Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Lokacin da Za A Daina Kiyayya Kwata-kwata!

Lokacin da Za A Daina Kiyayya Kwata-kwata!

Ko da mun yi iya ƙoƙarinmu mun daina ƙin mutane, ba za mu iya hana mutane nuna wannan halin ba. A yau, akwai mutanen da ba su yi kome ba, amma an ƙi jininsu. Yaya za a yi a daina ƙin mutane kwata-kwata?

Allah ne kaɗai zai iya sa mutane su daina nuna ƙiyayya kwata-kwata? Kuma Littafi Mai Tsarki ya ce zai yi hakan.​—Karin Magana 20:22.

ALLAH ZAI CIRE AINIHIN ABUBUWAN DA KE JAWO ƘIYAYYA

  1. 1. SHAIƊAN IBLIS. Shaiɗan, wato wannan mala’ikan da ya yi wa Allah tawaye, shi ne ainihin tushen ƙiyayyar da muke gani a yau. Allah zai hallaka Shaiɗan da dukan mutane masu halinsa.​—Zabura 37:38; Romawa 16:20.

  2. 2. DUNIYAR SHAIƊAN DA KE CIKE DA ƘIYAYYA. Allah zai hallaka duk abin da ke sa mutane su ƙi juna a duniyar nan, har da ’yan siyasa da malaman addini da suke zuga mutane su nuna ƙiyayya. Allah zai kuma hallaka mugayen ’yan kasuwa da ba sa yin gaskiya, sai cucin mutane.​—2 Bitrus 3:13.

  3. 3. AJIZANCI. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dukan mutane sun gāji zunubi, wato muna da kasawa shi ya sa muke saurin yin tunanin abin da bai dace ba kuma mu aikata shi. (Romawa 5:12) Wannan zunubin ne ya sa mutane suke saurin riƙe mutum a zuciya kuma su ƙi jininsa. Allah zai taimaka mana mu fita daga wannan halin. Bayan haka, ƙiyayya za ta zama labari.​—Ishaya 54:13.

LITTAFI MAI TSARKI YA CE ƘIYAYYA ZA TA ƘARE A DUNIYA

  1. 1. ZA A DAINA YIN RASHIN GASKIYA. Mulkin Allah da ke sama ne zai yi sarauta a kan duniya. Kuma a wannan sarautar, ba za a cuci kowa ba. (Daniyel 2:44) Za a daina nuna bambanci da rashin haƙuri. Allah zai kawo ƙarshen danniya da ake wa mutane a yau.​—Luka 18:7.

  2. 2. KOWA ZAI ZAUNA LAFIYA. Ba wanda zai sha wahala saboda yaƙi ko mugunta. (Zabura 46:9) Dukan mutanen da za su rage a duniya masu son zaman lafiya ne, don haka za a sami salama a ko’ina.​—Zabura 72:7.

  3. 3. KOWA ZAI RAYU HAR ABADA A CIKIN YANAYI MAI KYAU. A lokacin, dukan mutane za su ƙaunaci juna sosai. (Matiyu 22:39) Ko tunanin abubuwan da suka same mu a dā ma, ba zai sa mu baƙin ciki ba. (Ishaya 65:17) Idan aka kawar da ƙiyayya, mutane za su yi farin ciki sosai domin za a sami “salama a yalwace.”​—Zabura 37:11.

Shin za ka so ka yi rayuwa a irin wannan yanayin? Ko a yanzu ma, mutane da yawa suna bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce don su daina tsanan mutane. (Zabura 37:8) Abin da miliyoyin Shaidun Jehobah a faɗin duniya suke yi ke nan. Ko da yake sun fito daga wurare dabam-dabam, sun zama kamar iyali. Suna ƙaunar juna kuma suna da haɗin kai.​—Ishaya 2:​2-4.

Shaidun Jehobah za su so su gaya maka abin da za ka yi don ka iya jimrewa idan ana nuna maka bambanci ko ana maka rashin adalci. Abin da za su koya maka zai taimaka maka ka ƙaunaci mutane maimakon ka ƙi su. Za ka koyi yadda za ka ƙaunaci kowa, har da waɗanda suka ƙi jininka ko ba sa kyautata maka. Hakan zai sa ka ƙara yin farin ciki yanzu kuma ka zauna lafiya da mutane. Mafi muhimmanci ma, za ka koyi yadda za ka yi rayuwa a Mulkin Allah a lokacin da ba za a sake nuna ƙiyayya ba har abada.​—Zabura 37:29.