Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Ya Sa Kiyayya Ta Yi Yawa Haka?

Me Ya Sa Kiyayya Ta Yi Yawa Haka?

Me ya sa ƙiyayya sai ƙaruwa take yi a duniyar nan? Don mu san dalilin, muna bukatar mu fahimci abin da ake nufi da ƙiyayya da abin da ke sa mutane su soma ƙin juna da kuma yadda wannan ƙiyayyar take yaɗuwa.

Mece ce Ƙiyayya?

Ƙiyayya tana nufin mutum ya ji ba ya son ganin wani ko wasu irin mutane, wato, ya tsane su. Ƙiyayya ba yin fushi da mutum na ɗan lokaci ba ne, ya fi hakan.

ABIN DA YAKE JAWO ƘIYAYYA

Akwai dalilai da yawa da suke sa mutane su soma ƙin wasu. A yawancin lokuta, akan ƙi mutane don inda suka fito ko da ba su yi wani abu da bai dace ba. Za a iya musu kallon mugaye ko munafukai ko waɗanda ba za su taɓa canja halinsu ba. A wasu lokuta kuma akan rena su ko a dinga musu kallon masu jawo matsala. Waɗanda suke ƙin mutane wataƙila su ma an taɓa cin zalinsu ne ko an yi musu rashin adalci ko wani irin mugunta. Shi ya sa su ma suke ramawa.

YADDA ƘIYAYYA TAKE YAƊUWA

Mutum zai iya ƙin wasu irin mutane ko da bai taɓa haɗuwa da su ba. Alal misali, idan ’yan gidanmu ko abokanmu sun ƙi jinin wasu mutane, mu ma in ba mu yi hankali ba, za mu ƙi jininsu. Shi ya sa idan wani a iyali ko a gari ba ya son ganin wasu mutane, kafin ka ankara, sai ka ga kowa a iyalin ko a garin ya ƙi jinin waɗannan mutanen.

Idan muka fahimci yadda ƙiyayya take saurin yaɗuwa, za mu gane abin da ya sa mutane da yawa a yau suke ƙin juna. Amma kafin mu fahimci yadda za a magance ƙiyayya, muna bukatar mu san yadda aka yi ƙiyayya ta soma. Wannan bayanin yana cikin Littafi Mai Tsarki.

LITTAFI MAI TSARKI YA NUNA TUSHEN ƘIYAYYA

BA MUTANE NE SUKA SOMA NUNA ƘIYAYYA BA. Wani mala’ika da ya yi wa Allah tawaye ne ya soma wannan halin. Shi ne daga baya aka ba shi sunan nan Shaiɗan Iblis. Shaiɗan “mai kisa ne tun” da ya fara yi wa Allah tawaye. “Shi mai ƙarya ne, uban ƙarya kuma.” Don haka har wa yau, yana zuga mutane su riƙa ƙin juna kuma su riƙa yin mugunta. (Yohanna 8:44; 1 Yohanna 3:​11, 12) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Shaiɗan mugu ne, maƙaryaci ne, da kuma mai fushi sosai.​—Ayuba 2:7; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​9, 12, 17.

MUNA SAURIN ƘIN MUTANE DON MU MASU ZUNUBI NE. Adamu wanda shi ne mutumin da Allah ya fara halitta ya bi halin Shaiɗan. Shi ya sa dukan mutane suka gāji zunubi da ajizanci. (Romawa 5:12) Ƙiyayya ce ta sa ɗan farin Adamu, wato Kayinu ya kashe ɗan’uwansa Habila. (1 Yohanna 3:12) Akwai mutane da yawa a yau da suke nuna ƙauna da tausayi. Amma wannan zunubin da dukanmu muka gāda, ya sa yawancin mutane sun zama masu son kai da ƙishi da kuma girman kai. Kuma waɗannan halayen ne suke jawo ƙiyayya.​—2 Timoti 3:​1-5.

RASHIN SASSAUTA WA MUTANE YAKAN JAWO ƘIYAYYA. Wani abin da ke hura wutar ƙiyayya a duniyar nan shi ne yadda ake zuga mutane su zama marasa tausayi da masu neman ramako. Rashin jituwa da nuna bambanci da zage-zage da zalunci da ɓarna, sai karuwa suke yi domin “duniya duka tana a hannun mugun nan,” wato Shaidan Iblis.​—1 Yohanna 5:19.

Amma bayan Littafi Mai Tsarki ya gaya mana yadda ƙiyayya ta soma, ya kuma gaya mana yadda za a magance ta.