya ƙoƙarinka ka magance matsalar amma ba ka yi nasara ba fa? Kada ka rama da mugunta. Domin idan ka rama, ba mamaki abin zai ƙara yin muni. Kar ka rama, don ka kawo ƙarshen ƙiyayyar da ke tsakaninku. Ka bar kome a hannun Allah. “Ka dogara gare shi, zai kuwa taimake ka.”​—Zabura 37:​3-5, Littafi Mai Tsarki.